Tsarin Ayyuka na Makon 27 ga Janairu
MAKON 27 GA JANAIRU
Waƙa ta 106 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 2 sakin layi na 1-11 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Farawa 17-20 (minti 10)
Na 1: Farawa 17:18–18:8 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Shin Za Ka Iya Gane Annabawan Ƙarya?—td 4A (minti 5)
Na 3: Allah Yana da Suna—lr babi na 4 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 121
Minti 5: Ku Soma Nazari da Mutane a Ranar Asabar ta Farko. Jawabi. Ka ambata shirin da aka yi don fita wa’azi a ranar Asabar ta farko a watan Fabrairu kuma ka ƙarfafa kowa ya fito a ranar. Ka sa a yi amfani da bayanin da ke shafi na 4 wajen yin gajeren gwaji.
Minti 15: Waɗanne Maƙasudai Ne Ka Kafa? Tattaunawa bisa ga bayanin da ke littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, sakin layi na 2 a shafi na 117 zuwa ƙarshen babin. Ka gana da mai shela ɗaya ko biyu da suka kafa maƙasudin yin hidimar majagaba kuma suka cim ma hakan. Mene ne ’yan’uwa suka yi don su ƙarfafa su? Waɗanne ƙalubale ne suka fuskanta? Waɗanne albarka ne suka samu?
Minti 10: “Za Ku Iya Soma Nazari da Waɗanda Kuka Saba Ba Mujallunmu.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka soma nazari da wani da suka saba ba mujallu.
Waƙa ta 103 da Addu’a