Tsarin Ayyuka na Makon 1 ga Disamba
MAKON 1 GA DISAMBA
Waƙa ta 48 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 16, sakin layi na 18-22, da akwatin da ke shafi na 167(minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Kubawar Shari’a 32-34 (minti 10)
Na 1: Kubawar Shari’a 32:22-35 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Yadda Mutum Zai Ƙware Ya Zama Minista—td 31B (minti 5)
Na 3: Yara da Suka Faranta wa Allah Rai—lr babi na 41 (minti 5)
Taron Hidima:
Waƙa ta 128
Minti 10: Ku Ba da Mujallu a Watan Disamba. Tattaunawa. Ka sa a yi gwaji guda uku da ke wannan shafin. Bayan kowane gwaji, ka ba masu sauraro dama su yi kalamai a kan dalilin da ya sa suke ganin batun da ke gabatarwar zai ratsa zukatan mutanen da ke yankinsu.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Mene Ne Muka Cim Ma? Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka amfana daga bin shawarar da ke talifin nan “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Nuna wa Mutane Cewa Mun Damu da Su.” Ka ba su dama su faɗi labarai masu daɗi da suka samu.
Waƙa ta 119 da Addu’a