Tsarin Ayyuka na Makon 28 ga Yuli
MAKON 28 GA YULI
Waƙa ta 58 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 10 sakin layi na 18-21 da akwatin da ke shafi na 106 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Littafin Lissafi 1-3 (minti 10)
Na 1: Littafin Lissafi 3:21-38 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Waye Ne Allahnka?—lr babi na 27 (minti 5)
Na 3: Albarkar da Mulkin Allah Zai Kawo—td 33A (minti 5)
Taron Hidima:
Waƙa ta 89
Minti 10: Kun Shirya don Sabuwar Shekarar Makaranta? Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi wasu ƙalubalen da matasa Kiristoci suke fuskanta a makaranta. Ka bayyana yadda iyaye za su iya yin amfani da dandalinmu da kuma wasu littattafanmu wajen shirya yaransu. (1 Bit. 3:15) Ka tattauna ƙalubale ɗaya ko biyu da yara suke fuskanta a makaranta kuma ka bayyana wasu shawarwari da ƙungiyarmu ta bayar a kan yadda za su shawo kan ƙalubalen. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka taɓa yin wa’azi a makaranta.
Minti 10: Ganawa da Sakatare. Waɗanne ayyuka ne kake yi a matsayin sakatare? Ta yaya masu kula da rukunin wa’azi da kuma masu shela za su taimaka maka don ka haɗa rahoton hidimar ikilisiya daidai kuma a kan lokaci? Ta yaya rahoton da aka rubuta shi daidai zai taimaka wa dattawa da mai kula da da’ira da kuma ofishin reshe wajen ba da taimakon da ake bukata?
Minti 10: “Ku Bi Gurbin Annabawa—Zafaniya.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 70 da Addu’a