Ku Bi Gurbin Annabawa—Zafaniya
1. A wane irin yanayi ne Zafaniya ya yi hidimar annabi, kuma me ya sa ya kamata mu bi misalinsa?
1 A ƙarni na bakwai kafin zamaninmu, Isra’ilawa a Yahudiya sun shiga wani halin bauta wa Baal a fili. Ba a daɗe da kashe wannan mugun sarki Amon ba, kuma yanzu matashin nan Josiah ne yake sarauta. (2 Laba. 33:21–34:1) A wannan lokacin ne Jehobah ya aiki Zafaniya ya yi shelar hukuncinsa. Mai yiwuwa Zafaniya ya fito daga zuriyar sarakunan Yahudiya ne, amma bai bar hakan ya sa shi ya sanyaya muhimmancin saƙon hukunci da Jehobah ya ce ya idar ga sarakunan Yahudiya ba. (Zaf. 1:1; 3:1-4) Mu ma ya kamata mu kasance da gaba gaɗi kamar Zafaniya kuma mu ƙi barin dangantakarmu da danginmu ta shafi ibadarmu ga Jehobah a hanyar da ba ta dace ba. (Mat. 10:34-37) Wane saƙo ne Zafaniya ya idar, kuma mene ne sakamakon?
2. Mene ne ya wajaba mu yi don Jehobah ya cece mu a ranar hukuncinsa?
2 Ku Biɗi Jehobah: Jehobah ne kaɗai zai iya ceton mutane a ranar hukuncinsa. Hakan ne ya sa Zafaniya ya aririci mutanen Yahudiya su biɗi Jehobah, su biɗi adalci kuma su biɗi tawali’u kafin lokaci ya ƙure. (Zaf. 2:2, 3) Haka ma yake a yau. Kamar Zafaniya, muna ƙarfafa mutane su biɗi Jehobah. Amma, mu ma muna bukata mu ƙudurta cewa ba za mu daina “bin Ubangiji” ba. (Zaf. 1:6) Maimakon haka, muna biɗan Jehobah ta wajen yin nazarin Kalmarsa sosai da kuma neman ja-gorarsa. Muna biɗan adalci ta wajen kasancewa da ɗabi’a mai kyau. Ƙari ga haka, muna biɗan tawali’u ta wajen bin ja-gorar ƙungiyar Jehobah cikin sauƙin kai.
3. Me ya sa zai dace mu kasance da ra’ayi mai kyau a hidimarmu?
3 Sakamako Masu Kyau: Hukuncin da Zafaniya ya sanar ya ratsa zuciyar wasu a ƙasar Yahudiya. Mafi muhimmanci a cikin mutanen shi ne Josiah, wanda ya soma biɗan Jehobah tun yana yaro. Daga baya, Josiah ya yaƙi bautar gumaka a ƙasar gaba ɗaya. (2 Laba. 34:2-5) Ko da yake a yau wasu wuraren da muke shuka iri na Mulkin suna kama da bakin hanya ko duwatsu ko kuma ƙayoyi, wasu kuma suna kama da ƙasa mai kyau wanda yake ba da amfani mai kyau. (Mat. 13:18-23) Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da yi mana albarka yayin da muke shuka iri na Mulkinsa da himma.—Zab. 126:6.
4. Me ya sa zai dace mu riƙa sauraron ranar Jehobah?
4 Wasu cikin mutanen Yahudiya sun aza a zuciyarsu cewa Jehobah ba zai taɓa ɗaukan mataki ba. Amma Jehobah ya ba da tabbaci cewa babbar ranarsa ta kusa. (Zaf. 1:12, 14) Waɗanda suka nemi mafaka a wurinsa ne kawai za su tsira. (Zaf. 3:12, 17) Yayin da muke ‘dakatawa’ ko kuma sauraron ranar Jehobah, muna fata cewa za mu ci gaba da jin daɗin bauta wa Allahnmu mai girma tare da ’yan’uwanmu!—Zaf. 3:8, 9.