Gabatarwa
Hasumiyar Tsaro Janairu–Fabrairu
“Yau mun fito ne mu tattauna da iyalai. Iyaye da yawa suna so yaransu su ƙaunaci Allah. Kana ganin iyaye ne ya kamata su koya wa yaransu yadda za su ƙaunaci Allah, ko yara ne za su yi hakan da kansu? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka ji amsar da Littafi Mai Tsarki ya bayar.” [Karanta Kubawar Shari’a 6:5-7.] Ka nuna masa shafi na 16 na mujallar kuma ka ce: “Wannan talifin ya bayyana yadda iyaye za su iya taimaka wa ’ya’yansu.”
Awake! Fabrairu
“Muna ziyartar maƙwabtanmu ne don mu ba su mujallar Awake! na kwanan nan. Mujallar ta yi bayani a kan wata tambaya mai ban sha’awa. [Ka nuna masa bangon gaba.] Zan so in ji ra’ayinka a kan wani misali da aka ambata a cikin mujallar nan. [Karanta Misalai 29:11.] Kana ganin wannan ƙa’idar za ta iya amfanarmu a yau? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan mujallar ta tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki huɗu kuma ta yi bayani a kan yadda za mu amfana idan muka bi su.”