BABI NA 21
Ya Kamata Ne Mu Yi Fahariya A Kan Wani Abu?
MENENE fahariya take nufi? Ka sani?— Ga misali. Ka taɓa ƙoƙarin ka yi abin da ba ka iya ba sosai? Wataƙila buga kwallon ƙafa. Ko kuma ka taɓa ƙoƙarin ka yi wasan tsallake igiya. Akwai wanda ya taɓa cewa, “Wai! Wai! Wai! Ashe na fi ka iyawa ma?”— Wannan fahariya yake yi.
Yaya kake ji idan wasu sun yi haka? Kana jin daɗinsa?— To, yaya kake ji wasu za su ji idan kana fahariya game da kanka?— Daidai ne ka gaya wa wani, “na fi ka”?— Jehovah yana son mutane da suke yin haka ne?—
Babban Malami ya san mutane da suke tsammanin sun fi wasu. Suna yin fahariya game da kansu kuma suna raina kowa. Wata rana Yesu ya ba su wani labari da ya nuna musu cewa ba daidai ba ne su yi fahariya. Bari mu saurara.
Labarin game da Bafarisi ne da kuma mai karɓan haraji. Farisawa malaman addini ne kuma sau da yawa suna abubuwa kamar sun fi kowa adalci ko kuma tsarki. Bafarisi na labarin Yesu ya je haikalin Allah a Urushalima ya yi addu’a.
Me ya sa Allah ya yi farin ciki da mai karɓan haraji amma ba da Bafarisi ba?
Yesu kuma ya ce wani mai karɓan haraji ma ya je haikalin domin ya yi addu’a. Mutane da yawa ba sa son masu karɓan haraji. Suna tunanin cewa masu karɓan harajin suna ƙoƙari ne su cuce su. Kuma gaskiya ne yawancin masu karɓan harajin ba sa yin gaskiya.
A cikin haikalin, Bafarisi ya fara addu’a ga Allah yana cewa: ‘Ya Allah, na gode maka da yake ni ba mai zunubi ba ne kamar wasu mutane. Ba na cutar mutane ko kuma in yi wasu miyagun ayyuka. Ni ba kamar wancan mai karɓan haraji ba ne. Ni mutum ne mai adalci. Ba na cin abinci sau biyu a sati domin in samu lokacin yin bimbini game da kai. Kuma ina bayar da ushirin dukan abin da na ke da shi ga haikali.’ Bafarisin da gaske yana tsammanin ya fi wasu ko ba haka ba ne?— Kuma ya gaya wa Allah game da wannan ma.
Amma mai karɓan harajin ba haka yake ba. Bai ma iya ɗaga idanunsa sama ba sa’ad da yake addu’a. Ya ci gaba da tsayawa da nesa kuma kansa a ƙasa. Mai karɓan harajin ya yi nadama sosai domin zunubansa, kuma ya buga zuciyarsa domin baƙin ciki. Bai ga ya dace ya gaya wa Allah adalcinsa ba. Maimakon haka, ya yi addu’a: ‘Ya Allah, ka gafarta mini ni mai zunubi.’
Wanene cikin waɗannan mutane biyu kake tsammanin ya faranta wa Allah rai? Bafarisin ne da yake tsammanin, yana da adalci? Ko kuma mai karɓan haraji, wanda ya yi nadama domin zunubansa?—
Yesu ya ce mai karɓan harajin ne ya faranta wa Allah rai. Me ya sa? Yesu ya yi bayani: ‘Domin dukan wanda ya yi ƙoƙari ya nuna cewa ya fi wasu mutane za a kunyatar da shi. Amma wanda yake ganin kansa ƙarami ne za a girmama shi.’—Luka 18:9-14.
Wane darasi ne Yesu yake koyarwa cikin labarinsa?— Ya koyar ne cewa ba daidai ba ne mu yi tunanin mun fi wasu. Za mu ce ba ma tunanin mun fi wasu, amma ta hanyar da muke abubuwa, za mu nuna cewa mun fi su. Ka taɓa yin irin wannan?— Ka yi la’akari da manzo Bitrus.
Sa’ad da Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa dukansu za su guje shi sa’ad da aka kama shi, Bitrus ya yi fahariya: ‘Idan kowa ya bar ka, ni ba zan taɓa barin ka ba!’ Amma Bitrus bai yi gaskiya ba. Ya dogara ga kansa ainun. Ya guji Yesu. Amma dai ya komo, kamar yadda za mu gani a Babi na 30 na wannan littafin.—Matta 26:31-33.
Bari mu zaɓi misalai na zamani. Wataƙila an yi muku tambaya a aji a makaranta. Me za ka yi idan ka ba da amsar a take amma ɗayan ɗalibin bai ba da amsa ba? Hakika, za ka ji daɗi idan ka san amsar. Amma yana da kyau ne ka gwada kanka da wanda bai ba da amsa ba?— Daidai ne ka yi ƙoƙari ka ɗauki kanka da daraja kuma ka mai da ɗayan yaron marar daraja?—
Wannan shi ne abin da Bafarisin ya yi. Ya yi fahariyar cewa shi ya fi mai karɓan harajin. Amma Babban Malami ya ce Bafarisin bai yi abin da ke daidai ba. Gaskiya ne cewa wani zai iya ya yi wani abu fiye da yadda wani zai yi. Amma wannan ba ya nufin cewa ya fi ɗayan mutumin.
Idan kana da ilimi fiye da wasu wannan ya sa ka fi wasu ne?
Saboda haka, idan muna da ilimi fiye da wasu mutane, dalili ne mai kyau da za mu yi fahariya?— Ka yi tunani a kan wannan. Mu muka yi ƙwaƙwalwarmu?— A’a, Allah ne ya ba kowannenmu ƙwaƙwalwa. Kuma yawancin abin da muka sani mun koya ne daga wurin wani. Wataƙila mun karanta daga littafi. Wataƙila wani ne ya gaya mana game da su. Ko ma mu muka gano wani abu da kanmu, ta yaya muka yi?— Hakika, ta wajen amfani da ƙwaƙwalwar da Allah ya ba mu ne.
Idan wani ya yi ƙoƙari, abin da ya fi kyau shi ne ka gaya masa abin da zai sa shi ya yi murna. Ka gaya masa cewa kana son abin da ya yi. Wataƙila za ka taimake shi ya inganta abin. Haka kake so mutane su yi maka, ko ba haka ba ne?—
Me ya sa ba daidai ba ne mu yi fahariya idan mun fi wasu ƙarfi?
Wasu mutane sun fi wasu mutane ƙarfi. Me za ka yi idan kana da ƙarfi fiye da ƙaninka ko kuma ƙanwarka? Wannan dalili ne da za ka yi fahariya?— A’a. Abincin da muke ci ne yake ba mu ƙarfi. Kuma Allah ne yake ba da hasken rana da ruwan sama da kuma dukan abin da muke bukata domin abincinmu ya yi girma, ko ba haka ba ne?— To, saboda haka Allah ya kamata mu gode wa idan muka yi ƙarfi.—Ayukan Manzanni 14:16, 17.
Babu wanda yake so ya ji mutane suna fahariya game da kansu, ko da akwai ne?— Bari mu tuna da kalmomin Yesu: ‘Kamar yadda kake so mutane su yi maka, ka yi musu haka kai ma.’ Idan muka yi haka, ba za mu taɓa zama kamar Bafarisi ba wanda ya yi fahariya game da kansa cikin labarin da Babban Malami ya bayar.—Luka 6:31.
Sau ɗaya wani ya kira Yesu managarci. Babban Malami ya ce, ‘E, ni managarci ne’?— A’a, bai ce haka ba. Maimakon haka, ya ce: “Babu wani managarci sai ɗaya, Allah.” (Markus 10:18) Ko da yake Babban Malami kamili ne, bai yi fahariya game da kansa ba. Maimakon haka, ya yabi Ubansa, Jehovah.
Saboda haka, da akwai wani ne da za mu yi fahariya da shi?— E, da akwai. Za mu iya mu yi fahariya da Mahaliccinmu, Jehovah Allah. Idan muka ga abu mai kyau ko kuma wata halitta mai ban mamaki, za mu iya gaya wa wani, ‘Allahnmu mai girma, Jehovah ne ya yi wannan!’ Bari mu kasance ko da yaushe a shirye mu yi magana game da abubuwa masu girma da Jehovah ya riga ya yi da kuma waɗanda zai yi a nan gaba.
Menene wannan yaron yake fahariya a kai?
Ka karanta abin da Nassosi suka ce game da fahariya, kuma ka koyi yadda za mu guje wa yin fahariya game da kanmu: Misalai 16:5, 18; Irmiya 9:23, 24; 1 Korinthiyawa 4:7; da kuma 13:4.