Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima Ta Allah a makon 25 ga Oktoba, 2010. Mai kula da makarantar zai gabatar da bita ta minti 20 bisa ga abin da aka nazarta daga makon 6 ga Satumba zuwa 25 ga Oktoba, 2010.
1. Me ya sa Jehobah ya harbi Azariya (wato Uzziya,) da kuturta? (2 Sar. 15:1-6) [w05 8/1 shafi na 30 sakin layi na 4]
2. Menene za mu iya koya daga kasa harba kibiya fiye da sau uku da Yehowash ya yi? (2 Sar. 13:14-19) [w05 8/1 shafi na 30 sakin layi na 11]
3. Shin Hezekiya ya yi ƙawanci ne da ƙasar Masar? (1 Sar. 18:19-21, 25) [w05 8/1 shafi na 30 sakin layi na 5]
4. Me ya sa aka kira Jehobah ‘mai-sifanta’ nufinsa? (2 Sar. 19:25) [w99 9/1 shafi na 3 sakin layi na 3]
5. Wane gabagaɗi ne muke da shi daga 2 Sarakuna 24:3, 4? [w05 8/1 shafi na 30 sakin layi na 13]
6. Me ya sa 1 Sama’ila 16:10, 11 suka ce Dauda ɗan Yesse na takwas ne, amma Ezra ya ce shi na bakwai ne? (1 Laba. 2:15) [w05 10/1 shafi na 29 sakin layi na 1]
7. Ta yaya za mu iya yin koyi da misalin Gileadawa na dā? (1 Laba. 5:10, 18-22) [w05 10/1 shafi na 29 sakin layi na 7]
8. Wane darassi ne za mu iya koya daga Lawiyawa masu tsare kofa? (1 Laba. 9:26, 27) [w05 10/1 shafi na 29 sakin layi na 8]
9. Menene muhimmancin yin waƙa a Isra’ila ta dā? (1 Laba. 9:33) [w94 11/1 shafi na 12 sakin layi na 8; shafi na 13 sakin layi na 13]
10. Menene bai dace ba da yadda Dauda ya aikata a 1 Labarbaru 13:11? [w05 8/1 shafi na 11]