Idin Ƙetarewa ba ya wakiltar Jibin Maraice na Ubangiji, amma akwai abubuwan da za mu iya koya daga Idin Ƙetarewan. Alal misali, manzo Bulus ya kira Yesu “Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa.” (1Ko 5:7, Littafi Mai Tsarki) Kamar yadda jinin ɗan ragon da Isra’ilawa suka shafa a bakin kofa ya ceci su, haka nan jinin Yesu ya ceci mutane. (Fit 12:12, 13) Ƙari ga haka, ba a karya kashin ragon ba. Hakazalika, ba a karya kashin Yesu sa’ad da aka kashe shi ba duk da cewa haka ake yi idan aka rataye mutum a kan gungume.—Fit 12:46; Yoh 19:31-33, 36.