Kada Ku Ja da Baya
1. Mene ne yake bukatar gaba gaɗi kafin mu yi shi, kuma me ya sa?
1 Ka taɓa ja da baya daga yin wa’azi a makaranta domin kana jin tsoro cewa za a yi maka ba’a? Kana bukatar ka kasance da gaba gaɗi don ka yi magana, musamman idan kana jin kunya. Mene ne zai taimaka maka?
2. Idan ya zo ga batun yin wa’azi a makaranta, yaya za a yi amfani da sanin ya kamata?
2 Ka Yi Amfani da Sanin Ya Kamata: Ko da yake za a ɗauka cewa makaranta ne wurin da kake da zarafi na musamman don yi wa mutane wa’azi, ka tuna cewa ba za ka soma tattauna abubuwa na ruhaniya da kowa yadda kake yi sa’ad da kake wa’azi gida gida ba. Ka yi amfani da sanin ya kamata don ka san sa’ad da za ka yi magana. (M. Wa. 3:1, 7) Abin da aka tattauna a cikin aji ko kuma aikin makaranta zai iya ba ka zarafin furta imaninka. Ko kuwa wani ɗan ajinku zai iya tambaye ka dalilin da ya sa ba ka saka hannu a yin wasu ayyuka. Wasu Kiristoci sun gaya wa malamansu a farkon shekarar makaranta cewa su Shaidun Jehobah ne kuma sun ba malaman littattafai da ke bayyana imaninmu. Wasu sun ajiye littattafai a kan teburinsu don abokan makarantarsu su yi tambayoyi game da littattafan.
3. Yaya za ka yi shiri don yin wa’azi a makaranta?
3 Ku Kasance a Shirye: Idan ka yi shiri, za ka daɗa kasancewa da gaba gaɗi. (1 Bit. 3:15) Saboda haka, ka yi ƙoƙari ka yi tunani a kan tambayoyi da za a iya yi maka, kuma ka yi tunanin yadda za ka iya amsawa. (Mis. 15:28) Idan zai yiwu, ka ajiye Littafi Mai Tsarki da wasu littattafai kamar su Reasoning From the Scriptures da Questions Young People Ask—Answers that Work, littafi na ɗaya da na biyu da littattafai a kan halitta a makaranta, don ka yi amfani da su sa’ad da kake bukata. Ka gaya wa iyayenka su haɗa sashen gwaji sa’ad da kuke bautarku ta iyali.
4. Me ya sa za ka ci gaba da yin wa’azi a makaranta?
4 Ka Kasance da Ra’ayin da Ya Dace: Kada ka yi tsammani cewa abokan makarantarka za su yi maka ba’a a kowane lokacin da ka yi wa’azi. Wataƙila wasu za su so ka don gaba gaɗinka kuma su saurara. Amma kada ka yi sanyin gwiwa idan ba wanda ya saurara. Jehobah zai yi farin ciki cewa ka yi ƙoƙari. (Ibran. 13:15, 16) Ka ci gaba da roƙonsa ya taimaka maka ka ‘faɗi magana da ƙarfin zuciya duka.’ (A. M. 4:29; 2 Tim. 1:7, 8) Ka yi tunanin yadda za ka yi farin ciki sa’ad da wani ya saurare ka. Wannan yana iya zama ɗan’uwanka mai bauta wa Jehobah a nan gaba!