Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 12/15 p. 3
  • Ka Yi Hattara, Littafi Mai Tsarki Ba Camfi Ba Ne

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Hattara, Littafi Mai Tsarki Ba Camfi Ba Ne
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Tuna?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Sihiri da Maita Ba Su da Kyau
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
  • Kalmar Allah Tana da Iko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • An Sake Gano Begen Rai Na Har Abada A Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 12/15 p. 3

Ka Yi Hattara, Littafi Mai Tsarki Ba Camfi Ba Ne

“MAGANAR Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.” (Ibran. 4:12) Waɗannan kalmomin da manzo Bulus ya furta sun nuna cewa Littafi Mai Tsarki yana da iko ya rinjayi mutane kuma ya sa su canja salon rayuwarsu.

Bayan manzannin Yesu sun rasu, ’yan ridda suka taso kuma suka sa mutane su samu ra’ayi marar kyau game da ikon Littafi Mai Tsarki. (2 Bit. 2:1-3) Da sannu-sannu, limamai suka soma koyar cewa Littafi Mai Tsarki kayan dabo ne. Wani shehun malami mai suna Harry Y. Gamble ya rubuta wani littafi game da yin amfani da Littafi Mai Tsarki a matsayin camfi. Ya ce a ƙarni na uku, wani limami mai suna Origen ya ce jin kalmomin Littafi Mai Tsarki ma kaɗai yana iya taimaka wa mutum. Origen ya ce kalmomin ’yan sihiri suna da iko, amma kalmomin da Allah ya hure sun fi na ’yan sihiri iko sosai. John Chrysostom wanda ya wanzu a ƙarni na huɗu ya ce: “Iblis ba zai ma kuskura ya zo kusa da gidan da aka ajiye Littafi Mai Tsarki ba.” Ya kuma ce wasu mutane suna rataye wasu ayoyi na Littafi Mai Tsarki a wuyansu kamar laya. Wannan shehun malamin ya kuma ambata abin da wani ɗan tauhidi na cocin Katolika, mai suna Augustine ya ce: “Idan mutum yana da ciwon kai, zai iya buɗe littafin Yohanna kuma ya saka shi ƙarƙashin matashin kansa kafin ya kwanta.” Waɗannan koyarwar sun sa mutane suka soma yin amfani da Littafi Mai Tsarki a matsayin camfi. Kai kuma fa? Shin Littafi Mai Tsarki laya ce ko yana sa mutum ya taki sa’a ko kuwa yana kāre mutum?

Mutane suna kuma yin amfani da Littafi Mai Tsarki a hanyar da ba ta dace ba. Sun amince cewa idan sun buɗe Littafi Mai Tsarki, ayar da ta soma buɗuwa ce za ta taimake su. Alal misali, Shehun malamin ya ce, akwai wani lokaci da Augustine ya ji wani yaron maƙwabcinsa yana cewa: “Ɗauka ka karanta, ɗauka ka karanta.” Sai Augustine ya yi zato cewa Allah ne yake gaya masa ya buɗe kowace aya ta Littafi Mai Tsarki ya karanta.

Ka taɓa ganin mutanen da suke yin amfani da Littafi Mai Tsarki a wannan hanyar don magance matsalolinsu? Ko da yake yin amfani da Littafi Mai Tsarki don magance matsalolinsu ba laifi ba ne. Amma, yin amfani da Littafi Mai Tsarki a wannan hanyar ba ta dace ba.

Yesu ya yi wa almajiransa alkawari cewa zai aiko musu da ruhu mai tsarki. Ya ce: ‘Zai koya muku abubuwa duka, ya tuna muku kuma dukan abin da na faɗa muku.’ (Yoh. 14:26) Wannan ayar ta nuna cewa abin da muka karanta ne zai taimaka mana, ba buɗe wata aya ta Littafi Mai Tsarki ba.

Mutane da yawa suna sa rai cewa Littafi Mai Tsarki camfi ne da zai kāre su da magance matsalolinsu ko kuma ya sa su san abin da zai faru musu a nan gaba. Amma, Littafi Mai Tsarki ya haramta sihiri. (Lev. 19:26; K. Sha 18:9-12; A. M. 19:19) Gaskiya ce cewa Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana, amma ya kamata mu yi amfani da shi yadda ya dace. Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana idan muka yi nazarinsa. Samun cikakken sani na Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa mutane da yawa su san bambanci tsakanin nagarta da mugunta. Ya kuma taimaka musu su yi watsi da mugun hali, su ji daɗin iyalinsu kuma su zama abokan Allah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba