Idan Kuna Bukatar Littattafai na Wani Yare da Gaggawa
A wasu lokatai mukan sadu da mutane da suke son su karanta littattafanmu a wani yare da ikilisiyarmu ba ta da su. Ka san cewa idan kana da Intane da kuma na’urar buga littattafai, za ka iya buga littattafai a harsuna kusan ɗari huɗu da kanka? Ga yadda za ka iya yin hakan:
• Ka shiga Duniyar gizonmu na www.watchtower.org.
• Akwai wasu jerin harsuna a hannun dama na dandalin. Ka danna hoton kwallon duniya da ke wurin don ka ga dukan harsuna da ke wurin.
• Ka danna yaren da kake so. Wani shafi zai buɗo wanda zai nuna littattafai da za ka iya bugawa, kamar su warƙoƙi, mujallu da talifofi. Tun da an rubuta wannan shafin ne a harshen da ka zaɓa, kada ka damu idan ba ka fahimci jigon ba.
• Ka danna kowanne abu da kake so. Abin da ka danna zai buɗo maka kuma za ka iya buga shi ta wurin danna boturin da aka rubuta print, wato, buga a dandalin.
Duniyar gizonmu tana ɗauke da wasu cikin littattafanmu, za a iya samun ƙarin littattafai da muke da su ta hanyar ikilisiya. Da zarar ka ga cewa wani yana son saƙonmu, ya fi dacewa ka karɓi littattafai daga kantar littattafai.