Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 6/14 p. 7
  • Bitar Makarantar Hidima ta Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bitar Makarantar Hidima ta Allah
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 6/14 p. 7

Bitar Makarantar Hidima ta Allah

Za a tattauna tambayoyin da ke gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 30 ga Yuni, 2014.

  1. Me ya sa yake da muhimmanci mu bi ƙa’idar da ke littafin Fitowa 23:2 sa’ad da muke so mu yi nishaɗi ko kuma mu shaƙata? [5 ga Mayu, w11 7/15 shafuffuka na 10-12 sakin layi na 3-7]

  2. Mene ne ya nuna cewa dokar da aka ba firistoci cewa su tsabtace kansu kafin su miƙa hadaya ga Jehobah tana da muhimmanci sosai, kuma ta yaya ta zama abin tuni ga bayin Allah a yau? (Fit. 30:18-21) [19 ga Mayu, w96 7/1 shafi na 15 sakin layi na 9]

  3. Me ya sa ba a yi wa Haruna horo domin ɗan maraƙin da ya ƙera ba? (Fit. 32:1-8, 25-35) [19 ga Mayu, w04 7/1 shafi na 27 sakin layi na 4]

  4. Me ya sa ya kamata mu yi bimbini a kan ayyukan Jehobah da suka nuna cewa shi mai ƙauna ne da kuma alheri? (Fit. 34:12) [26 ga Mayu, w10 8/15 shafi na 22 sakin layi na 6]

  5. Me ya sa labarin Bezalel da Oholiab abin ƙarfafa ne a gare mu? (Fit. 35:30-35) [26 ga Mayu, w10 9/15 shafi na 10 sakin layi na 13]

  6. Mene ne “allo . . . mai-tsarki,” wato alamar keɓewa da ke jikin rawanin babban firist na Isra’ila yake tuna masa, kuma mene ne wannan alamar take koya mana game da keɓe kai da muka yi? (Fit. 39:30) [2 ga Yuni, w01 2/1 shafi na 18 sakin layi na 2-3]

  7. Wane hakki ne dukan Kiristoci suke da shi idan ya zo ga batun kai ƙaran Kirista da ya yi zunubi mai tsanani? (Lev. 5:1) [9 ga Yuni, w12 2/15 shafi na 22 sakin layi na 15]

  8. Me ya sa ake yin hadaya ta salama a zamanin Isra’ilawa, kuma mene ne wannan tanadin yake wakilta a gare mu? (Lev. 7:31-33) [16 ga Yuni, w12 1/15 shafi na 19 sakin layi na 11-12]

  9. Mene ne mai yiwuwa ya sa ’ya’yan Haruna, wato Nadab da Abihu suka yi zunubi, kuma waɗanne darussa ne muka koya daga labarinsu? (Lev. 10:1, 2, 9) [23 ga Yuni, w04 7/1 shafi na 29 sakin layi na 6-8]

  10. Me ya sa haihuwa take sa mace ta zama “marar-tsarki”? (Lev. 12:2, 5) [23 ga Yuni, w04 7/1 shafi na 30 sakin layi na 2]

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba