RAYUWAR KIRISTA
Ku Kasance da Halaye Masu Kyau—Sauƙin Kai
ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI:
Sauƙin kai zai sa mu kusaci Jehobah sosai.—Za 138:6
Sauƙin kai zai sa mu kasance da dangantaka mai kyau da mutane.—Fib 2:3, 4
Girman kai yana da haɗari sosai.—Mis 16:18; Eze 28:17
YADDA ZA KA KASANCE DA HALIN:
Ka nemi taimako kuma ka bi shawarar da aka ba ka.—Za 141:5; Mis 19:20
Ka riƙa yi wa mutane hidima.—Mt 20:25-27
Kada ka bar matsayin da kake da shi ya sa ka girman kai.—Ro 12:3
A waɗanne hanyoyi ne zan iya kasancewa da sauƙin kai?
KU KALLI BIDIYON NAN KU GUJI ABUBUWAN DA ZA SU SA KU ZAMA MARASA AMINCI—GIRMAN KAI, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Mene ne halin da muke nunawa sa’ad da aka yi mana gargaɗi yake nuna game da mu?
Ta yaya addu’a take taimaka mana mu kasance da sauƙin kai?
A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna cewa muna da sauƙin kai?