RAYUWAR KIRISTA
Ku Yi Tarayya da Mutanen da Suke Ƙaunar Jehobah
Me ya sa muke bukatar mu riƙa tarayya da mutanen da suke ƙaunar Jehobah? Domin waɗanda muke tarayya da su za su iya rinjayar mu mu yi abubuwa masu kyau ko marasa kyau. (K. Ma 13:20) Alal misali, sa’ad da Sarki Yowash yake abota da Babban Firist mai suna Yehoyida, ya yi “abin da yake daidai a idon Yahweh.” (2Tar 24:2) Amma bayan da Yehoyida ya rasu, mutanen da Yowash ya soma tarayya da su sun sa ya daina bauta ma Jehobah.—2Tar 24:17-19.
A ƙarni na farko, manzo Bulus ya kwatanta ikilisiyar Kirista da “babban gida,” ’yan’uwan da suke ikilisiyar kuma ya kwatanta su da “kayan” gida. Idan muka guji yin tarayya da duk wanda ba ya son ya faranta wa Jehobah rai har da danginmu, za mu ci gaba da zama “abin da aka keɓe domin aiki na musamman.” (2Ti 2:20, 21) Don haka, mu ci gaba da yin abota da mutanen da suke ƙaunar Jehobah kuma suke ƙarfafa mu mu bauta masa.
KU KALLI BIDIYON NAN KU GUJI YIN TARAYYA DA ABOKAN BANZA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
A waɗanne hanyoyi ne za mu iya soma tarayya da abokan banza?
A wannan bidiyon, mene ne ya taimaka wa ’yan’uwa ukun su daina tarayya da abokanan banza?
Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka maka ka zaɓi abokan kirki?
Shin an ‘keɓe ni domin aiki na musamman’ ne?—2Ti 2:21