Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/15 pp. 27-31
  • Kana Barin E Ɗinka Ya Zama E Da Gaske?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Barin E Ɗinka Ya Zama E Da Gaske?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YESU NE FITACCEN MISALI
  • BULUS YA CIKA ALKAWARINSA
  • WASU MISALAI MASU KYAU
  • ALKAWARI MAFI MUHIMMANCI DA KA YI
  • YADDA ZA KA AMFANA DAGA BABBAN FIRIST DA KUMA SARKINMU
  • Ka Yi Biyayya Don Ka Amfana Daga Alkawuran Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Shin Kuna ce I, daga Baya Kuma Ku ce A’a?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/15 pp. 27-31

Kana Barin E Ɗinka Ya Zama E Da Gaske?

“Bari zancenku ya zama, I, i; da A’a, a’a.”—MAT. 5:37.

MECE CE AMSARKA?

Mene ne Yesu ya ce game da rantsuwa?

Me ya sa Yesu misali mai kyau ne na mutumin da ya cika alkawarinsa?

A waɗanne fannoni na rayuwa ne ya kamata mu bar E ɗinmu ya zama E?

1. Mene ne Yesu ya ce game da rantsuwa, kuma me ya sa?

KIRISTOCI ba sa bukatar su rantse kafin a amince da abin da suka ce. Suna yin biyayya ga abin da Yesu ya ce: “Bari zancenku ya zama, I, i.” Hakan yana nufin cewa mutum ya riƙa faɗin gaskiya a kowane lokaci. Amma, kafin ya faɗi wannan, ya ce: “Ba za ku yi rantsuwa ko kaɗan ba.” Yesu ya faɗi hakan ne domin yadda mutane suke rantsuwa a duk abin da suka ce, ko da ba su da niyyar yin abin da suka yi alkawarinsa. Idan mutum ya yi rantsuwa bisa abin da ba zai iya yi ba kuma fa? Yana nuna cewa ba za a iya amince da shi ba, kuma “mugun” yana da tasiri bisa kansa.—Karanta Matta 5:33-37.

2. Me ya sa rantsuwa ba laifi ba ne a wani lokaci?

2 Yesu yana nufin cewa bai dace ba ne a yi rantsuwa sam? Kamar yadda muka koya a talifin da ya gabata, Jehobah da bawansa Ibrahim sun yi rantsuwa a kan batutuwa masu muhimmanci. Ban da haka ma, Dokar Allah ta bukaci a yi rantsuwa don a sasanta wasu irin jayayya. (Fit. 22:10, 11; Lit. Lis. 5:21, 22) Saboda haka, Kirista yana iya yin rantsuwa a kotu don ya tabbatar da abin da ya faɗa. A wani lokaci, Kirista yana iya jin cewa ya dace ya yi rantsuwa don ya tabbatar da alkawarin da ya yi ko abin da ya faɗa. Yesu ya faɗi gaskiya sa’ad da babban firist na Yahudawa suka ce sai ya rantse. (Mat. 26:63, 64) Amma, Yesu ba ya bukatar ya rantse tun da yake yana faɗin gaskiya a kowane lokaci. Duk da haka, yakan ce: “Hakika, hakika, ina ce muku” domin mutane su amince da shi. (Yoh. 1:51; 13:16, 20, 21, 38) Bari mu ga abin da misalin Yesu da Bulus da kuma wasu da zancensu E ya zama E ya koya mana.

YESU NE FITACCEN MISALI

3. Wane alkawari ne Yesu ya yi, kuma mene ne Jehobah ya yi?

3 “Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah.” (Ibran. 10:7) Waɗannan kalaman sun nuna cewa Yesu ya ba da kansa don ya yi dukan abin da aka annabta game da Zuriyar da aka yi alkawarinta, har da “ƙuje duddugensa” da Shaiɗan zai yi. (Far. 3:15) Babu ɗan Adam da ya taɓa ɗaukan irin wannan nawayar. Jehobah ya nuna cewa ya amince da Ɗansa, ko da yake bai bukaci Yesu ya yi rantsuwa ba.—Luk 3:21, 22.

4. Mene ne Yesu ya yi don E ɗinsa ya zama E?

4 Yesu yana cika alkawarinsa a kowane lokaci. Ba ya barin kome ya hana shi yin aikin da Ubansa ya sa shi, wato, yin wa’azin Mulkin Allah da kuma almajirtar da mutanen Jehobah ya jawo. (Yoh. 6:44) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu yana cika alkawarinsa. Ya ce: “Dukan alkawarin Allah cikarsu a gare shi take.” (2 Kor. 1:20, Littafi Mai Tsarki) Hakika, Yesu ne fitaccen misali na wanda ya cika alkawarin da ya yi wa Ubansa. Yanzu, bari mu yi la’akari da wani da ya yi iya ƙoƙarinsa don ya bi misalin Yesu.

BULUS YA CIKA ALKAWARINSA

5. Wane misali ne Bulus ya kafa mana?

5 “Me zan yi, Ubangiji?” (A. M. 22:10) Abin da Bulus, wanda a lokacin ake kiransa Shawulu ya ce ke nan sa’ad da Yesu ya bayyana masa a wahayi. Yesu yana son Shawulu ya daina tsananta wa almajiransa. A sakamako, Bulus ya tuba, aka yi masa baftisma kuma ya soma wa’azi game da Yesu ga dukan al’umma. Bulus ya ci gaba da kiran Yesu “Ubangiji,” kuma ya yi masa biyayya har bar duniya. (A. M. 22:6-16; 2 Kor. 4:5; 2 Tim. 4:8) Bulus ya bambanta da wasu da Yesu ya ce game da su: “Don menene kuwa kuna kirana, Ubangiji, Ubangiji, amma ba ku yi abin da na faɗi ba?” (Luk 6:46) Hakika, Yesu yana son dukan waɗanda suke kiransa Ubangiji su bi misalin Bulus ta wajen cika alkawarinsu.

6, 7. (a) Me ya sa Bulus ya canja tsarin tafiyarsa zuwa Korinti, kuma me ya sa bai dace da wasu suka kushe shi ba? (b) Me ya kamata mu yi wa waɗanda suke shugabanci a tsakaninmu?

6 Bulus ya yi wa’azin Mulki da ƙwazo a dukan ƙasashen Asiya Ƙarama da Turai. Ya kafa ikilisiyoyi da yawa kuma ya sake ziyartarsu. A wasu lokatai, ya rantse cewa abin da ya rubuta gaskiya ne. (Gal. 1:20) Sa’ad da wasu Korintiyawa suka soma shakkar abin da Bulus ya rubuta, sai ya kāre kansa. Ya ce: “Kamar yadda Allah mai aminci ne, maganarmu zuwa gareku ba i da a’a ba ce.” (2 Kor. 1:18) Sa’ad da Bulus ya rubuta musu wannan wasiƙar, ya riga ya bar Afisa yana hanyar zuwa Korinti kuma ya bi ta Makidoniya. Da ma ya yi shirin sake ziyartar Korinti kafin ya shiga Makidoniya. (2 Kor. 1:15, 16) Kamar yadda masu kula masu ziyara suke yi a yau, a wani lokaci suna iya canja tsarin tafiyarsu. Suna canja tsarin ne don dalilai masu muhimmanci. Bulus ma ya canja tsarinsa na ziyarar Korinti ne domin dalili mai kyau. Wane dalili ne?

7 Bayan Bulus ya gama shirye-shirye, sai ya sami labari cewa ikilisiyar da ke Korinti suna da matsalar tsatsaguwa da kuma lalata a tsakaninsu. (1 Kor. 1:11; 5:1) Ya yi musu gargaɗi a wasiƙarsa ta farko domin a warware matsalolin. Maimakon ya tafi Korinti daga Afisa, Bulus ya canja tsarin tafiyarsa domin ’yan’uwan su samu zarafin yin amfani da gargaɗin da ya bayar. Hakan zai ba shi damar ƙarfafa su sa’ad da ya dawo. Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta biyu don ya tabbatar musu da abin da ya sa ya canja tsarin tafiyarsa. Ya ce: “Ina kiran Allah domin mashaidi ga raina, na ƙi zuwa Korintus domin in sawaƙa maku.” (2 Kor. 1:23) Kada mu zama kamar waɗanda suka kushe Bulus, amma mu daraja waɗanda aka naɗa su shugabance mu. Ya kamata mu yi koyi da Bulus, kamar yadda ya yi da Yesu.—1 Kor. 11:1; Ibran. 13:7.

WASU MISALAI MASU KYAU

8. Wane misali ne Rifkatu ta kafa mana?

8 “Zan tafi.” (Far. 24:58) Kalaman da Rifkatu ta furta ke nan, don ta nuna wa mahaifiyarta da wanta cewa tana da niyya ta zama matar Ishaƙu ɗan Ibrahim. Za ta bar gida ranar nan kuma ta yi tafiya da baƙo har tsawon mil 500. (Far. 24:50-58) Rifkatu ta cika alkawarinta, kuma ta zama mata mai tsoron Allah ga Ishaƙu. Ta yi zaman baƙuwa a tanti cikin Ƙasar Alkawari duk rayuwarta. Allah ya albarkace ta, kuma ta haifi mutumin da ya zama sashe na zuriyar da aka yi alkawarinta wato, Yesu Kristi.—Ibran. 11:9, 13.

9. Ta yaya Ruth ta cika alkawarinta?

9 “A’a, mu dai za mu koma tare da ke zuwa wurin mutanenki.” (Ruth 1:10) Abin da gwauraye biyu na ƙasar Mowab suka gaya wa surukuwarsu Naomi ke nan. Ruth da Orpah sun faɗi hakan ne sa’ad da Naomi wadda ita ma gwauruwa ce za ta koma Baitalami. Naomi ta nace su koma ƙasarsu. A ƙarshe, Orpah ta koma amma Ruth ta bar A’a nata ya zama A’a. (Karanta Ruth 1:16, 17.) Ta bar iyalinta da bauta ta ƙarya da ke ƙasar Mowab, kuma ta manne wa Naomi. Ta ci gaba da bauta wa Jehobah a dukan rayuwarta. Jehobah ya albarkace ta, kuma ta zama ɗaya cikin mata biyar da suka zama kakannin-kakannin Yesu, kamar yadda littafin Matta ya ambata.—Mat. 1:1, 3, 5, 6, 16.

10. Me ya sa Ishaya ya zama misali mai kyau a gare mu?

10 “Ga ni; ka aike ni.” (Isha. 6:8) Kafin ya yi wannan furucin, Ishaya ya ga Jehobah a wahayi yana zaune a kan kursiyinsa. Sa’ad da yake kallo, sai ya ji Jehobah ya ce: “Wa zan aika, kuma wanene za ya tafi domin mu?” Jehobah yana neman wani da zai aika ya idar da saƙonsa ga mutanensa masu rashin biyayya. Sai Ishaya ya ce: “Ga ni; ka aike ni,” kuma ya cika alkawarinsa. Ya yi hidima a matsayin annabi na tsawon shekaru fiye da 46, yana idar da saƙo cewa Allah zai hukunta mutanensa masu rashin biyayya. Kuma ya annabta cewa Allah zai dawo da su ƙasarsu don su riƙa bauta masa.

11. (a) Me ya sa yake da muhimmanci E ɗinmu ya zama E? (b) Ka ba da misalin waɗanda ba su bar zancensu E ya zama E ba.

11 Don me Jehobah ya sa aka rubuta waɗannan misalan a cikin Littafi Mai Tsarki? Kuma me ya sa yake da muhimmanci mu bar E namu ya zama E? Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi cewa “masu-tada alkawari” sun “isa mutuwa.” (Rom. 1:31, 32) Wasu da Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa ba su bar E nasu ya zama E ba, su ne Fir’auna na ƙasar Masar da Sarki Zedekiya na Yahuda da Hananiya da kuma Safiratu. Sun kafa misali marar kyau kuma sun sha wuya.—Fit. 9:27, 28, 34, 35; Ezek. 17:13-15, 19, 20; A. M. 5:1-10.

12. Mene ne zai taimaka mana mu riƙa cika alkawarinmu?

12 Muna rayuwa cikin “kwanaki na ƙarshe,” shi ya sa akwai mutane “marasa tsarkaka” da suke “riƙe da siffofin ibada, amma suna saɓa wa ikonta.” (2 Tim. 3:1-5) Wajibi ne mu guji irin wannan mugun tarayyar. Maimakon haka, ya kamata mu riƙa cuɗanya a kai a kai da waɗanda suke barin E nasu ya zama E.—Ibran. 10:24, 25.

ALKAWARI MAFI MUHIMMANCI DA KA YI

13. Wane alkawari ne ya fi muhimmanci ga mabiyin Yesu Kristi?

13 Keɓe kai ga Jehobah shi ne alkawari mafi muhimmanci da mutum ya taɓa yi. Ana tambayar waɗanda suke son su zama almajiran Yesu sau uku ko za su iya cika alkawarinsu. (Mat. 16:24) A lokacin da wani yake son ya zama mai shela marar baftisma, dattawa sukan yi masa wannan tambayar, “Ka tabbata kana son ka zama Mashaidin Jehobah?” Daga baya idan mutumin ya samu ci gaba sosai kuma yana son a yi masa baftisma, sai dattawa su sake tambayarsa, “Ka keɓe kanka cikin addu’a ga Jehobah?” A ƙarshe, a ranar da ake baftisma, ana tambayar waɗanda suke son su yi baftisma, “Bisa ga hadayar Yesu Kristi, kun tuɓa daga zunubanku kuma kun keɓe kanku ga Jehobah domin ku yi nufinsa?” A gaban dukan waɗanda suka halarci taron, suna amsawa E ga alkawarin da suka yi na bauta wa Allah har abada.

14. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu riƙa yi wa kanmu?

14 Ko da ba ka daɗe da yin baftisma ba, ko kuma ka yi shekaru da yawa kana bauta wa Allah, kana bukatar ka binciki kanka a kai a kai da waɗannan tambayoyin: ‘Ina bin misalin Yesu kuwa ta wajen cika alkawari mafi muhimmanci da na yi? Ina yin biyayya ga Yesu kuwa ta wurin saka wa’azi da kuma almajirtarwa a matsayin aikin da ya fi muhimmanci a rayuwata?’—Karanta 2 Korintiyawa 13:5.

15. A waɗanne fannoni na rayuwa ne ya kamata E ɗinmu ya zama E?

15 Cika alkawari na keɓe kai da muka yi ya ƙunshi kasancewa da aminci a wasu batutuwa masu muhimmanci. Alal misali: Kana da aure ne? Idan haka ne, ka ci gaba da daraja wa’adin da ka yi cewa za ka ƙaunaci matarka ko mijinki. Ka yi wata yarjejeniya na kasuwanci ne ko kuma ka cika fom na ƙarin gata a ƙungiyar Jehobah? Idan haka ne ka cika alkawarinka. Idan wani da ba shi da kuɗi sosai ya gayyace ka cin abinci a gidansa, kada ka ƙi zuwa don wani mai arziki ma ya gayyace ka. Ka yi alkawari cewa za ka koma ziyara wurin wani da ka yi masa wa’azi? Idan haka ne, bari E naka ya zama E kuma Jehobah zai albarkaci hidimarka.—Karanta Luka 16:10.

YADDA ZA KA AMFANA DAGA BABBAN FIRIST DA KUMA SARKINMU

16. Mene ne ya kamata mu yi idan mun saɓa alkawarinmu?

16 Littafi Mai Tsarki ya ce dukanmu ajizai ne kuma mukan “yi tuntuɓe,” musamman ta yadda muke magana. (Yaƙ. 3:2) Mene ne ya kamata mu yi idan muka ga cewa mun kasa cika alkawarinmu? A Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa, yana yiwuwa a nuna jin ƙai ga duk wanda “ya yi rantsuwa da garaje da bakinsa.” (Lev. 5:4-7, 11) A yau ma, ana iya gafarta wa Kiristoci idan suka kasa cika alkawarinsu. Babban Firist, Yesu Kristi, zai taimaka mana don Jehobah ya gafarta mana idan muka tuba. (1 Yoh. 2:1, 2) Domin mu ci gaba da samun amincewar Allah, wajibi ne mu tuba da gaske. Alal misali, kada saɓa alkawari ya zama jininmu. Kuma, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu magance duk wata matsalar da muka jawo domin mun saɓa alkawarinmu. (Mis. 6:2, 3) Hakika, zai fi kyau mu yi tunani sosai kafin mu yi duk wani alkawari.—Karanta Mai-Wa’azi 5:2.

17, 18. Wace irin rayuwa ce dukan waɗanda suke barin E ɗinsu ya zama E za su more nan ba da daɗewa ba?

17 Dukan bayin Jehobah da suke barin E ɗinsu ya zama E, za su ji daɗin rayuwa a nan gaba. Shafaffu 144,000 za su yi rayuwa marar matuƙa a sama, kuma “za su yi mulki . . . shekara dubu” tare da Yesu. (R. Yoh. 20:6) Mutane da yawa za su more rayuwa a aljanna a duniya, kuma za su zama kamiltattu sa’ad da Kristi, sarkin Mulkin Allah ya soma sarauta bisa duniya.—R. Yoh. 21:3-5.

18 Idan muka kasance da aminci a gwajin da za mu fuskanta a ƙarshen Sarautar Yesu na Shekara Dubu, ba za mu sake shakkar abin da wani ya faɗa ba. (R. Yoh. 20:7-10) A lokacin, idan wani ya ce E, yana nufin E, kuma idan ya ce A’a, yana nufin A’a. Gama, dukan waɗanda suke da rai za su yi koyi da ƙaunatacen Ubanmu na sama, Jehobah “Allah na gaskiya.”—Zab. 31:5.

[Hoto a shafi na 28]

Yesu ya cika alkawarin da ya yi wa Ubansa, tun daga lokacin da ya yi baftisma har mutuwarsa

[Hoto a shafi na 30]

Kana cika alkawari mafi muhimmanci da ka yi kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba