Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 7/15 pp. 17-22
  • Na Yi Rashin Uba​—⁠Na Sake Samun Wani Uba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Na Yi Rashin Uba​—⁠Na Sake Samun Wani Uba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • RAYUWATA A MATSAYIN ƊAN SIKAWUT
  • FARKON HAƊUWA NA DA WANI MASHAIDIN JEHOBAH
  • YADDA WASU MATA DA KE HIDIMA A ƘASASHEN WAJE SUKA ZIYARCE NI
  • KOYO GAME DA AINIHIN UBANMU MAI TSARKI NA SAMA
  • YADDA NA SOMA YIN WA’AZI
  • SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI
  • YIN HIDIMA DABAM-DABAM
  • ZIYARA TA MUSAMMAN A ƘASAR ROMANIYA
  • TUNAWA DA BAYA DA ƊOKIN NAN GABA
  • Jehobah Bai Taba Yasar da Ni Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Na Ji Dadin Koya da Kuma Koyar da Wasu Game da Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Jehobah Ya Koyar da Ni In Yi Nufinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 7/15 pp. 17-22

Tarihi

Na Yi Rashin Uba Na Sake Samun Wani Uba

Gerrit Lösch ne ya ba da labarin

AN HAIFI mahaifina a shekara ta 1899, a birnin Graz, a ƙasar Austriya. Shi matashi ne a lokacin da aka yi Yaƙin Duniya na Ɗaya a shekara ta 1939. An tilasta masa ya shiga rukunin sojojin Jamus jim kaɗan bayan da Yaƙin Duniya na Biyu ya ɓarke. An kashe mahaifina a lokacin da suke yaƙi a ƙasar Rasha a shekara ta 1943. Abin baƙin ciki shi ne, ina ɗan shekara biyu ne kawai sa’ad da mahaifina ya rasu kuma don haka, ban san shi ba. A lokacin da nake makaranta, ina baƙin ciki sosai sa’ad da na tuna cewa wasu abokan makarantana suna da ubanni kuma ni ba ni da shi. A lokacin da nake matashi, ina samun ƙarfafa sa’ad da na karanta cewa Ubanmu na sama ba ya mutuwa.—Hab. 1:12.

RAYUWATA A MATSAYIN ƊAN SIKAWUT

A lokacin da nake ɗan shekara bakwai, na shiga ƙungiyar ’yan Sikawut. Wani laftanan mai suna Robert Stephenson Smyth Baden-Powell ne ya kafa ƙungiyar a shekara ta 1908, a ƙasar Biritaniya. Kuma an san da zaman wannan ƙungiyar faɗin duniya. A shekara ta 1916, ya sake kafa wata Ƙungiyar Sikawut na Yara iri na.

Ina jin daɗi duk lokacin da muka fita yawo muna yaɗa zango, mu kwana a tantoci kuma mu yi maci sanye da kaki muna kaɗa ganga. Na ji daɗin yin tarayya da sauran ’yan Sikawut. Domin muna yin waƙoƙi a inda muka je kuma da yamma mu yi wasanni a daji. Ƙari ga haka, mun koyi abubuwa game da halitta, kuma hakan ya sa na ƙara ƙaunar abubuwan da Mahalicci ya yi.

Ana ƙarfafa ’yan Sikawut su riƙa yin alheri kowace rana. Wannan shi ne takenmu. Muna gaida juna cewa, “A Shirye Kullum,” kuma hakan ya burge ni sosai. Mu yara fiye da dari ne a ƙungiyarmu. Rabi ’yan Katolika, rabi kuma ’yan Farostatan, sa’an nan ɗaya kuma ɗan addinin Buddha.

Akan yin taron ƙasa da ƙasa na ’yan Sikawut bayan shekaru kaɗan kuma an soma hakan tun daga shekara ta 1920. Na halarci taron ’yan Sikawut na Ƙasa da Ƙasa na bakwai a birnin Bad Ischl, a ƙasar Austriya a watan Agusta na shekara ta 1951. Bayan haka, na halarci taro na tara a Tashar Sutton, kusa da birnin Birmingham, a ƙasar Ingila a watan Agusta na 1957. ’Yan Sikawut 33,000 daga ƙasashe 85 ne suka halarci wannan taron. Ƙari ga haka, wajen mutane 750,000 ne suka ziyarce mu haɗe da Sarauniya Elizabeth na ƙasar Ingila. Hakan ya sa na ji kamar ’yan Sikawut ’yan’uwan juna ne a faɗin duniya. Ban taɓa sanin cewa zan sami mutane da suke ƙaunar juna sosai fiye da haka ba, wato ’yan’uwa a ƙungiyar Jehobah.

FARKON HAƊUWA NA DA WANI MASHAIDIN JEHOBAH

A wajen watan Maris ko Afrilu na shekara ta 1958, na kusan gama koyon aikin sayar da abinci a Hotel mai suna Wiesler a birnin Graz, a ƙasar Austriya. A wurin ne na sami wani ɗan’uwa mai suna Rudolf Tschiggerl, abokin aikina da ya yi mini wa’azi. Wannan ne lokaci na farko da na ji koyarwar gaskiya game da Littafi Mai Tsarki. Ya gaya mini cewa koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya bai jitu da Littafi Mai Tsarki ba. Na ƙaryata shi kuma na gaya masa cewa koyarwar yana cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma da yake ina ƙaunar sa, na yi ƙoƙarin rinjayarsa ya shiga Cocin Katolika.

Ɗan’uwa Rudolf, wanda muke kiransa Rudi, ya ba ni Littafi Mai Tsarki. Na nace ya ba ni juyin Littafi Mai Tsarki na ’yan Katolika, sai ya ba ni kuma ya saka wata warƙa da Shaidun Jehobah suka wallafa a ciki. Ban so warƙar ba don na ga kamar da yaudara a ciki. Duk da haka, na yarda mu tattauna Littafi Mai Tsarki tare. Da yake Ɗan’uwa Rudi mai hikima ne, bai sake ba ni wasu littattafai ko mujallu da Shaidun Jehobah suka wallafa ba. Mun yi kusan wata uku muna tattauna Littafi Mai Tsarki da shi jifa-jifa kuma muna yin hakan har tsakar dare.

Bayan da na gama koyan sayar da abinci a hotal da ke birnin Graz, mahaifiyata ta kai ni makarantar gudanar da harkokin hotal. Makarantar tana kusa da tsaunuka a kudancin Turai da ake kira Alps, a garin Bad Hofgastein. Makarantar tana da alaƙa da Grand Hotel da ke Bad Hofgastein don haka, a wasu lokatai akan tura ni wurin don in kara koyo.

YADDA WASU MATA DA KE HIDIMA A ƘASASHEN WAJE SUKA ZIYARCE NI

Bayan haka, sai Rudi ya tura adireshina zuwa ofishin reshen da ke birnin Vienna. Ofishin kuma ya tura wasu ’yan’uwa mata biyu masu wa’azi a ƙasashen waje, wato Ilse Unterdörfer da Elfriede Löhr su ziyarce ni.a Wata rana sai wani da yake aiki a hotal ɗin ya kira ni ya ce akwai wasu mata a waje cikin mota da suke so su gan ni. Na yi mamaki sosai don ba taɓa saninsu ba. Duk da haka, sai na je don in ga ko zan waye su. Daga baya, na fahimci cewa sun taɓa rarraba littattafai a lokacin da Nazi suke mulki a ƙasar Jamus sa’ad da aka saka wa wa’azinmu takunkumi kafin Yaƙin Duniya na Biyu. Kafin a soma Yaƙin, ’yan sandan ciki sun kama su kuma suka kai su sansanin da ke lardin Lichtenburg. Bayan yaƙin, sai aka ƙaurar da su zuwa sansanin da ke Ravensbrück, kusa da birnin Berlin.

Na yi wa matan ladabi sosai don su sa’o’in mahaifiyata ne. Shi ya sa na tsai da shawara cewa ba zan ɓata lokaci wajen tattaunawa da su ba kuma bayan wasu makonni ko watanni in ce musu ba na son nazarin. Na ce su zo mini da nassosin da suka yi magana game da koyarwar cocin katolika da ke cewa papa roma shi ne ya gāji manzo Bitrus. Na gaya musu cewa zan nuna wa limamin cocinmu don mu tattauna su. Na ɗauka cewa yin hakan zai sa in gane koyarwar gaskiya.

KOYO GAME DA AINIHIN UBANMU MAI TSARKI NA SAMA

Cocin Katolika sun bayyana cewa Bitrus shi ne papa roma na fari, kuma waɗanda suka zama papa roma daga baya sun gaji Bitrus ne. (Wannan koyarwar bisa ga yadda suka fahimci abin da Yesu ya faɗa a Matta 16:18, 19 ne. Wannan fahimtar ba daidai ba ne.) Cocin Katolika sun gaskata cewa papa roma ba ya kuskure sa’ad da yake bayyana koyarwar Kirista kuma duk abin da ya faɗa daidai ne. ’Yan Katolika da yawa sun gaskata da hakan. Ni ma na gaskata da hakan kuma na ɗauka cewa tun da yake papa roma ne ya koyar da Allah-uku-cikin-ɗaya, to koyarwar gaskiya ce. Amma na ce idan har papa roma yana kuskure, to wannan koyarwar ƙarya ce.

Sa’ad da na ziyarci limamin, na yi masa tambayoyi amma ya kasa ba ni amsa. Maimakon haka, sai ya ba ni wani littafi game da koyarwar Katolika a kan wannan batun. Na tafi gida da littafin kuma na karanta shi. Na sake dawowa da ƙarin tambayoyi. Limamin ya kasa ba ni amsoshin kuma ya ce: “Ba zan iya gamsar da kai ba. . . . Ina yi maka fatan alheri!” Bai ƙara tattaunawa da ni game da batun ba.

Bayan haka, na shirya don Ilse da Elfriede su soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Sun koya mini abubuwa da yawa game da Ubanmu na sama Mai Tsarki, Jehobah. (Yoh. 17:11) A lokacin babu wata ikilisiya a wurin, shi ya sa waɗannan mata biyun suke yin taro a gidan wani mutum da ake nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Mutane kaɗan ne kawai suke halartan taron. Mata biyun ne suke gudanar da abubuwan da ake tattaunawa a taron da yake babu wani ɗan’uwa da ya yi baftisma da zai yi ja-gora. A wasu lokatai, wani ɗan’uwa yakan zo daga wani wuri don ya yi jawabi ga jama’a a wani daƙin haya.

YADDA NA SOMA YIN WA’AZI

Ilse da Elfriede sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni a watan Oktoba, 1958, kuma bayan wata uku da yin nazari, sai na yi baftisma a watan Janairu na shekara ta 1959. Kafin in yi baftisma na tambaye su ko zan iya bin su zuwa wa’azi don in ga yadda ake yi. (A. M. 20:20) Bayan na bi su sau ɗaya, sai na gaya musu su ba ni wani yankin da zan riƙa yin wa’azi. Sun ba ni wani ƙauye da nake zuwa ni kaɗai in yi wa’azi gida-gida kuma ina komawa don in ziyarci waɗanda suke son koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ɗan’uwa na farko da muka fita wa’azi tare mai kula da da’ira ne wanda daga baya ya ziyarce mu.

Da na sauke karatu a makarantar koyan gudanar da ayyukan hotal a shekara ta 1960, sai na koma gida don in taimaka wa dangina su koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Har yanzu, babu wani cikin dangina da ya zama Mashaidin Jehobah, amma wasu a cikinsu sun fara son gaskiya.

SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI

A shekara ta 1961, an karanta wa ikilisiyoyi wasiƙu daga ofishin reshe don ƙarfafa ’yan’uwa su soma hidimar majagaba. Na san cewa ba ni da hujjar ƙin yin hidimar majagaba da yake ban yi aure ba kuma ina da kuzari. Na yi tunanin cewa ina bukatar mota da za ta taimaka mini a hidimar majagaba, sai na tambayi mai kula da da’irarmu ɗan’uwa Kurt Kuhn, ko zan iya yin aiki na ’yan watanni don in sayi motar. Amsar da ya ba ni ita ce, “Yesu da manzanninsa sun yi amfani da mota ne a hidimar da suka yi?” Tambayar da ya yi mini ya sa na fahimci abin da nake bukata na yi! Sai na tsai da shawarar soma hidimar majagaba nan da nan. Da farko na bukaci yin canji da yake ina aikin sa’o’i 72 a mako.

Na roƙi shugaban aikina ya ba ni damar yin aikin sa’o’i 60 a mako. Ya amince da hakan kuma bai rage kuɗin da yake biya na a wata ba. Bayan haka, sai na sake roƙansa na yi aikin sa’o’i 48 a mako. Ya sake amincewa da hakan kuma bai rage kuɗin da yake biya na a wata ba. Har ila na roƙe shi kuma cewa ina son in riƙa yin aikin sa’o’i 36 a mako kuma ya sake amincewa da hakan. Abin mamaki, bai rage kuɗin da yake biya na ba. Wataƙila ya yi hakan ne don ba ya son in daina aiki da shi. Ta haka ne na soma hidimar majagaba. A lokacin, majagaba suna ba da sa’o’i 100 a wata.

Bayan wata huɗu, aka naɗa ni majagaba na musamman da kuma bawan ikilisiya a wata ƙaramar ikilisiya a lardin Carinthia, a garin Spittal an der Drau. A lokacin, majagaba na musamman suna ba da sa’o’i 150 a wata. Ba ni da abokin hidima, duk da haka, wata ’yar’uwa mai suna Gertrude Lobner ta taimaka mini. Ƙari ga haka, wannan ’yar’uwar ita ce mai taimako na a ikilisiya.b

YIN HIDIMA DABAM-DABAM

A shekara ta 1963 ne aka tura ni hidimar mai kula mai ziyara. Sau da yawa nakan shiga jirgin ƙasa da manyan jakunkuna don in ziyarci ikilisiyoyi. Da yake yawancin ’yan’uwa a wurin ba su da mota, ba wanda yake zuwa tashan jirgin ƙasa don ya taya ni ɗaukan jakunkunan sa’ad da na sauka. Nakan taka da kafa zuwa masaukina maimakon shigan tasi don ba na son ’yan’uwan su ji wani iri.

A shekara ta 1965, aka gayyace ni aji na 41 na Makarantar Gilead kuma a lokacin ban yi aure ba tukun. ’Yan ajinmu da yawa ba su yi aure ba. Bayan da na sauke karatu, sai aka ce in koma ƙasar Austriya don in ci gaba da hidimar mai kula da da’ira kuma hakan ya ba ni mamaki sosai. Amma kafin in bar ƙasar Amirka, an gaya mini in raka wani mai kula mai ziyara don mu ziyarci wasu ikilisiyoyi na tsawon wata ɗaya. Na ji daɗin hidimar da na yi da Ɗan’uwa Anthony Conte, yana son yin wa’azi kuma ya ƙware a yin hakan. Mun yi hidima a arewacin Amirka a wani ƙauye da ake kira Cornwall.

A lokacin da na dawo ƙasar Austriya, sai na haɗu da wata ’yar’uwa kyakkyawa marar aure mai suna Tove Merete. Iyayenta sun koya mata Littafi Mai Tsarki tun tana ’yar shekara biyar. Sa’ad da aka tambaye mu yadda muka haɗu, muna yawan cewa, “Ofishin reshe ne ya haɗa mu.” Mun yi aure shekara ɗaya bayan haka, wato a watan Afrilu na shekara ta 1967, kuma an ce in ci gaba da hidimata.

A shekara ta 1968, na gano cewa Jehobah ya yi mini alheri kuma ya shafe ni in zama ɗa a gare shi. Ta hakan ne na soma wata dangantaka ta musamman da Ubana na sama, tare da dukan waɗanda suke ‘kira, Abba, Uba,’ kamar yadda littafin Romawa 8:15 ta nuna.

Ni da matata Merete mun ci gaba da yin hidimar masu kula masu ziyara har zuwa shekara ta 1976. A wasu lokatan ɗari, mukan kwana a ɗakuna masu sanyi sosai. Akwai wata rana da muka tashi daga barci sai muka tarar cewa ɓangaren bargon da muka rufe a fuskarmu ya daskare don tsabar sanyi! Sai muka soma tafiya da abin ɗumama ɗaki mai amfani da lantarki. A wasu wurare, duk sa’ad da muke so mu je bayan gida daddare, sai mun bi da hanya mai cike da dusar ƙanƙara. Ba mu da ɗakin kanmu, saboda haka, muna yawan zama a ɗakin da muka sauka har ranar Litinin. A ranar Talata, sai mu tafi wata ikilisiya.

Ina farin cikin faɗin cewa a duk waɗannan shekarun, matana ta ba ni goyon baya sosai. Tana son yin wa’azi, kuma ban taɓa ƙarfafa ta kafin ta fita yin wa’azi ba. Tana kuma ƙaunar mutane. Hakan ya kasance da ban taimako sosai.

A shekara ta 1976, an gayyace mu yin hidima a ofishin reshe da ke birnin Vienna a ƙasar Austriya, kuma an naɗa ni a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ofishin Reshe. A lokacin, ofishin reshen Austriya yana kula da aikin da ake yi a ƙasashen Turai da ke Gabas kuma yana tsara yadda za a shigar da littattafai cikin ƙasashen a asirce. Ɗan’uwa Jürgen Rundel ya yi ja-gora a wannan aikin. Daga baya, aka ce na yi ja-gora a aikin fassara littattafai a cikin harsuna guda goma a ƙasashen Turai da ke Gabas. Har yau, Ɗan’uwa Jürgen da matarsa, Gertrude, suna hidimar majagaba ta masamman a ƙasar Jamus. Daga shekara ta 1978, ofishin reshe da ke Austriya ya soma buga mujallu a cikin harsuna shida. Kuma ofishin ya aika wa mutane a wasu ƙasashe mujallun. Ɗan’uwa Otto Kuglitsch, wanda shi da matarsa, Ingrid suke hidima a ofishin reshe da ke Jamus ne yake kula da maɗaba’ar.

’Yan’uwan da ke ƙasashen Turai da ke Gabas ma sun buga mujallu a ƙasashensu. Sun yi hakan ta wajen yin amfani da na’urar ɗaukan hoton littattafai ko kuma yin amfani da fim. Amma suna bukatar tallafi daga wajen ’yan’uwa a wasu ƙasashe. Jehobah ya kula da ayyukansu. A ofishin reshen, mun so waɗannan ’yan’uwan da suka jimre wa tsanantawa cikin shekaru da yawa.

ZIYARA TA MUSAMMAN A ƘASAR ROMANIYA

A shekara ta 1989, na sami gatan zuwa ƙasar Romaniya tare da Ɗan’uwa Theodore Jaracz, memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Sun je wannan ƙasar domin su taimaka wa wasu ’yan’uwan su dawo cikin ƙungiyar Jehobah. Daga shekara ta 1949, waɗannan ’yan’uwan sun fita daga ƙungiyar Jehobah kuma suka kafa nasu ikilisiyoyi. Duk da haka, sun ci gaba da yin wa’azi da kuma yi wa sababbi baftisma. An ma kai su kurkuku don sun ƙi shigan soja, kamar yadda ’yan’uwanmu da suke ƙungiyar Jehobah suka yi. A lokacin, an saka wa aikinmu a ƙasar Romaniya takunkumi, saboda haka, mun haɗu da ’yan’uwan a asirce. Mun haɗu a gidan Ɗan’uwa Pamfil Albu, da wasu dattawa huɗu da suka manyanta da kuma wakilan Kwamiti na Ƙasar Romaniya. Wani ɗan’uwa kuma mai suna Rolf Kellner, wanda zai fassara tattaunawar ya zo daga ƙasar Austriya.

A dare na biyu da suka tattauna, Ɗan’uwa Albu ya lallashe dattawa huɗun su goyi bayansu. Ya ce: “Idan ba mu yi hakan yanzu ba, wataƙila ba za mu sake samun wannan zarafin ba.” Bayan wannan tattaunawar, kusan ’yan’uwa dubu biyar sun dawo ƙungiyar Jehobah. Babu shakka, hakan ya sa Jehobah farin ciki kuma ya kunyatar da Shaiɗan!

Kusan ƙarshen shekara ta 1989, kafin mulkin kama karya na ƙasashen da ke Turai na Gabas su lauye, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ce ni da matata mu ƙaura zuwa hedkwatarmu da ke birnin New York, a Amirka. Hakan abin mamaki ne sosai a gare mu. Mun soma hidima Bethel da ke Brooklyn a watan Yuli na 1990. A shekara ta 1992, an naɗa ni a matsayin mataimakin Sashen Hidima na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Kuma tun watan Yuli na shekara ta 1994, na sami gatan yin hidima a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.

TUNAWA DA BAYA DA ƊOKIN NAN GABA

A yau, ba na aikin sayar da abinci. Amma, ina jin daɗin yin aiki tare da wasu ’yan’uwa don shirya abubuwa da ke kamar abinci da za su ƙarfafa dangantakar ’yan’uwanmu a faɗin duniya. (Mat. 24:45-47) Idan na tuna fiye da shekara 50 da na yi a hidima ta cikakken lokaci, ina matuƙar farin ciki. Ina farin ciki domin yadda Jehobah yake yi wa ’yan’uwanmu a faɗin duniya albarka. Ina son halartar taron ƙasashe inda muke koyo game da Ubanmu da ke sama, wato Jehobah da kuma gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Ina fata cewa ƙarin miliyoyin mutane za su soma nazarin Littafi Mai Tsarki don su koyi gaskiya kuma su soma bauta masa tare sauran ’yan’uwanmu Kiristoci a faɗin duniya. (1 Bit. 2:17) Ina ɗokin ganin yadda za a ta da matattu a duniya kuma wataƙila zan ga mahaifina daga sama. Ina fata cewa shi da mahaifiyata da kuma sauran dangina za su so bauta wa Jehobah a Aljanna.

Ina ɗokin ganin yadda za a ta da matattu a duniya kuma wataƙila zan ga mahaifina daga sama

a Ka duba labarinsu a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1979.

b Amma yanzu ba ma amfani da sunan nan bawan ikilisiya da kuma mai taimaka masa, maimakon haka, muna amfani da mai tsara ayyukan rukunin dattawa da sakatare.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba