Ka Yi Amfani da Sassa Dabam-dabam na Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Yadda Ya Dace
Yayin da ɗalibi yake koyan ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa kuma yana amfani da abin da yake koya, zai sami ci gaba kuma ya kasance da halaye masu kyau. (Zab. 1:1-3) Za mu iya taimaka wa ɗalibinmu ya sami ci gaba idan muna yin amfani da sassa dabam-dabam na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da kyau.
Tambayoyin Gabatarwa: An soma kowane babi da tambayoyin da za a sami amsoshinsu a babin. Za ka iya yin waɗannan tambayoyin domin ka sa ɗalibinka ya yi marmarin nazarin da za ku yi. Ko kuma ka sa shi ya yi gajeren kalami a kan kowace tambaya. Idan bai ba da amsar daidai ba, ba zai dace ka yi masa gyara nan tāke ba. Kalaminsa zai taimaka maka ka san wuraren da ya kamata ka mai da wa hankali da kuma nanata sa’ad da kuke nazarin.—Mis. 16:23; 18:13.
Rataye: Idan ɗalibin ya fahimci abin da kuka nazarta kuma ya aminci da shi, zai dace ka gaya masa ya karanta ratayen da ya tattauna batun da kansa. Kafin ku soma nazari na gaba, zai dace ka yi amfani da ‘yan mintoci don ka san ko ya fahimci ratayen da ya karanta. Amma idan ka ga cewa zai amfana, ka ɗauki lokaci sa’ad da kuke nazarin don ku tattauna ratayen ko kuma wasu sakin layi na ratayen kuma ka yi masa tambayoyin da ka shirya.
Akwatin Bita: Akwatin bita da ke ƙarshen kowane babi yana ɗauke da amsoshin tambayoyin da aka yi a farkon babin. Za ka iya yin amfani da wannan akwatin don ka taimaka wa ɗalibinka ya fahimci kuma ya iya bayyana darussan da ya koya. Ku karanta rubutun da ke akwatin da kuma ayoyin Littafi Mai Tsarki da aka ambata a ciki. Bayan haka, ka gaya wa ɗalibinka ya yi amfani da ayoyin wajen bayyana dalilin da ya sa abin da aka ambata a akwatin gaskiya ne.—A. M. 17:2, 3.