Tsarin Ayyuka na Makon 21 ga Fabrairu
MAKON 21 GA FABRAIRU
Waƙa ta 97 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh rataye shafi na 219-220 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Nehemiya 12-13 (minti 10)
Na 1: Nehemiya 13:15-22 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ma’anar Bauta wa Jehobah Allah Shi Kaɗai—Fit. 20:5 (minti 5)
Na 3: Tilas Ne Gamin Aure ya Zama da Daraja—td 7A (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 133
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Jehobah Ba Zai Bar Amintattunsa Ba. (Zab. 37:28) Tattaunawa da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2010, shafuffuka na 12 zuwa 15. Ka nanata labaran da ke cikin talifin. Bayan ka tattauna kowanne labari, ka gayyaci masu sauraro su yi kalami a kan darussan da suka koya.
Minti 10: Yadda Za a Yi Kammalawa Mai Kyau a Hidimar Fage. Jawabi da aka ɗauko daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 221, sakin layi na 5, zuwa ƙarshen shafi na 222. Ka sa a yi gajeren gwaji a kan bayani ɗaya ko biyu daga cikin littafin.
Minti 10: “Ka Amfana Daga Yin Nazarin Littafin nan Ka Kusaci Jehovah.” Tattaunawar talifin da dattijo zai yi. Sa’ad da kake tattauna sakin layi na 3, ka karanta kuma ka tattauna shafi na 25 sakin layi na 23 na littafin.
Waƙa ta 31 da Addu’a