RAYUWAR KIRISTA
Mu Yi Wa’azi da Haɗin Kai A Yankuna da Ake Yaruka da Yawa
Idan mutane suka ji wa’azi a yarensu, hakan na sa su saurara da kyau. Mai yiwuwa shi ya sa a lokacin Fentakos na shekara ta 33, Jehobah ya sa an yi wa Yahudawa “masu tsoron Allah” daga ƙasashe dabam-dabam wa’azi a ‘yaren’ ƙasarsu, duk da cewa suna jin Ibrananci da Helenanci, wato yaruka da aka saba yi a lokacin. (A. M 2:5, 8) A yankunan da ake yaruka da yawa, ikilisiyoyi suna iya yin taro a yaruka dabam-dabam amma suna wa’azi a yanki ɗaya. Ta yaya masu shela a irin waɗannan ikilisiyoyin za su haɗa kai don su yi ma kowa wa’azi ba tare da yin wa’azi a kai a kai a wuri ɗaya ba don hakan zai iya sa masu sauraronmu fushi?
Ku tattauna batun (K. Ma 15:22): Masu kula da hidima daga waɗannan ikilisiyoyi za su tattauna tare don su san yadda za su yi wa’azi a yankin yadda ya dace. Idan yankin ikilisiyoyin da ke wani yare bai da girma, za su so kada ku yi wa’azi a gidajen da ake yarensu a yankin. Amma, idan ba za su iya yin wa’azi a yankinsu gaba ɗaya ba don yana da yawa kuma mutane da suke yaren ikilisiyar suna a warwatse, za su iya ce ku yi ma kowa wa’azi amma idan akwai wani da ke son saƙonmu a yankin, ku sanar da su. (od-E 93 sakin layi na 37) Ko kuma za su iya ce ma ikilisiyarku ta taimaka musu wajen neman waɗanda ke yin yarensu a yankinku. Idan kuka samu wanda yake son saƙonmu, sai ku tura musu adreshinsa. (km 7/12 akwatin da ke shafi na 5) Ku tuna cewa, a wasu gidaje ana yin yare fiye da ɗaya. Saboda haka, idan kun karɓi bayanin mutum, ku tabbata cewa kun bi duk wata dokar ƙasa a kan yadda za a kāre bayanan mutane.
Ku haɗa kai (Afi 4:16): Ku bi duk wani umurnin da mai kula da hidima ya ba ku. Idan kana nazari da wanda ba yarensa kuke yi a ikilisiyarku ba fa? Ɗalibin zai samu ci gaba sosai idan ka haɗa shi da wani a ikilisiyar da ake yin yaren da ya fi fahimta da kyau.
Ku yi shiri (K. Ma 15:28; 16:1): Idan kuka haɗu da wani da yake yin wani yare sa’ad da kuke wa’azi, ku yi ƙoƙari ku yi masa wa’azi. Ku bincika don ku san yaruka da ake yi a yankin kuma ku sauƙar da bidiyoyi da wasu juyin Littafi Mai Tsarki na yarukan a na’urarku. Za ku iya yin amfani da manhajar JW Language don ku iya koyan gaisuwa a yarukan.