“Ban Sake Samunsa a Gida Ba!”
Kai ma ka taɓa yin wannan furucin game da wani da ya yi sha’awar saƙonmu? Ko da yake ka koma wurin mutumin sau da sau don ka yi ban ruwa ga iri na gaskiya da ka shuka a zuciyarsa, ka kasa samunsa. (1 Kor. 3:6) A wasu lokatai, ƙwararrun masu shela sukan rubuta wasiƙa ga mutumin da suka kasa samunsa a gida, ko kuma su ɗan yi wani rubutu su ajiye a ƙofarsa. Wasu masu shela sun san cewa mai yiwuwa zai yi wuya su sake samun wanda suke masa wa’azi a gida, saboda haka, sukan tambaye shi lambarsa da basira cewa: “Zan iya kiranka a waya?” Za mu iya ƙirga koma ziyara a duk lokacin da muka sake ziyartan wani ko mun sake yi masa wa’azi ta hanyar wasiƙa ko waya ko saƙon imel ko saƙon tes ko kuma muka bar masa ’yar wasiƙa a bakin ƙofarsa. Ko da wani ba ya cika zama a gida, zai yiwu mu ci gaba da tattaunawa da shi.