Tsarin Ayyuka na Makon 25 ga Oktoba
MAKON 25 GA OKTOBA
Waƙa ta 2
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 10 sakin layi na 1-9
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Labarbaru 12-15
Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 14
Minti 8: Sanarwa. “Idan Kuna Bukatar Littattafai na Wani Yare da Gaggawa.” Jawabi.
Minti 12: Haɗin Kanmu a Dukan Duniya Yana Ɗaukaka Jehobah. Jawabi da aka ɗauko daga littafin nan Organized To Do Jehovah’s Will, shafi na 165, sakin layi na 2, zuwa kan magana da ke shafi na 168. Ka sa wasu daga masu sauraro su ba da labarai da aka buga da ya nuna yadda haɗin kanmu da ƙauna suka sa aka ba da shaida.
Minti 15: Ku Riƙa Sadaukar da Kai. (Luk 9:23) Tattaunawa da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 2007, shafi na 21, sakin layi na 10 da 11. Ka haɗa da wasu labarai da aka buga ko kuma waɗanda suka faru a yankin da suka nuna misalin sadaukar da kai a hidima. Ka gayyaci masu sauraro su ba da kalami a kan darussa da suka koya.
Waƙa ta 66