Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/15 pp. 2-3
  • Ku Taimaka wa Makafi Su San Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Taimaka wa Makafi Su San Jehobah
  • Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Makamantan Littattafai
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yadda Za Mu Yi Wa Makafi Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Allah Ya Amsa Adduꞌar Wata Makauniya
    Labarai
Hidimarmu Ta Mulki—2015
km 5/15 pp. 2-3

Ku Taimaka wa Makafi Su San Jehobah

1. Ta yaya Yesu ya nuna jin ƙai ga makafi?

1 Sa’ad da Yesu yake barin birnin Yariko ’yan kwanaki kaɗan kafin a kashe shi, sai wasu makafi biyu suka ta da murya suka ce masa: “Ubangiji, ka yi mana jinƙai.” Ko da yake Yesu ya damu sosai don abin da yake gab da fuskanta, ya dakata ya kira su kuma ya warkar da su. (Mat. 20:29-34) Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu a nuna jinƙai?

2. Ta yaya za mu iya yi wa makahon da muka gani a cikin jama’a wa’azi?

2 Ku Riƙa Taimako: Idan ka haɗu da makaho a cikin jama’a, ka gaya masa sunanka kuma ka ce za ka so ka taimaka masa. Wataƙila mutumin ba zai saki jiki da kai da farko ba da yake ana yawan cin zarafin makafi. Amma idan ka yi fara’a kuma ka nuna ka damu da shi, zai iya saki jiki da kai. Zai dace mu tuna cewa yanayin makafi ya bambanta kuma hakan zai iya nuna irin taimakon da ya kamata mu bayar. Bayan ka taimaka masa, za ka iya gaya masa cewa kai mai wa’azin bishara ne. Sai ka karanta masa nassosi kamar su Zabura 146:8 ko kuma Ishaya 35:5, 6. Idan ya iya karatun makafi, sai ka tambaye shi ko zai so ka kawo masa wani littafin da zai taimaka masa ya ƙara sanin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, za ka iya taimaka masa wajen sauko da wasu sauti a dandalin jw.org. Idan kwamfutarsa tana da na’urar da ke juya rubutun da ke allon kwamfuta zuwa sauti, ƙila zai so a saukar masa da littattafan da ke dandalin jw.org da kuma wasu littattafan da za a iya saukar da fasalin RTF wato Rich Text Format.—Ka duba akwatin nan “Sa’ad da Kuke Taimaka wa Makaho. . . .”

3. Ta yaya za mu iya neman makafi a yankinmu?

3 Ku Nemi Makafi: Ba ma cika samun makafi sa’ad da muke wa’azi gida-gida don yawancinsu ba sa cika son tattaunawa da baƙi. Saboda haka, muna bukata mu ƙoƙarta sosai don mu “nemi” irin waɗannan mutane sa’ad da muke wa’azi. (Mat. 10:11) Shin kana da abokin aiki ko abokin makaranta wanda makaho ne? Ka yi amfani da wannan damar don ka yi masa wa’azi. Idan akwai makarantar makafi a yankinku, ka nemi izinin saka wasu littattafanmu na makafi a laburarin makarantar. Shin ka san wani da ɗan’uwansa makaho ne? Akwai ƙungiyoyin da ke taimaka wa makafi a yankinku ko wani gidan haya da makafi suke zama a ciki? Ka gaya wa ɗan’uwansa ko mai tarbar baƙi a wurin ko kuma darektan cewa Shaidun Jehobah suna son su taimaka wa makafi, kuma za su so su tanadar wa makafin littattafai ko sauti a yarensu. Ka nuna masa alkawarin da Allah ya yi a cikin Littafi Mai Tsarki cewa nan ba da daɗewa ba, zai buɗe idanun makafi. Za ka iya nuna masa bidiyon nan da ke dandalin jw.org mai jigo “Da Ba Don Littafin Ba, Babu Abin da Zan Fahimta,” da ya ba da labarin wani makaho da ya amfana daga Littafi Mai Tsarki na makafi. Idan ka bayyana dalilin zuwanka, hakan zai ba ka zarafin tattaunawa da wasu makafi da ke wurin.

4. Waɗanne darussa ne za mu koya daga labarin Janet?

4 Wata ’yar’uwa makauniya mai suna Janet ta ziyarci gidan makafi. Sai ta soma tattaunawa da wata mata. Janet ta gaya mata cewa, “Yesu ya warkar da makafi sa’ad da yake duniya don ya nuna abin da zai yi wa makafi a nan gaba.” Bayan haka, sai Janet ta karanta mata littafin Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4, kuma ta bayyana mata yadda Allah zai yi amfani da Mulkinsa don ya cika wannan alkawarin. Matar ta ɗan yi shiru, sai ta ce: “Ban taɓa jin wani makaho ya yi irin wannan bayanin ba. Yawancin mutanen da ba makafi ba sun gaskata cewa mutane suna makanta ne don wasu laifuffuka da su ko kuma kakanninsu suka aikata.” Daga baya, Janet ta tura wa matar adireshin Yanar gizo ta imel da za ta iya shiga don ta karanta littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? kuma yanzu suna nazarin Littafi Mai Tsarki sau biyu a mako.

5. Wace albarka ce za mu samu idan muka nuna cewa mun damu da makafi ko da yake ba za mu iya warkar da su kamar yadda Yesu ya yi ba?

5 Ko da yake ba za mu iya warkar da makafi kamar yadda Yesu ya yi ba, amma za mu iya taimaka wa dukan mutanen da allah na wannan zamanin ya makantar da zukatansu, har da makafi su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki. (2 Kor. 4:4) Yesu ya warkar da makafi biyu kusa da Yariko don ya ji ‘tausayin’ su. (Mat. 20:34, Littafi Mai Tsarki) Idan muka nuna mun damu da makafi kamar yadda Yesu ya yi, za mu sami gatan taimaka wa wasunsu su san Jehobah wanda zai kawar da makanta har abada.

Sa’ad da Kuke Taimaka wa Makaho . . .

  • Ku yi masa magana kai tsaye amma kada ku ta da murya. Makafi ba sa gani amma suna ji sosai.

  • Idan kuna ja-gorarsa, ku saukar da hannunku ƙasa don ya riƙe saman gwiwar hannunku. Zai iya bin ku a baya idan kuna tafiya a hankali a gabansa. Idan kun ga falwaya ko matakala ko kuma wani abu da zai iya sa shi tuntuɓe yayin da kuke tafiya, zai dace ku gaya musu.

  • Kada ku yi jinkirin yin amfani da kalamai kamar su “kalla” da kuma “duba” domin makafi ma suna amfani da waɗannan kalaman. Suna iya gani da azancinsu, har suna iya kwatanta hotunan wasu abubuwan da ake musu magana a kai.

  • Ku tattauna a inda babu surutu. Makafi ba sa jin daɗin zama a inda ake surutu sosai, don ba za su iya fahimtar abin da ke faruwa a wurin ba.

  • Ku sanar da shi sa’ad da kuke so ku je wani wuri. Hakan zai sa kada ya riƙa magana shi kaɗai yana zato cewa yana tare da wani.

  • Idan makahon yana son saƙonmu amma ba ya zama a yankinku, ku cika fom ɗin nan Please Follow Up (S-43), bayan haka, ku ba sakataren ikilisiyarku.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba