Tsarin Ayyuka na Makon 25 ga Nuwamba
MAKON 25 GA NUWAMBA
Waƙa ta 122 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
jl Darasi na 11-13 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Yaƙub 1-5 (minti 10)
Na 1: Yaƙub 1:22–2:13 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Yadda Ƙauna Take Shawo Kan Tsoro—1 Yoh. 4:16-18 (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Muke Mutuwa?—td 34A (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 95
Minti 10: Yadda Za Mu Iya Ba da Mujallunmu a Watan Disamba. Tattaunawa. Ka yi amfani da sakan 30 zuwa minti ɗaya don ka ambata dalilin da ya sa mutane a yankinku za su so mujallun. Bayan haka, ka ba masu sauraro dama su faɗi tambayar da za su yi da za ta sa mutane su so mujallar, sa’an nan su faɗi nassin da za su karanta bisa ga jigon da ke bangon gaba na Hasumiyar Tsaro ɗin. Ka yi hakan ma da Awake! kuma idan da sauran lokaci, ka yi hakan da wani talifi dabam a cikin Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! Ka sa a nuna yadda za a iya ba da kowacce cikin mujallun.
Minti 10: A Wace Hanya Ce Ya Kamata Ka Mai da Martani? Jawabi bisa ga bayanin da ke cikin littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 69, sakin layi na 1-5. Ka sa a yi gwaji da zai nuna yadda mai shela zai iya ba da amsa ga ɗalibinsa da ke bukatar tsai da wata shawara. Ɗalibin ya yi masa tambaya cewa, “Da a ce kai ne a cikin yanayina, da me za ka yi?”
Minti 10: “Kalmar Allah Tana da Iko.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka sanar da kwanan watan ranar taro na musamman idan ka san da hakan.
Waƙa ta 45 da Addu’a