Abin da Muke Bukata don Mu Zama Ƙwararrun Malamai
An taɓa yi wa Yesu tambaya sau biyu game rai na har abada. Yesu ya yi la’akari da yanayin mai tambayar kafin ya ba da amsa. (Luk. 10:25-28; 18:18-20) Saboda haka, ko da mun san bayanin da ke cikin littafin nazarin sosai, ya kamata mu yi la’akari da yanayin ɗalibin sa’ad da muke shiri. Waɗanne abubuwa ne za su yi wa ɗalibin wuya ya yarda da su ko kuma ya fahimta? Waɗanne ayoyi ne ya kamata ka karanta masa? Sakin layi nawa ne ya kamata mu tattauna da shi? Ya kamata mu shirya misalai ko bayanai ko kuma tambayoyin da za mu yi amfani da su don ya fahimci batun. Ƙari ga haka, tun da yake Jehobah ne yake sa mutane su fahimci gaskiyar Littafi Mai Tsarki, ya kamata mu yi addu’a game da ɗalibin da sa’ad da muke shirya nazarin da kuma basirar da za mu yi amfani da shi don taimaka masa ya san Allah.—1 Kor. 3:6; Yaƙ. 1:5.