Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/15 p. 13
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ka Tuna?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/15 p. 13

AMSOSHIN TAMBAYOYIN MASU KARATU

Shin a zamanin dā, Isra’ilawa suna kashe masu laifi ta wajen rataye su a kan gungume?

Al’ummai da yawa a zamanin dā suna kashe ɓarayi ta wajen rataye su a kan gungume. Romawa kuma sukan ɗaura ko kuma su kafa wa mutumin ƙusa, sai su bar shi a wurin kwanaki da yawa domin ya sha azaba da ƙishirwa da yunwa da zafin rana da ruwan sama da iska da kuma sanyi. Romawa suna ɗaukan rataye mutum a kan gungume a matsayin wulakancin da ake yi wa ɓarayi.

Al’ummar Isra’ila kuma fa? Shin suna kashe ɓarayi ta wajen rataye su a kan gungume ne? Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta ce: “Idan kuma mutum ya yi zunubi wanda ya isa mutuwa, har kuwa an kashe shi, ka kuwa rataye shi ga itace; gangar jikinsa ba za ya kwana a itacen ba, amma lallai za ka bizne shi a ran nan.” (K. Sha 21:22, 23) Hakika, a lokacin da aka rubuta Nassosin Ibrananci, ana kashe mutum da ya cancanci mutuwa kafin a rataye shi a kan gungume ko kuma itace.

Littafin Levitikus 20:2 ya ce: “Kowanene shi da ke daga cikin ’ya’yan Isra’ila, ko kuwa na cikin baƙin da ke sauke cikin Isra’ila, wanda ke bada zuriyarsa ga Molech: hakika za a kashe shi: mutanen ƙasa za su jejjefe shi da duwatsu.” Ana kashe duk waɗanda suke da “mabiya ko maita” ta wajen jifarsu da duwatsu.—Lev. 20:27, Littafi Mai Tsarki.

Littafin Kubawar Shari’a 22:23, 24 ya ce: “Idan da yarinya wadda ta ke budurwa, an kuwa ɗaura wa wani mutum aure da ita, wani mutum kuma ya iske ta cikin gari, ya kwana da ita; sai ku fito da su duka biyu zuwa ƙofar garin nan, ku jejjefe su da duwatsu har su mutu; ita yarinyan, domin tana cikin gari, ba ta kuwa yi ihu ba; mutumin, domin ya ƙasƙantadda matar ɗan’uwansa: haka nan za ka kawar da mugunta daga cikinka.” A al’ummar Isra’ila, jifar mutum da duwatsu shi ne ainihin hanyar da ake kashe waɗanda suka yi laifi mai tsanani.a

Hakika, ana kashe mutumin da ya cancanci mutuwa kafin a rataye shi a kan gungume ko kuma itace

Kubawar Shari’a 21:23 ya ce: “Wanda an rataye shi la’antace ne ga Allah.” Hakika rataye gawan wanda yake “la’antace ne ga Allah” a kan itace zai zama kashedi ga Isra’ilawa.

a Masana da yawa sun gaskata cewa a ƙarƙashin doka, ana kashe mutumin da ya yi laifi kafin a rataye jikinsa a kan gungume. Amma a ƙarni na farko, da akwai tabbaci cewa Yahudawa sun rataye waɗanda suka yi laifi da ransu, sai su mutu a kan gungumen.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba