Tsarin Ayyuka na Makon 17 ga Oktoba
MAKON 17 GA OKTOBA
Waƙa ta 85 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 70 zuwa 74 (minti 25)
□ Makarantar Hidima Ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Misalai 12-16 (minti 10)
Na 1: Misalai 15:1-17 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ta Yaya Karɓaɓɓun Addu’o’i Suke Kama da Turaren Ƙonawa ga Jehobah?—Zab. 141:2; R. Yoh. 5:8 (minti 5)
Na 3: Menene Muhimmancin Warkarwa na Ruhaniya?—td 42A (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 12
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Mene ne Muka Koya? Tattaunawa. Ka sa a karanta Matta 5:11, 12, 14-16, 23, 24. Ka tattauna yadda waɗannan ayoyin za su iya taimaka mana a hidimarmu.
Minti 10: Bari Mai Gidan Ya Gani da Idanunsa. Tattaunawa da aka ɗauko daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 145. Ka sa a yi gajeren gwaji da ya nuna yadda mai shela ya koma ziyara wurin wani da babu sunan Allah a nasa Littafi Mai Tsarki.
Minti 10: “Kada Ku Ja da Baya.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka sa manya da yara su faɗi labarin da suka samu sa’ad da suka yi wa’azi a makaranta.
Waƙa ta 80 da Addu’a