RAYUWAR KIRISTA
Ka Nuna Sauƙin Kai Sa’ad da Aka Yaba Maka
A wasu lokuta mutane za su iya yaba mana. Idan suka yabe mu da zuciya ɗaya, hakan yana ƙarfafa mu sosai. (K. Ma 15:23; 31:10, 28) Amma dole ne mu mai da hankali don kada yabon da ake mana ya sa mu zama da girman kai kuma mu soma rena mutane.
KU KALLI BIDIYON NAN KU RIƘE AMINCI KAMAR YESU SA’AD DA AKA YABE KU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Waɗanne abubuwa ne za su iya sa a yaba mana?
Ta yaya ’yan’uwan suka yaba ma Sergei?
Ta yaya yabon da suka yi wa ɗan’uwan ya wuce gona da iri?
Waɗanne darussa ne ka koya daga yadda Sergei ya nuna sauƙin kai?