Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/14 p. 8
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 4/14 p. 8

Gabatarwa

Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Mayu

“Muna ziyartar mutane ne yau don mu tattauna wata tambaya. [Ka nuna masa tambaya ta farko a shafi na ƙarshe a Hasumiyar Tsaro ta Mayu–Yuni.] Mene ne ra’ayinka game da wannan tambayar?” [Ka bari ya ba da amsa.] Ku tattauna sakin layi na farko a ƙarƙashin tambaya ta farko da kuma nassosin da aka rubuta a wurin. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna sakin layi na biyu.

Hasumiyar Tsaro Mayu–Yuni

“Muna ɗan tattaunawa ne da mutane a kan abin da kusan kowa yake yi, wato addu’a. Mutane suna yin addu’a, ko da wane addini ne suke bi. Kana ganin Allah yana jin addu’a, ko kuma ana yinta ne kawai don a sami kwanciyar hankali daga matsaloli? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka ji abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a batun addu’a. [Karanta 1 Yohanna 5:14.] Wannan mujallar ta tattauna yadda addu’a take amfanar mu.” Ka nuna masa talifin da ya soma a shafi na 3.

Awake! Mayu

“Muna ziyartar mutane ne don mu taimaka musu su magance matsalar gajiya. A ganinka mutane suna yawan gajiya ne a yau fiye da dā? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa sun gano cewa bin shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki yana taimaka musu su magance matsalar yawan gajiya. Ga wani misali. [Karanta Matta 6:34.] Wannan mujallar ta bayyana yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mana mu san yadda za mu bi da abubuwa huɗu masu jawo gajiya.”

Abin lura: Masu kasuwanci da kuma sana’a za su so wannan talifin sosai.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba