Tsarin Ayyuka na Makon 7 ga Yuli
MAKON 7 GA YULI
Waƙa ta 99 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 9 sakin layi na 21-24 da akwatin da ke shafi na 96 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Levitikus 17-20 (minti 10)
Na 1: Levitikus 19:19-32 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Yesu Kristi Ɗan Allah Ne da Kuma Sarkin da Aka Naɗa—td 43A (minti 5)
Na 3: Kada Ka Zama Ɓarawo!—lr babi na 24 (minti 5)
Taron Hidima:
Waƙa ta 14
Minti 10: Ku Ba Da Mujallu a Watan Yuli. Tattaunawa. Ka sa a yi amfani da gabatarwar da ke wannan shafin don a nuna yadda za a iya ba da mujallun. Bayan haka, ka tattauna gabatarwar daga farko har ƙarshe. A ƙarshe, ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su karanta mujallun da kyau kuma su ƙoƙarta su rarraba mujallun da himma.
Minti 10: Bukatun Ikilisiya.
Minti 10: Mene Ne Muka Cim Ma? Sakatare ne zai tattauna wannan sashen. Ka faɗi abubuwan da aka cim ma a lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kuma ka yaba wa ’yan’uwa don ƙoƙarin da suka yi. Ka ba masu sauraro dama su faɗi abubuwa masu daɗi da suka shaida yayin da suke rarraba takardar gayyata ko kuma lokacin da suke hidimar majagaba na ɗan lokaci.
Waƙa ta 123 da Addu’a