Abin Da Ke Ciki
15 Ga Nuwamba, 2012
© 2012 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.
Na Nazari
TALIFOFIN NAZARI
24-30 GA DISAMBA, 2012
‘Ka Koya Mini na Aikata Nufinka’
SHAFI NA 3 • WAƘOƘI: 69, 120
31 GA DISAMBA, 2012–6 GA JANAIRU, 2013
Yesu Ya Kafa Misali na Tawali’u
SHAFI NA 10 • WAƘOƘI: 84, 82
7-13 GA JANAIRU, 2013
SHAFI NA 15 • WAƘOƘI: 26, 68
14-20 GA JANAIRU, 2013
Ka Amfana Daga Yadda Jehobah Yake Gafarta Mana?
SHAFI NA 21 • WAƘOƘI: 67, 91
21-27 GA JANAIRU, 2013
SHAFI NA 26 • WAƘOƘI: 77, 118
MANUFAR TALIFOFIN NAZARI
TALIFIN NAZARI NA 1 SHAFUFFUKA NA 3-7
Sarki Dauda na ƙasar Isra’ila ta dā ya ɗaukaka sunan Jehobah da kuma nufe-nufensa. Ya kuma san ma’anar ƙa’idodin Allah kuma ya roƙi Jehobah ya koya masa yadda zai yi nufinsa, kamar yadda wannan talifin ya nuna. Wannan talifin zai kuma koya mana abin da ya sa ya kamata mu riƙa yin kome bisa ga nufin Allah a kowane lokaci.
TALIFOFIN NAZARI NA 2, 3 SHAFUFFUKA NA 10-19
Kiristoci sun san cewa suna bukatar su zama masu tawali’u domin su mabiyan Yesu ne. Talifi na farko ya tattauna misali mai kyau na tawali’u da Yesu ya kafa mana. Talifi na biyu ya tattauna yadda za mu koya kuma mu kasance da tawali’u.
TALIFOFIN NAZARI NA 4, 5 SHAFUFFUKA NA 21-30
Waɗannan talifofin za su nuna mana yadda Jehobah yake shirye ya gafarta zunubai, har da mafi tsanani ma. A wasu yanayi, yana da wuya mu gafarta wa wasu. Duk da haka, ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mana mu riƙa gafartawa kullum.
A FITOWAR NAN
8 Yalwarsu ta Biya Bukatar Wasu
BANGO: Yana wa’azi a ƙaramin garin Albarracín da ke Sifen ta tsakiya. Akwai masu shela 78 a ikilisiyar Teruel. Waɗannan ’yan’uwan suna wa’azi a garin Albarracín da kuma wasu garurruka da ƙauyuka 188
SIFEN
YAWAN JAMA’A
47,042,900
MASU SHELA
111,101
WAƊANDA SUKA HALARCI TUNA DA MUTUWAR YESU A 2012
192,942