KA TUNA?
Ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
Yaya Kiristoci za su ɗauki halin cewa aya da suka soma buɗewa a cikin Littafi Mai Tsarki za ta taimake su?
Kiristoci na gaskiya ba sa yin camfi. Maimakon haka, suna nazarin Littafi Mai Tsarki don su samu cikakken sani da kuma ja-gorar Allah.—12/15, shafi na 3.
Wace “duniya” ce za ta wuce?
Wannan “duniya” da za ta wuce tana nufin mutanen da ba sa rayuwar da ta jitu da nufin Allah. (1 Yoh. 2:17) Duniya da kuma mutane masu aminci za su tsira.—1/1, shafuffuka na 5-7.
Ko da yake Habila ya mutu, ta yaya yake mana jawabi har yanzu? (Ibran. 11:4)
Yana hakan ta wurin bangaskiyarsa. Za mu iya koya daga wurinsa kuma mu nemi mu yi koyi da bangaskiyarsa. Misalinsa yana mana jawabi a yau.—1/1, shafi na 12.
Waɗanne abubuwa ne bai kamata mu ƙyale su nisanta mu daga Allah ba?
Wasu su ne: Aiki da nishaɗi da yin cuɗanya da wani danginmu da aka yi wa yankan zumunci da yadda muke amfani da fasaha na zamani da damuwa game da lafiyar jikinmu da kasancewa da ra’ayin da bai dace ba game da kuɗi da kuma cika ɗaukan ra’ayinmu ko kuma matsayinmu da muhimmanci.—1/15, shafuffuka na 12-21.
Wane darasi ne muka koya daga yadda Musa ya kasance da tawali’u?
Musa bai yi fahariya ba sa’ad da ya samu matsayi, maimakon hakan ya dogara ga Allah ba ga kansa ba. Bai kamata mu bar iko ko matsayi ko iyawa da muke da shi ya sa mu fahariya ba, maimakon hakan, ya kamata mu dogara ga Jehobah. (Mis. 3:5, 6)—3/1, shafi na 5.
Mene ne yake nufi cewa Isra’ilawa “marasa-kaciya ne a zuci”? (Irm. 9:26)
Sun yi tawaye kuma sun ƙi su tuba, suna bukatar su kawar da abin da ya sa su rashin biyayya, kamar tunaninsu da sha’awoyi ko kuma muradinsu da ba su jitu ba da na Allah. (Irm. 5:23, 24)—3/15, shafuffuka na 9-10.
Ta yaya Yesu ya kafa misali wajen yin rayuwa mai ma’ana?
Burin Yesu a rayuwa shi ne yin nufin Allah. Ya ƙaunaci Ubansa sosai kuma ya ƙaunaci mutane. Saboda haka, Yesu ya san cewa Ubansa ya amince da shi kuma yana ƙaunarsa. Waɗannan abubuwa ne suke sa rayuwa ta kasance da ma’ana.—5/1, shafuffuka na 4-5.
Mene ne sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya ya ƙunsa?
Ya ƙunshi Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da kwamitin da ke kula da reshe da masu kula masu ziyara da rukunin dattawa da ikilisiyoyi da kuma kowane mai shela.—4/15, shafi na 29.
Shin Isra’ilawa suna kashe masu laifi ta wajen rataye su a kan gungume?
A’a. Al’ummai da yawa a zamanin dā sun yi hakan amma ban da Isra’ilawa. A lokacin da ake rubuta Nassosin Ibrananci, Isra’ilawa suna kashe masu laifi ta wajen jifarsu da duwatsu. (Lev. 20:2, 27) Sa’an nan su rataye jikinsa a kan gungume don a gargaɗar da mutane.—5/15, shafi na 13.