Tsarin Ayyuka na Makon 2 ga Disamba
MAKON 2 GA DISAMBA
Waƙa ta 123 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
jl Darasi na 14-16 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Bitrus 1–2 Bitrus 3 (minti 10)
Na 1: 1 Bitrus 2:18–3:7 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ya Kamata Mu Ji Tsoron Matattu Ne?—td 34B (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Muka Ba da Gaskiya Cewa Yesu Ne Almasihu—Luk 24:44; Gal. 4:4 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 116
Minti 5: Ku Soma Nazari da Mutane a Ranar Asabar ta Farko. Jawabi. Ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a ranar Asabar ta farko a watan Disamba. Ka sa a yi amfani da talifin da ke bangon baya na Hasumiyar Tsaro wajen yin gajeren gwaji don a nuna yadda za a iya soma nazari da mutane.
Minti 15: Kun Gwada Yin Amfani da Su Kuwa? Tattaunawa. Ka ɗan tattauna bayanan da ke waɗannan talifofin a cikin Hidimarmu ta Mulki: “Dandalinmu na Intane—An Tsara Shi Ne don ’Yan’uwa da Kuma Wasu Su Amfana” (km 12/12), “Ku Yi Amfani da Bidiyo Wajen Koyarwa,” da kuma “Wa Zai Fi Son Wannan Talifin?” (km 5/13). Sa’an nan ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka amfana daga bayanan da ke cikin waɗannan talifofin.
Minti 10: Bukatun Ikilisiya.
Waƙa ta 12 da Addu’a