Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/15 p. 4
  • Tsarin Ayyuka na Makon 1 Ga Yuni

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tsarin Ayyuka na Makon 1 Ga Yuni
  • Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Ƙananan Jigo
  • MAKON 1 GA YUNI
Hidimarmu Ta Mulki—2015
km 5/15 p. 4

Tsarin Ayyuka Makon 1 Ga Yuni

MAKON 1 GA YUNI

Waƙa ta 13 da Addu’a

Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:

cl babi na 25 sakin layi na 9-16 (minti 30)

Makarantar Hidima ta Allah:

Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sama’ila 16-18 (minti 8)

Na 1: 2 Sama’ila 17:14-20 (minti 3 ko ƙasa da hakan)

Na 2: Misalai na Masu Sauƙin Kai da Gaske a Cikin Littafi Mai Tsarki (minti 5)

Na 3: Ta Yaya Za Ka Yi Amfani da Dukiyarka da Kyau?—igw 21 sakin layi na 1-4 (minti 5)

Taron Hidima:

Jigon Wata: Ku taimaki ire-iren mutane su san ainihin koyarwar Littafi Mai Tsarki.—1 Tim. 2:3, 4.

Waƙa ta 36

Minti 10: Ku Ba da Mujallu a Watan Yuni. Tattaunawa. Da farko, ka sa a yi gwaji a kan yadda za a iya ba da mujallun ta wajen yin amfani da gabatarwar da aka bayar. Bayan haka, ka yi kalami a kan kowace gabatarwar.

Minti 10: Ku Yi Amfani da Takardun Gayyata Yadda Ya Dace. Tattaunawa. An sanar da mu a cikin wasiƙa ta 27 ga Nuwamba, 2014, zuwa ga dukan ikilisiyoyi cewa an yi wata sabuwar takardar gayyata da za a riƙa amfani da ita wajen gayyatar mutane zuwa “taron ikilisiya ko kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki.” An saka “hotunan taron ikilisiya da kuma yadda ake gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki” a cikin takardar gayyatar. Ko da kun sami sabuwar takardar gayyatar ko a’a, ka nanata yadda take da amfani a wa’azi da kuma gayyato mutane zuwa taro. (km 12/05-E shafi na 4) Ka yi waɗannan tambayoyi na gaba: (1) Kuna da wani labari mai daɗi a kan rarraba takardun gayyata? (2) Ta yaya za mu iya yin amfani da takardar wajen gabatar da kanmu da kuma soma tattaunawa sa’ad da muke wa’azi gida-gida? (3) Ta yaya za mu iya yin amfani da ita a hanya mai kyau ta wajen soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kyauta? (4) Ta yaya iyaye za su iya yin amfani da takardun gayyata wajen koya wa yaransu yin wa’azi? (5) Ta yaya masu shela da suke yin wa’azi ta hanyar wasiƙa za su iya yin amfani da takardar wajen gayyatar mutane zuwa taronmu? (6) Wace dabara mai kyau ce kuke amfani da ita wajen gayyatar ɗalibanku da kuma wasu su halarci taronmu? Ka ƙarfafa masu sauraro su rarraba takardar gayyatar sa’ad da suke ayyukansu na yau da kullum, kuma su ba da rahoton adadin takardar gayyatar da suka rarraba. A rubuta shi a sashen da ake rubuta rahoton warƙoƙi.

Minti 10: Mene ne Muka Cim ma? Tattaunawa. Ka ba ’yan’uwa dama su faɗi darussan da suka koya a talifin nan “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Wa’azi ga Mutumin da Ke Wani Yare.” Ka ba masu sauraro dama su faɗi labarai masu daɗi da suke da shi.

Waƙa ta 25 da Addu’a

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba