‘Ka Kusaci Allah’
‘Ka kusaci Allah, shi kuwa za ya kusace ka.’—YAƘUB 4:8.
1, 2. (a) Wace da’awa ce mutane suke yi sau da yawa? (b) Wace ƙarfafa ce Yaƙub ya bayar, me ya sa ake bukatarta?
“ALLAH yana tare da mu.” Waɗannan kalmomi suna rubuce a kan-sarki na ƙasashe dabam dabam har ma da inifam na sojoji. A kan sulalla da kuma kuɗaɗe na zamani an rubuta “mun dogara ga Allah.” Yana da sauƙi mutane su yi da’awar suna da dangantaka ta kusa da Allah. Amma ba za ka yarda ba cewa, kasancewa da irin wannan dangantaka tana bukatar fiye da maganar baki kawai ko kuma rubutu don wasu su gani?
2 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa zai yiwu a kasance da dangantaka da Allah. Amma ana bukatar ƙoƙari. Wasu Kiristoci shafaffu ma a ƙarni na farko sun bukaci su ƙarfafa dangantakarsu da Jehovah Allah. Kirista mai kula, Yaƙub, ya yi wa wasu kashedi game da sha’awoyinsu na jiki da rashin tsabta na ruhaniya. A cikin wannan kashedin, ya ba da wannan ƙarfafar: ‘Ku kusaci Allah, shi kuwa za ya kusace ku.’ (Yaƙub 4:1-12) Menene Yaƙub yake nufi da ku ‘kusaci’?
3, 4. (a) Menene ƙila furcin nan ‘ku kusaci Allah’ ya tunasar wa waɗanda Yaƙub ya rubuta musu wasiƙa a ƙarni na farko? (b) Me ya sa za mu tabbata cewa kusantar Allah tana yiwuwa?
3 Yaƙub ya yi amfani da furci da waɗanda suka karanta wasiƙarsa suka sani. Dokar Musa ta bai wa firistoci takamammun umurnai game da yadda za su ‘zo kusa da,’ ko kuma su kusaci Jehovah a madadin mutanensa. (Fitowa 19:22) Da haka an tunasar da waɗanda Yaƙub ya rubuta wa wasiƙa cewa kusantar Jehovah ba abin da za a ɗauka da wasa ba ne. Jehovah ne ya fi kome matsayi.
4 A wani ɓangare kuma, wani manazarcin Littafi Mai Tsarki ya lura cewa, “wannan ƙarfafar [a Yaƙub 4:8] ya bayyana bege mai ƙarfi.” Yaƙub ya sani cewa koyaushe Jehovah yana gayyatar mutane ajizai su kusace shi. (2 Labarbaru 15:2) Hadayar Yesu ta buɗe hanyar kusantar Jehovah sosai. (Afisawa 3:11, 12) A yau, an buɗe wa mutane miliyoyi hanyar kusantar Allah. To, ta yaya za mu yi amfani da wannan zarafi mai kyau? Za mu bincika hanyoyi uku da za mu iya kusantar Jehovah Allah.
Ka Ci Gaba da Samun ‘Sanin’ Allah
5, 6. Ta yaya misalin matashi Sama’ila ya kwatanta abin da “samun sanin” Allah ya ƙunsa?
5 In ji Yohanna 17:3, Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” Yawancin fassara na wannan ayar sun ɗan bambanta da New World Translation. Maimakon su ce “samun sanin” Allah, suka fassara aikatau ɗin “san” Allah ko kuma “sanin” Allah. Amma, manazarta da yawa sun lura cewa kalmar da aka yi amfani da ita a Helenanci na asali ta ƙunshi ma’ana fiye da haka—abu ne da za a ci gaba da yi da zai kai ga abuta na kusa da juna.
6 Sanin Allah ba sabon ra’ayi ba ne a zamanin Yesu. Alal misali, a Nassosin Ibrananci, mun karanta cewa sa’ad da Sama’ila yake yaro, “ba ya rigaya ya san Ubangiji ba.” (1 Samu’ila 3:7) Wannan yana nufi ne cewa Sama’ila bai san kome ba game da Allahnsa? A’a. Iyayensa da firistoci babu shakka sun koyar da shi sosai. Amma, kalmar Ibrananci da aka yi amfani da ita a wannan ayar, in ji wani manazarci, za a iya “amfani da ita ga aboki na kusa.” Sama’ila bai san Jehovah sosai ba tukuna, kamar yadda za ya san shi daga baya sa’ad da ya zama kakakin Jehovah. Yayin da Sama’ila ya ci gaba da girma, ya zo ga sanin Jehovah sosai, ya sami dangantaka ta kusa da shi.—1 Samu’ila 3:19, 20.
7, 8. (a) Me ya sa ba za mu yi sanyin gwiwa ba don koyarwar Littafi Mai Tsarki mai zurfi? (b) Waɗanne ne wasu zurfafar gaskiya ta Kalmar Allah da ya kamata mu yi nazarinsu?
7 Kana samun sanin Jehovah don ka sarƙu da shi sosai? Domin ka yi haka, kana bukatar ka “yi marmarin” abinci na ruhaniya da Allah yake bayarwa. (1 Bitrus 2:2) Kada ka gamsu da koyarwa na sama sama. Ka yi ƙoƙari ka san wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki masu zurfi. (Ibraniyawa 5:12-14) Irin waɗannan koyarwan suna kashe maka gwiwa ne, domin kana tsammani suna da wuya ainun? Idan haka ne, ka tuna cewa Jehovah ne ‘Mai Koyarwa Mai Girma.’ (Ishaya 30:20) Ya san yadda zai idar da zurfafan gaskiya zuwa cikin zukatan mutane ajizai. Zai albarkaci ƙoƙarinka don ka fahimci abin da yake koya maka.—Zabura 25:4.
8 Me ya sa ba za ka binciki kanka ba game da wasu “zurfafa na Allah”? (1 Korinthiyawa 2:10) Waɗannan ba darussa ba ne marar ma’ana irin waɗanda ’yan tauhidi da limamai suke musu a kai. Koyarwa ne masu amfani da za mu samu fahimin azanci da kuma zuciyar Ubanmu mai ƙauna. Alal misali, fansa, “asiri” ne, da alkawari dabam dabam da Jehovah ya yi amfani da su ya albarkaci mutanensa kuma ya cika ƙudurinsa—waɗannan da wasu darussa kamarsu suna da daɗi da ban albarka don bincike da kuma yin nazari.—1 Korinthiyawa 2:7.
9, 10. (a) Me ya sa fahariya take da haɗari, kuma me zai taimake mu mu guje mata? (b) Sa’ad da ya zo ga sani na Jehovah, me ya sa za mu yi ƙoƙari mu kasance da tawali’u?
9 Yayin da kake ƙara sanin zurfafan gaskiya na ruhaniya, ka kiyayi haɗari da ke zuwa da sani—fahariya. (1 Korinthiyawa 8:1) Fahariya tana da haɗari, tana ware mutum da Allah. (Misalai 16:5; Yaƙub 4:6) Ka tuna, ba mutumin da yake da dalilin yin fahariya domin iliminsa. Alal misali, ka yi la’akari da waɗannan kalmomi daga gabatarwar wani littafi da ya kimanta ci gaban kimiyya ta ’yan Adam na baya bayan nan: “Da zarar mun ƙara ilimi, haka nan za mu ƙara fahimtar cewa iliminmu bai fi cikin ludayi ba. . . . Dukan abin da muka koya kaɗan ne idan aka gwada da abin da ba mu koya ba tukuna.” Irin wannan tawali’u yana da ban wartsakewa. Idan kuma ya zo ga tarin sani mafi girma—sanin Jehovah Allah—muna da kyakkyawan dalili na kasancewa da tawali’u. Me ya sa?
10 Ka lura da wasu furci na Littafi Mai Tsarki game da Jehovah. “Tunaninka da zurfi su ke ƙwarai.” (Zabura 92:5) “Fahimin [Jehovah] marar-iyaka ne.” (Zabura 147:5) “Fahimin [Jehovah] ya wuce gaban a bi ciki.” (Ishaya 40:28) “Ya zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa!” (Romawa 11:33) Hakika, ba za mu taɓa sanin dukan abu game da Jehovah ba. (Mai-Wa’azi 3:11) Ya koya mana abubuwa da yawa na ban al’ajabi, duk da haka har yanzu da abubuwa marasa iyaka da za mu koya. Wannan begen ba abin sha’awa ba ne kuma mai sa tawali’u? Yayin da muke koyo, bari koyaushe mu yi amfani da saninmu don kusantar Jehovah kuma mu taimaka wa wasu su yi haka—ba domin mu ɗaga kanmu fiye da wasu ba.—Matta 23:12; Luka 9:48.
Ka Nuna Ƙaunarka ga Jehovah
11, 12. (a) Yaya ya kamata sani da muke samu game da Jehovah ya shafe mu? (b) Menene ke nuna ko ƙaunar mutum ga Allah tabbatacciya ce?
11 Manzo Bulus ya nuna nasaba da ke tsakanin sani da ƙauna. Ya rubuta: “Abin da ni ke addu’a ke nan, ƙaunarku ta yalwata har gaba gaba cikin sani da ganewa duka.” (Filibbiyawa 1:9) Maimakon kumburi, kowacce gaskiya mai tamani da muka koya game da Jehovah da ƙudurinsa ya kamata ta ƙara ƙaunarmu ga Ubanmu na samaniya.
12 Hakika, mutane da yawa da suke da’awar suna ƙaunar Allah da gaske ba sa ƙaunarsa. Za su iya kasancewa da motsin rai na gaske da ya cika zuciyarsu. Irin wannan yana da kyau, abin yabo ne, sa’ad da ya jitu da cikakken sani na Littafi Mai Tsarki. Amma ba daidai yake da ƙauna ta gaske ga Allah ba. Me ya sa? Ka lura da yadda Kalmar Allah ta ba da ma’anar irin wannan ƙauna: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa.” (1 Yohanna 5:3) Ƙaunar Jehovah tabbacacciya ce sa’ad da an nuna ta a ayyuka na biyayya.
13. Ta yaya tsoron Allah zai taimake mu mu nuna ƙaunarmu ga Jehovah?
13 Tsoron Allah zai taimake mu mu yi wa Jehovah biyayya. Wannan fargaba mai tsanani da daraja sosai ga Jehovah na zuwa daga samun saninsa, koyo game da tsarkakarsa marar iyaka, ɗaukaka, iko, shari’a, hikima, da kuma ƙauna. Irin wannan tsoron yana da muhimmanci ga kusantarsa. Hakika, ka lura da abin da Zabura 25:14 ta ce: “Asirin Ubangiji ga masu-tsoronsa ya ke.” Saboda haka, idan muna tsoron ɓata wa Ubanmu da muke ƙauna rai, za mu kusace shi. Tsoron Allah zai taimake mu mu yi biyayya da gargaɗi mai kyau da ke rubuce a Misalai 3:6: “A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” Menene wannan yake nufi?
14, 15. (a) Waɗanne shawarwari muke fuskanta a rayuwa ta yau da kullum? (b) Ta yaya za mu yanke shawara a hanya da ke nuna tsoron Allah?
14 Kana tsai da shawara kowacce rana, manya da ƙanana. Alal misali, wane irin taɗi za ka yi da abokan aikinka, abokan makaranta, da kuma maƙwabtanka? (Luka 6:45) Za ka yi aiki da ke gabanka da ƙwazo, ko kuma za ka nemi hanyoyi da za ka yi aikin ba tare da yinsa sosai ba? (Kolossiyawa 3:23) Za ka kusaci waɗanda ba sa ƙaunar Jehovah, ko za ka biɗi ka ƙarfafa dangantakarka da mutane masu ruhaniya? (Misalai 13:20) Menene za ka yi, har a ƙananan hanyoyi ka ɗaukaka abubuwa na Mulkin Allah? (Matta 6:33) Idan ƙa’idodin Nassi irin waɗanda aka nuna a nan suna ja-gorar shawararka kowacce rana, lallai kana tuna Jehovah “cikin dukan al’amuranka.”
15 Watau, kowacce shawara da muka yi, ya kamata wannan tunani ya yi mana ja-gora: ‘Jehovah zai so na yi haka kuwa? Wane tafarki zai fi faranta masa rai?’ (Misalai 27:11) Nuna tsoron Allah a wannan hanyar, hanya ce mafi kyau na nuna cewa muna ƙaunar Jehovah. Tsoron Allah zai motsa mu mu kasance da tsabta—a ruhaniya, a ɗabi’a, da kuma a zahiri. Ka tuna, cikin ayar da Yaƙub ya aririce Kiristoci su ‘kusaci Allah,’ ya yi musu gargaɗi: “Ku tsabce hannuwanku, ku masu zunubi; ku tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.”—Yaƙub 4:8.
16. Ta bai wa Jehovah, menene ba za mu taɓa cika ba, duk da haka me koyaushe za mu yi nasarar yi?
16 Hakika, nuna muna ƙaunar Jehovah ya ƙunshi fiye da guje wa abin da ke mugu. Ƙauna ta motsa mu kuma mu yi abin da yake daidai. Alal misali, ta yaya muke nuna godiya ga alherin Jehovah? Yaƙub ya rubuta: “Kowacce kyakkyawar baiwa da kowacce cikakkiyar kyauta daga bisa ta ke, tana sauƙowa daga wurin Uban haskoki.” (Yaƙub 1:17) Hakika, sa’ad da muka bai wa Jehovah dukiyarmu, ba ma azurta shi. Shi yake da dukiya da abubuwa da muke da su. (Zabura 50:12) Sa’ad da muka bai wa Jehovah lokacinmu da kuzari, ba biyan bukata da ba zai iya cika su muke yi ba. Ko ma idan mun ƙi wa’azin bisharar Mulkin Allah, zai iya sa duwatsu su yi magana! To, me ya sa, za mu bai wa Jehovah dukiyarmu, lokaci, da kuzari? Mafi muhimmanci, domin ta haka muke nuna muna ƙaunarsa da dukan zuciyarmu, rai, azanci, da kuma ƙarfi.—Markus 12:29, 30.
17. Menene zai motsa mu mu bai wa Jehovah da daɗin rai?
17 Sa’ad da muka bai wa Jehovah abu, ya kamata mu yi haka da farin ciki, “Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” (2 Korinthiyawa 9:7) Ƙa’ida da ke rubuce a Kubawar Shari’a 16:17 za ta taimaka mana mu bayar da daɗin rai: “Kowane mutum za ya bayar gwargwadon iyawatasa, gwargwadon albarkar Ubangiji Allahnka wadda ya ba ka.” Sa’ad da muka yi tunanin yadda Jehovah yake ba mu hannu sake, muna so mu ba shi da daɗin rai kuma hannu sake. Irin wannan bayarwa na faranta masa rai, kamar yadda ƙaramar kyauta daga yaro mai ƙauna ke faranta wa iyayensa rai. Nuna ƙaunarmu a wannan hanyar zai taimaka mana mu kusaci Jehovah.
Ka Gina Dangantaka ta Wurin Addu’a
18. Me ya sa yake da amfani mu bincika yadda za mu inganta addu’o’inmu?
18 Lokacin addu’a ta kanmu yana ba mu zarafi mai kyau—lokacin magana ta asiri da Ubanmu na samaniya. (Filibbiyawa 4:6) Tun da addu’a hanya ce mai kyau ta kusantar Allah, yana da kyau mu dakata mu bincika ingancin addu’armu. Ba dole ne addu’armu ta nuna iya magana ba, amma ya kamata ta kasance furci ne na gaskiya da ya fito daga zuciyarmu. Ta yaya za mu inganta addu’o’inmu?
19, 20. Me ya sa ya kamata mu yi bimbini kafin mu yi addu’a, waɗanne batutuwa suka dace mu yi bimbini a kan su?
19 Za mu iya gwada bimbini kafin mu yi addu’a. Idan mun yi bimbini tun kafin lokaci, za mu iya sa addu’armu ta kasance mai ma’ana kuma takamammiya, ta haka za mu guji maimaita furci da muke tunawa da sauri. (Misalai 15:28, 29) Wataƙila ta tunani a kan jigon da Yesu ya ambata a addu’arsa ta misali da kuma bincika yadda wannan yake da dangantaka da yanayinmu zai taimaka. (Matta 6:9-13) Alal misali, za mu iya tambayar kanmu game da yadda za mu saka hannu cikin yin nufin Jehovah a duniya. Za mu iya gaya wa Jehovah cewa muna son mu kasance da amfani a gare shi yadda zai yiwu kuma mu nemi taimakonsa a cika kowane aiki da ya ba mu? Mun damu game da bukatunmu na abin duniya? Don waɗanne zunubai muke bukatar gafara, su waye muke bukata mu gafarce su? Waɗanne gwaji ke damunmu, mun fahimci yadda muke bukatar kāriyar Jehovah da gaggawa game da wannan?
20 Ƙari ga haka, za mu iya tuna da mutane da muka sani da suke bukatar taimakon Jehovah musamman. (2 Korinthiyawa 1:11) Bai kamata mu manta da batun godiya ba. Idan muka yi tunani game da wannan, za mu ga dalilin yi wa Jehovah godiya kuma mu yaba masa kowacce rana don nagartarsa mai yawa. (Kubawar Shari’a 8:10; Luka 10:21) Yin haka yana da ƙarin amfani—zai taimake mu mu kasance da ra’ayi mai kyau game da rayuwa.
21. Nazarin waɗanne misalai na Nassi zai taimake mu sa’ad da muke dumfarar Jehovah cikin addu’a?
21 Nazari ma zai inganta addu’o’inmu. Akwai addu’o’i na musamman da maza da mata masu aminci suka yi da ke rubuce cikin Kalmar Allah. Alal misali, idan muna fuskantar matsala mai wuya, yana sa mu alhini kuma yana ba mu tsoro don zaman lafiyar waɗanda muke ƙauna, za mu iya karanta addu’ar da Yaƙub ya yi sa’ad da yake son ya sadu da ɗan’uwansa, Isuwa. (Farawa 32:9-12) Ko kuma mu yi nazarin addu’a da Sarki Asa ya yi sa’ad da sojojin Kushawa miliyan ɗaya suka kai wa mutanen Allah farmaki. (2 Labarbaru 14:11, 12) Idan mun damu domin matsala da take so ta ɓata sunan Jehovah, to, zai yi kyau mu bincika addu’ar Iliya a gaban masu bautar Ba’al a Dutsen Karmel, kamar addu’ar Nehemiya game da yanayin takaici na Urushalima. (1 Sarakuna 18:36, 37; Nehemiah 1:4-11) Karatu da yin bimbini a kan irin waɗannan addu’o’i zai iya ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ya ba mu fahimi game da yadda za mu dumfari Jehovah da damuwa da suka nauyaya mana.
22. Menene jigon shekara ta 2003, kuma menene za mu riƙa tambayar kanmu a kai a kai?
22 Hakika, babu ɗaukaka, babu makasudi, da suka fi a bi gargaɗin Yaƙub na cewa mu ‘kusaci Allah.’ (Yaƙub 4:8) Bari mu yi haka ta ci gaba cikin sanin Allah, ta neman mu nuna muna ƙaunarsa a kai a kai, da ta gina dangantaka da shi cikin addu’o’inmu. A duk shekarar 2003, da muke tuna da Yaƙub 4:8 jigonmu na shekara, mu ci gaba da bincika kanmu ko da gaske muna kusantar Jehovah. Furci na gaba fa? A wane azanci Jehovah zai ‘kusace ku,’ wace albarka zai kawo? Talifi na gaba zai bincika wannan batun.
Ka Tuna?
• Me ya sa kusantar Jehovah aba ce da za a ɗauka da muhimmanci?
• Waɗanne makasudi za mu iya kafawa game da samun sani na Jehovah?
• Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehovah?
• A waɗanne hanyoyi za mu gina dangantaka ta kusa da Jehovah cikin addu’a?
[Bayanin da ke shafi na 11]
Jigon shekara ta 2003 zai zama: ‘Ku kusaci Allah, shi kuwa za ya kusace ku.’—Yaƙub 4:8.
[Hoto a shafi nas 8, 9]
Sa’ad da yake girma, Sama’ila ya zo ga sanin Jehovah sosai
[Hoto a shafi na 11]
Addu’a da Iliya ya yi a Dutsen Karmel misali ne mai kyau a gare mu