Idonka Sarai ne Kuwa?
1. Menene ‘idonmu ya kasance sarai’ yake nufi?
1 Abubuwan da idanunmu suke gani suna tasiri a kan halinmu. Shi ya sa kalaman Yesu suka dace: “Idan idon sarai ne, dukan jikinka za ya zama cike da haske.” (Mat. 6:22) Idan idonmu “sarai” ne a ruhaniya kamar yadda Yesu ya faɗa, zai mai da hankali ga cim ma abu ɗaya, wato, yin nufin Allah. Za mu sa Mulkin farko a rayuwarmu kuma ayyuka da abubuwan duniya da ba ma bukata ba za su shafi hidimarmu ba.
2. Menene zai iya raunana tunaninmu, amma menene zai taimaka mana?
2 Bukatan Bincika Kai: Tallace-tallace da kuma abin da wasu suke da shi zai iya raunana tunaninmu na sanin abubuwan da muke bukata. Kafin ka biɗi wani abu ko kuma ka sayi wani abu da zai ci lokacinka, kuɗi, ko kuma kuzari, zai dace ka ‘yi lissafi’ ta wajen yi wa kanka wannan tambayar, ‘Wannan zai kyautata hidimata ga Jehobah ko zai raunana ta?’ (Luk 14:28; Filib. 1:9-11) Yana da kyau kuma mu riƙa yin tunani a kai a kai game da yadda za mu iya daɗa sauƙaƙa rayuwarmu don mu ƙara saka hannu a hidima.—2 Kor. 13:5; Afis. 5:10.
3. Menene muka koya daga wata ’yar’uwa wadda ta yi canje-canje don ta sauƙaƙa rayuwarta?
3 Sa’ad da wata ’yar’uwa ta soma hidimar majagaba na kullum, ta yanke shawarar ci gaba da aikinta na cikakken lokaci ko da yake idan ta yi aiki na ɗan lokaci za ta samu isasshen kuɗi na kula da bukatunta. Daga baya ta ce: “Babu wanda zai iya bauta wa shugaba biyu. Na saɗaukar da abin da nake so don in kula da ainihin abin da nike bukata. Na fahimci cewa abin duniya suna tsufa, kuma zan galabaita idan na ci gaba da biɗarsu.” Yanayinta ya sa ta yi canje-canje don sauƙaƙa rayuwarta, ta canja aikin da take yi, kuma hakan ya sa ta ci gaba da yin hidimar majagaba.
4. Me ya sa kasancewa da idon da sarai ne yake da muhimmanci?
4 Gaggawar da ke tattare da lokacinmu ya sa kasancewa da idon da sarai ne yana da muhimmanci. Kowacce rana da ta wuce tana jawo mu kusa da ƙarshen wannan zamanin da kuma somawar sabuwar duniya ta Allah. (1 Kor. 7:29, 31) Ta wajen mai da hankali ga aikin wa’azi, za mu iya ceto kanmu da waɗanda suka saurare mu.—1 Tim. 4:16.