Wani Sabon Kayan Bincike
Miliyoyin masu shela a faɗin duniya sun yi amfani da littafin nan Watch Tower Publications Index wajen yin bincike. Duk da haka an wallafa shi a harsuna kaɗan ne kawai domin yana da batutuwan bincike da yawa a ciki. Amma Littafin Bincike don Shaidun Jehobah littafi ne da aka wallafa cikin harsuna wajen 170, kuma yana ɗauke da sunayen littattafan da aka wallafa daga shekara ta 2000 zuwa sama da hakan. Ba a buga Littafin Bincike don Shaidun Jehobah a harsunan da akwai Watch Tower Publications Index ba amma an saka shi a dandalin jw.org, a cikin Watchtower Library da kuma Watchtower—ONLINE LIBRARY. Littafin Bincike don Shaidun Jehobah zai taimaka maka wajen neman amsoshi ga tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki, da samun bayanai a kan batutuwan da ke damunka, da kuma a yin shiri don ibada ta iyali da taron ikilisiya.