Ƙarfafa Daga “Bakin Jarirai”
A watan Disamba na 2009, Kotun Ƙoli na ƙasar Rasha ya yanke hukunci a kan Shaidun Jehobah da ke birnin Taganrog. A sakamako, aka ƙwace wurin taronmu kuma aka ce littattafan da muke bugawa guda talatin da huɗu ba su dace ba. An saka wannan labarin da kuma hotunan ’yan’uwan da hakan ya shafa, har da ƙananan yara a cikin Yanar gizonmu.
Ba da daɗewa ba bayan haka, ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasar Rasha, ya karɓi wani saƙo daga wata iyali da ke birnin Queensland a ƙasar Ostareliya. Iyalin ta karanta labarin waɗannan ’yan’uwa a ƙasar Rasha, kuma ta aiko da akwati da kuma wasiƙa. Ga abin da ke cikin wasiƙar: “’Yan’uwa, imani da kuma jimirin ’yan’uwan da ke ƙasar Rasha ya burge yaranmu Cody da Larissa sosai. Sun rubuta katin gaisuwa da wasiƙu kuma mun saka wasu kyauta da za mu so mu aika wa yaran da ke birnin Taganrog. Muna son su san cewa akwai wasu yara ma da suke bauta wa Jehobah a wasu ƙasashe, kuma suna ƙaunarsu.”
Sa’ad da yaran suka karɓi saƙon, sai su ma suka aika wasiƙa da hotuna da suka nuna cewa su ma suna godiya ga iyalin da ke ƙasar Ostareliya. Abin da Cody da Larissa suka yi ya burge wani ɗan’uwa da ke ofishin ƙasar Rasha sosai har ya rubuta musu wasiƙa. Ya ce: “Ba shi da daɗi ko kaɗan idan an hukunta yara da manya a kan laifin da ba su yi ba. ’Yan’uwanmu da ke birnin Taganrog ba su yi laifi ba, amma an ƙwace wurin taronsu. Kuma hakan ya sa su baƙin ciki sosai. Za su yi farin ciki sosai idan sun ga cewa ’yan’uwa a wasu ƙasashe ba su manta da su ba. Muna godiya sosai don ƙauna da kuma karimcinku.”—Zab. 8:2.
Shaidun da ke dukan duniya kamar iyali ɗaya suke, kuma ƙaunar da muke wa juna tana taimaka mana mu jimre da matsalolin rayuwa. Mutane suna kala wa Shaidun Jehobah sharri cewa littattafanmu suna sa mutane su tsani juna. Amma, yaranmu a ƙasashe da kuma al’adu dabam-dabam sun nuna cewa suna ƙaunar juna. Hakan ya nuna cewa kalaman Yesu gaskiya ne. Ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—Yoh. 13:35.
[Hotona a shafi na 32]
Yaran da ke ƙasar Rasha (hagu) da suka karɓi kyauta daga yaran da ke ƙasar Ostareliya (dama)