Tsarin Ayyuka na Makon 12 ga Mayu
MAKON 12 GA MAYU
Waƙa ta 49 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 7 sakin layi na 1-8 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Fitowa 27-29 (minti 10)
Na 1: Fitowa 29:19-30 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Hanyar Yin Farin Ciki—lr babi na 17 (minti 5)
Na 3: Allah Ba Ya So Mu Haɗa Bautarmu da Na Wasu Addinai—td 19A (minti 5)
Taron Hidima:
Waƙa ta 75
Minti 15: Al’ummai Duka Za Su Gangaro Wurinsa. (Isha. 2:2) Ka gana da masu shela guda biyu. Ɗaya a cikinsu ya zama wanda ya daɗe yana bauta wa Jehobah, ɗayan kuma ya zama wanda bai daɗe sosai ba. Wane abu ne ya sa suka yi sha’awar gaskiya? Waɗanne ƙalubale ne suka fuskanta? Wane abu ne suka ji daɗinsa a ranar da suka fara halartan taro? Mene ne ya faru a rana ta farko da suka fita wa’azi? Ta yaya wasu a cikin ikilisiya suka taimaka musu su manyanta a dangantakarsu da Allah?
Minti 15: “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Hanyar Shirya Gabatarwarmu.” Tattaunawa. Ka sa a yi gajeren gwaji da ya ƙunshi sassa biyu. Na farko, a nuna wani mai shela yana wa’azi, amma bai shirya gabatarwarsa da kyau ba, sa’an nan a na biyu, ya yi amfani da gabatarwa da ya shirya da kyau. Idan da lokaci, ka ɗan tattauna wasu muhimman bayanai daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafuffuka na 215-219.
Waƙa ta 117 da Addu’a