Masu Ƙananan Jiki, Masu Kirki
YAYA zai zama ka yi wa baƙi magana game da Mulkin Allah idan tsawonka santimita 76 ne kawai? Laura za ta iya gaya maka. A shekararta na 33, tsawonta santimita 76 ne kawai. Ita da ’yar’uwarta, María, wadda shekararta 24 kuma tsawonta santimita 86 suna da zama a Quito, Ecuador. Bari su yi bayanin tangarɗa da suke fuskanta a hidimarsu ta Kirista.
“Zuwa inda muke wa’azi da kuma taronmu na Kirista, muna takawa kamar rabin kilomita mu shiga bos. Daga inda ake saukar da mu, za mu sake takawa kamar rabin wata kilomita mu sake shiga wani bos. A wannan hanyar da akwai mafaɗatan karnuka guda biyar. Karnuka suna tsorata mu sosai domin muna ganinsu manya-manya kamar dawakai. Domin mu kore su idan bukata ta kama, muna ɗaukan sanda, mu ɓoye a wani waje kafin mu shiga bos saboda mu riƙe idan muna komawa gida.
“Don mu shiga bos ɗin sai mun ɗaga ƙafa sosai. Domin mu sami sauƙin shiga bos ɗin sai mu hau juji da ya yi tudu a tashar bos ɗin. Wasu direbobi suna kaiwa wajen jujin, amma wasu ba sa zuwa. Saboda haka, doguwa a tsakaninmu sai ta taimake gajeriyar ta shiga. Shiga bos na biyu yana bukatar mu tsallake wata babbar hanya mai hayaniya—aiki ne ƙwarai da gajejjerun ƙafafunmu. Domin ƙananan jiki da muke da shi, jakar littattafai mai nauyi tana ƙara mana wahala. Don mu rage nauyin jakar, muna amfani da ƙaramin Littafi Mai-Tsarki kuma mun rage yawan littattafai da muke ɗauka.
“Tun muna ƙanana, mun damu da yadda muke ƙwarai. Maƙwabta sun san cewa muna tsoron magana da baƙi. Saboda haka suna mamaki da farin cikin ganin muna ƙwanƙwasa musu ƙofa, kuma koyaushe suna ranta mana kunnuwansu. Amma a inda ba a san mu sosai ba, mutane sau da yawa suna yi mana kallon wada; saboda haka, ba koyaushe ba ne suke ba mu hankalinsu sosai kamar yadda ya cancanci hidimarmu. Duk da haka, ganin ƙaunar Jehovah tana ƙarfafa mu mu ci gaba a aikin wa’azi. Yin tunani a kan Misalai 3:5, 6 ma ya ba mu ƙarfi.”
Kamar yadda Laura da María suka nuna jimiri duk da tangarɗa da suke fuskanta zai ɗaukaka Allah. Manzo Bulus ya yi addu’a a cire masa ‘ƙaya da ke jikinsa,’ wataƙila wani ciwo ne na zahiri. Amma Allah ya gaya masa: “Alheri na ya ishe ka: gama cikin kumamanci ikona ya ke cika.” Hakika, ba sai an cire mana naƙasa ba kafin mu bauta wa Allah. Cikakken tawakkali ga Allah za ta taimake mu mu yi amfani da yanayinmu da kyau. Domin Bulus ya ɗauki ‘ƙaya da ke jikinsa’ haka, ya iya cewa: “Sa’anda ina rashin ƙarfi, sa’annan mai-ƙarfi ni ke.” (2 Korinthiyawa 12:7, 9, 10) Bayan wasu shekaru Bulus ya rubuta: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.”—Filibbiyawa 4:13.
A zamanin yau, Allah yana cim ma manyan ayyuka ta hannun maza, mata da yara waɗanda suke ba da kai gareshi. Wasu cikinsu naƙasassu ne a wasu hanyoyi. Ko da yake dukansu suna sa rai za su warke a ƙarƙashin Mulkin Allah, ba sa jira har sai lokacin da Allah ya sauƙaƙa masu wahalarsu kafin su yi wani abu a hidimarsa.
Ka na wahala daga wani raunana ne? Kada ka fid da rai! Ta bangaskiyarka za ka zama tsakanin waɗannan Bulus, Laura, da kuma María. Game da su za a iya cewa, kamar yadda yake ga maza da mata masu bangaskiya a lokuttan dā: “Daga cikin rashin ƙarfi aka ƙarfafa su.”—Ibraniyawa 11:34.
[Hoto a shafi na 30]
María
Laura
[Hoto a shafi na 31]
María tana taimaka wa Laura ta shiga bos
[Hotuna a shafi na 31]
“Karnuka suna tsorata mu sosai domin muna ganinsu manya-manya kamar dawakai”
A ƙasa: Laura da María da waɗanda su suke nazarin Littafi Mai-Tsarki da su