Ka Amfana Daga Yin Nazarin Littafin nan Ka Kusaci Jehovah
1 Mun yi farin cikin samun littafin nan Ka Kusaci Jehovah a Taron Gunduma na “Masu Shelar Mulki da Himma.” Mutane da yawa sun karanta littafin nan da nan. Babu shakka, jigo na shekara ta 2003: ‘Ku kusaci Allah, shi kuwa za ya kusace ku’ ya motsa mutane da yawa su yi hakan.—Yaƙ. 4:8.
2 Za mu soma nazarin littafin nan Ka Kusaci Jehovah a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya a makon 6 ga Yuni. Ta yaya za mu amfana sosai daga nazarinmu? Yin shiri na da muhimmanci. Za a yi nazarin babi ɗaya a makonni biyu, hakan zai sa a yi nazarin sakin layi kaɗan a kowanne mako. Wannan zai ba ka lokaci mai yawa don ka ba da kalami daga zuciya da ka samo daga nazarinka da kuma bimbini daga littafin. Ƙari ga hakan, za a yi nazarin sakin layi kaɗan a makonnin da za a yi bitar ƙarshen kowanne babi, don a samu lokacin yin amfani da sashe na musamman na littafin.
3 Somawa daga babi na biyu, akwai akwati mai jigo “Tambayoyi don Bimbini” da ke ƙarshen kowanne babi. Bayan an kammala sakin layi na ƙarshe a babin, mai gudanar da nazarin zai sa ’yan’uwa su tattauna akwatin. Zai sa waɗanda suke cikin ikilisiyar su yi kalami a kan abubuwa masu kyau da ke cikin Nassosi da suka yi bimbini a kai. (Mis. 20:5) Ƙari ga tambayoyin da aka yi a akwatin, zai iya yin wasu tambayoyi kamar su: “Mene ne wannan bayanin ya koya maka game da Jehobah? Ta yaya ya shafi rayuwarka? Ta yaya za ka yi amfani da shi don ka taimaki mutane?” Manufar yin waɗannan tambayoyin shi ne ya sa ’yan’uwa su yi kalaman da ke zuciyarsu, ba kawai ya yi tambayoyi a kan ƙananan bayanai ba.
4 Ka Kusaci Jehovah littafi ne na musamman. Ko da yake dukan littattafan da “bawan nan mai aminci” suka wallafa suna ɗaukaka Jehobah, amma wannan littafin ya mai da hankali gabaki ɗaya ga tattauna halayen Jehobah. (Mat. 24:45-47) Zarafi mai ban sha’awa yana jiranmu! Za mu amfana sosai daga yin nazari mai zurfi na halayen Jehobah. Muna fata cewa nazarin wannan littafin zai sa mu kusaci Ubanmu na samaniya, kuma za mu daɗa ƙwarewa wajen taimaka wa mutane su yi hakan.