Me Ya Sa ya Kamata Ka Saka Hidimar Jehobah Farko a Rayuwarka?
“Bakina za ya zantar da adalcinka, da cetonka dukan yini.”—ZAB. 71:15.
MECE CE AMSARKA?
Me ya sa Nuhu da Musa da Irmiya da kuma Bulus suka sa Jehobah kan gaba a rayuwarsu?
Waɗanne bincike ne za su sa ka yi shawara game da yadda za ka yi rayuwa?
Me ya sa ka yanke shawarar sa Jehobah kan gaba a rayuwarka?
1, 2. (a) Idan mutum ya yi baftisma, mene ne ya ƙudura aniya zai yi? (b) Ta yaya za mu amfana idan muka yi la’akari da misalan Nuhu da Musa da Irmiya da kuma Bulus?
SA’AD DA ka keɓe kanka ga Allah kuma ka yi baftisma a matsayin mabiyin Yesu, ka ɗauki mataki mai muhimmanci. Keɓe kanka ga Allah ita ce shawara mafi muhimmanci da za ka tsai da. Kamar kana gaya wa Jehobah cewa: ‘Ina son ka zama Shugabana a kowane fannin rayuwata. Ni bawanka ne. Ka tsara mini yadda zan yi amfani da lokacina, ka nuna mini abubuwan da zan sa a kan gaba a rayuwa da kuma yadda zan yi amfani da baiwata da dukiyata.’
2 Idan ka yi baftisma, abin da ka gaya wa Jehobah ke nan. Wannan shawara ce mai kyau da ka yi kuma mataki ne da ya dace. To, yanzu da ka amince cewa Jehobah ya zama shugabanka, yaya kake yin amfani da lokacinka? Misalan Nuhu da Musa da Irmiya da kuma manzo Bulus za su taimaka mana wajen bincika kanmu. Kowanne daga cikinsu ya yi iya ƙoƙarinsa a bautarsa ga Jehobah. Yanayinmu da nasu ɗaya ne. Shawarwarin da suka yi sun nuna abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsu kuma ya kamata hakan ya motsa mu mu bincika yadda muke amfani da lokacinmu.—Mat. 28:19, 20; 2 Tim. 3:1.
KAFIN RIGYAWAR
3. Ta yaya zamaninmu ya yi kama da na Nuhu?
3 Yesu ya kwatanta zamaninmu da na Nuhu. Ya ce, “Kuma kamar yadda kwanakin Nuhu su ke, hakanan kuma bayanuwar Ɗan Mutum za ta zama. Gama kamar yadda suna ci, suna sha, suna aure, suna auraswa a cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa, har randa Nuhu ya shiga cikin jirgi, ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka.” (Mat. 24:37-39) Yawancin mutane a yau ba sa sauraron gargaɗin da bayin Allah suke yi. Ba sa damuwa cewa muna rayuwa a lokaci mai muhimmanci. Mutane da yawa suna kamar mutanen da suka rayu a zamanin Nuhu, ba su gaskata cewa Allah zai halaka miyagun mutane ba. (2 Bit. 3:3-7) Yaya Nuhu ya yi amfani da lokacinsa duk da cewa mutane ba su bi gargaɗin da ya ba su ba?
4. Bayan Jehobah ya ba Nuhu aiki na musamman, yaya Nuhu ya yi amfani da lokacinsa kuma me ya sa ya yi hakan?
4 Allah ya gaya wa Nuhu cewa zai halaka miyagun mutane kuma ya ba shi aiki mai muhimmanci ya yi. Nuhu ya gina jirgi don ceton mutane da dabbobi. (Far. 6:13, 14, 22) Ya gaya wa mutane cewa Allah zai kawo ƙarshen zamaninsu. Manzo Bitrus ya kira shi “mai shelan adalci,” kuma hakan ya nuna cewa Nuhu ya yi aiki tuƙuru don ya sa mutane su fahimci cewa suna raye ne a lokaci mai muhimmanci. (Karanta 2 Bitrus 2:5.) Kana ganin cewa da zai dace Nuhu da iyalinsa su yi amfani da lokacinsu don su yi kasuwanci kuma su fi wasu wadata ko kuma su mai da hankali ga jin daɗin rayuwa? A’a! Don sun san abin da zai faru, kuma hakan ya sa sun guji yin duk wani abu da zai raba hankalinsu.
ZAƁIN DA WANI ƊAN SARKIN MASAR YA YI
5, 6. (a) Me ya sa aka koya wa Musa “dukan hikimar Masarawa”? (b) Me ya sa ya ƙi yin rayuwa a matsayin ɗan sarkin Masar?
5 Yanzu, bari mu koyi darasi daga misalin Musa. ’Yar Fir’auna ta ɗauke shi a matsayin ɗanta kuma ya yi girma a fadar Masar a matsayin ɗan sarki. An koya masa “dukan hikimar Masarawa.” (A. M. 7:22; Fit. 2:9, 10) Babu shakka, an yi masa wannan koyarwar don a shirya shi ne ya soma yin hidima a fadar Fir’auna. Da ya zama mai martaba a gwamnati mafi iko a lokacin, kuma da zai kasance da abubuwa masu kyau kuma da an girmama shi. Amma, waɗannan ne abubuwan da Musa ya sa kan gaba a rayuwarsa?
6 Saboda koyarwa da ya samu daga wajen iyayensa sa’ad da yake ƙarami, Musa ya san alkawarin da Jehobah ya yi wa kakanninsa wato, Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yakubu. Musa ya amince da waɗannan alkawuran. Babu shakka, ya yi tunani sosai a kan rayuwarsa na nan gaba da kuma amincinsa ga Jehobah. Saboda haka, wace shawara ce Musa ya tsai da sa’ad da lokaci ya yi da zai zaɓi ko ya ci gaba da zama ɗan sarki ko kuma ya zama bawa Ba’isra’ila? Musa ya gwammace “a wulakance shi tare da mutanen Allah, da ya ji daɗin nishatsin zunubi domin ’yan kwanaki.” (Karanta Ibraniyawa 11:24-26.) Daga baya, ya bi ja-gorar da Jehobah ya ba shi a kan yadda zai yi amfani da rayuwarsa. (Fit. 3:2, 6-10) Me ya sa Musa ya yi hakan? Domin ya amince da alkawuran da Allah ya yi. Ya san cewa duk wani ci gaba da zai samu a ƙasar Masar ba zai dawamma ba. Hakika, ba da daɗewa ba bayan haka, Allah ya huƙunta wannan al’ummar da annoba goma. Dukan bayin Jehobah za su iya koyon darasi daga misalin Musa. Maimakon neman kayan duniya, ya kamata mu mai da hankali ga Jehobah da kuma aikin da ya ce mu yi.
IRMIYA YA SAN ABIN DA ZAI FARU
7. A wace hanya ce yanayin Irmiya ya zama ɗaya da namu?
7 Wani mutum da ya saka hidimar Jehobah farko a rayuwa kuma shi ne annabi Irmiya. Jehobah ya ba Irmiya aiki a matsayin annabinsa don ya faɗa wa mutane hukuncin da Allah zai yi wa Urushalima da Yahuda da suke bauta wa allolin ƙarya. Yanayin Irmiya ɗaya ne da namu domin ya yi rayuwa ne a “kwanakin ƙarshe” na zamaninsa. (Irm. 23:19, 20) Ya san cewa tabbas zamanin ba zai dawwama ba.
8, 9. (a) Me ya sa Allah ya daidaita tunanin Baruk? (b) Mene ne ya kamata mu yi la’akari da shi sa’ad da muke tattali?
8 Waɗanne abubuwa ne Irmiya ya ƙi yi saboda abin da ya gaskata? Bai yi ƙoƙarin tara kayan duniya ba domin ya san cewa zamanin ba zai dawwama ba. Da a ce ya yi hakan, da wauta ce a gare shi. Amma Baruk, sakataren Irmiya bai fahimci hakan ba. Shi ya sa Allah ya hure Irmiya ya shawarci Baruk cewa: “Duba, abin da na gina, shi zan rushe; abin da na dasa kuma, shi zan tumɓuke; wannan kuwa ko’ina a cikin ƙasan nan. Kana fa biɗa wa kanka manyan abu? kada ka biɗe su: gama, ga shi, zan jawo mugunta a bisa dukan masu-rai, . . . amma zan ba ka naka rai ganima gareka, dukan wuraren da ka tafi.”—Irm. 45:4, 5.
9 Ba mu san ‘manyan abubuwan’ da Baruk ya biɗa wa kansa ba.a Amma, mun san cewa ko mene ne, ba za su dawwama ba, abubuwa ne da Babiloniyawa za su ƙwace sa’ad da suka kai hari ga Urushalima a shekara ta 607 kafin zamaninmu. Mene ne wannan labarin ya koya mana? Muna bukatar mu shirya wasu abubuwa da za mu yi amfani da su don mu biya bukatunmu na yau da kullum. (Mis. 6:6-11) Amma, zai dace idan mun ɓata lokacinmu da kuma ƙarfinmu don biɗan abubuwan da ba za su dawwama ba? Hakika, ƙungiyar Jehobah tana yin tattali don gina sababbin Majami’un Mulki da ofisoshin reshe da kuma wasu ayyuka da suka shafi aikin wa’azi. Waɗannan ayyukan sun bambanta don suna tallafa wa Mulkin Allah ne. Zai dace dukan waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah su yi tattali don Mulkin Allah. Ka gaskata da dukan zuciyarka cewa kana biɗan mulkin Jehobah fiye da kome, kuma kana biɗan adalcinsa?—Mat. 6:33.
“INA LISSAFTA DUKAN ABU HASARA”
10, 11. (a) Kafin Bulus ya zama Kirista, mene ne ya sa a gaba a rayuwarsa? (b) Me ya sa Bulus ya canja muradinsa gaba ɗaya?
10 Yanzu, bari mu tattauna misalin Bulus. Kafin ya zama Kirista, mutane suna ganin cewa Bulus zai yi kuɗi da suna sosai. Ya biɗi ilimi a ƙarƙashin wani sanannen malami a lokacin. Babban firist ya amince da shi kuma ya ba shi wani aiki mai muhimmanci. Ya samu ci gaba fiye da sauran tsaransa. (A. M. 9:1, 2; 22:3; 26:10; Gal. 1:13, 14) Amma, rayuwar Bulus ta canja sa’ad da ya fahimci cewa Jehobah ya yi watsi da Yahudawa a matsayin al’umma.
11 Bulus ya san cewa yin tattali don samun aiki a ƙarƙashin tsarin Yahudawa ba zai sa ya samu albarkar Jehobah ba. (Mat. 24:2) Bulus ya fahimci nufin Allah kuma ya san babban gata ne ya saka hannu a aikin wa’azi. Har ma ya ce abubuwan da yake biɗa a dā “hasara” ne. Bulus ya yi watsi da addinin Yahudawa kuma ya yi amfani da sauran kwanakinsa a duniya a yin wa’azin bishara.—Karanta Filibiyawa 3:4-8, 15; A. M. 9:15.
KA BINCIKA ABUBUWA DA SUKA FI MUHIMMANCI A RAYUWARKA
12. Bayan Yesu ya yi baftisma, wane aiki ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa?
12 Nuhu da Musa da Irmiya da Bulus da kuma mutane da yawa kamar su, sun yi amfani da lokacinsu da kuzarinsu a biɗan ayyukan da suka shafi bautar Allah. Sun kafa mana misali mai kyau. Ko da yake, wanda ya kafa mana misalin mafi kyau a bautar Allah shi ne Yesu. (1 Bit. 2:21) Bayan ya yi baftisma, Yesu ya yi amfani da rayuwarsa a duniya don yin wa’azin bishara da kuma girmama Jehobah. Saboda haka, ya kamata bautar Jehobah ta kasance kan gaba a rayuwar duk mutumin da ya amince cewa Jehobah ne Shugabansa. Bautar Jehobah ce kan gaba a rayuwarka? Ta yaya za mu daidaita yin aiki tuƙuru a hidimar Jehobah da kuma yin ayyukanmu?—Karanta Zabura 71:15; 145:2.
13, 14. (a) Mene ne ake ƙarfafa dukan Kiristoci su yi addu’a a kai? (b) Wane farin ciki ne mutanen Allah za su iya samu?
13 A cikin shekaru da yawa yanzu, ƙungiyar Jehobah tana ƙarfafa Kiristoci su yi addu’a don su samu damar yin hidimar majagaba. Wasu amintattun bayin Jehobah ba za su iya yin wa’azi na sa’o’i 70 a duk wata ba saboda yanayin da suke ciki. Bai kamata hakan ya sa su baƙin ciki ba. (1 Tim. 5:8) Kai kuma fa? Za ka iya yin wa’azi a matsayin majagaba kuwa?
14 Ka tuna da farin cikin da bayin Jehobah suka yi a lokacin tuna da mutuwar Yesu na bana. A watan Maris, an ba ’yan’uwa gata na musamman don su ba da rahoton sa’o’i 30 ko 50 a matsayin masu hidimar majagaba na ɗan lokaci. (Zab. 110:3) Miliyoyi sun saka hannu a wannan hidimar kuma hakan ya sa ’yan’uwa a ikilisiya farin ciki sosai. Za ka iya daidaita harkokinka don ka ci gaba da samun farin cikin da ake samu a hidimar majagaba na ɗan lokaci? Sa’ad da ɗan’uwa da ya yi baftisma ya fita wa’azi a matsayin mai hidimar majagaba na ɗan lokaci, yakan yi farin ciki a ƙarshen kowace rana kuma zai iya cewa: “Jehobah, na yi iya ƙoƙarina a hidimarka.”
15. Wane muradi ne ya kamata matashi Kirista ya kasance da shi sa’ad da yake makaranta?
15 Idan kai matashi ne wanda ya kusan gama makaranta, wataƙila kana da ƙoshin lafiya kuma ba ka da ayyuka da yawa. Ka yi tunani sosai kuwa game da zama mai hidimar majagaba na kullum? A bayyane yake cewa malamanka a makaranta suna gani cewa zuwa jami’a ko kwaleji shi ne zai sa ka samu aiki mai kyau da kuma ci gaba a rayuwa. Suna da wannan ra’ayin ne domin sun amince ne da ƙungiyoyin ’yan Adam da kuma biyan kuɗi. Kuma waɗannan abubuwan ba za su dawwama ba. Amma, idan ka saka hidimar Jehobah farko a rayuwarka, za ka yi amfani da lokacinka yadda ya dace kuma yin hakan zai sa ka dawwama. Kuma zai nuna cewa kana koyi da Yesu. Irin wannan shawara mai kyau zai sa ka yi farin ciki. Zai kāre ka. Ƙari ga hakan, zai nuna cewa ka ƙuduri aniyar cika alkawarin da ka yi sa’ad da ka keɓe kanka ga Jehobah.—Mat. 6:19-21; 1 Tim. 6:9-12.
16, 17. Waɗanne tambayoyi ne Kiristoci za su iya yi wa kansu game da hidimarsu ga Jehobah?
16 Bayin Jehobah da dama a yau suna aiki na sa’o’i da yawa don su biya bukatun iyalinsu. Duk da haka, akwai waɗanda suke aiki na tsawon lokaci da ya wuce kima. (1 Tim. 6:8) ’Yan kasuwa da masu talla suna son mu yi tunani cewa ba za mu iya rayuwa ba idan ba mu saya duk wani sabon abu da ake yayinsa a kasuwa ba. Amma, Kiristoci na gaskiya ba za su yarda Shaiɗan da kuma duniyarsa su zaɓa musu abin da ya fi muhimmanci a rayuwa ba. (1 Yoh. 2:15-17) Waɗanda suka yi ritaya daga aikin gwamnati ko aikin kamfani fa? Abubuwan da ya fi dacewa da za su yi da sabon zarafin da suka samu shi ne yin hidimar majagaba da kuma saka hidimar Jehobah kan gaba a rayuwarsu.
17 Duk waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah za su iya yi wa kansu waɗannan tambayoyin: Ina sa al’amuran Mulki kan gaba a rayuwata kuwa? Ina nuna irin halin sadaukarwa da Yesu ya nuna? Ina bin shawarar Yesu na kasancewa mai binsa a ko yaushe? Zan iya daidaita harkokina don in ƙara lokacin da nake yin wa’azi da kuma wasu ayyuka da suka shafi hidimar Jehobah? Ko da ba zan iya ƙara lokacin da nake wa’azi a yanzu ba, ina ci gaba da kasancewa da halin sadaukarwa?
“KU YI NUFI HAR KU AIKA KUMA”
18, 19. Mene ne za ka iya yin addu’a a kai, kuma me ya sa wannan roƙon zai faranta wa Jehobah rai?
18 Ƙwazon da mutanen Jehobah suke nunawa abin ban farin ciki ne. Duk da haka, wasu za su ji cewa ba sa sha’awar hidimar majagaba ko kuma ba su cancanta ba, ko da a ce suna da zarafin yin haka. (Fit. 4:10; Irm. 1:6) Idan haka ne ka ke ji, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Bulus ya ce Jehobah ne “yana aiki a cikinku da za ku yi nufi har ku aika kuma.” (Filib. 2:13) Idan ba ka da sha’awar ƙara inganta hidimarka, ka roƙi Jehobah ya sa ka kasance da sha’awa da kuma ƙwazon yin hakan.—2 Bit. 3:9, 11.
19 Nuhu da Musa da Irmiya da Bulus da kuma Yesu mutane ne masu aminci. Sun yi amfani da lokacinsu don su sanar da mutane game da hukuncin Jehobah. Ba su yarda wani abu ya raba hankalinsu ba. Ƙarshen wannan yanayin da duniya take ciki a yau ya yi kusa sosai, saboda haka, ya kamata dukanmu da muka keɓe kanmu ga Jehobah mu tabbata cewa muna yin iya ƙoƙarinmu mu bi misalan da waɗannan bayin Allah suka kafa. (Mat. 24:42; 2 Tim. 2:15) Idan mun yi hakan, za mu faranta wa Jehobah rai kuma za mu samu albarka sosai.—Karanta Malakai 3:10.
[Hasiya]
a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2008, shafuffuka na 8 da 9, sakin layi na 7-9.
[Hoto a shafi na 21]
Mutane ba su ji gargaɗin da Nuhu ya ba su ba
[Hoto a shafi na 24]
Ka yi tunani sosai game da zama majagaba na kullum kuwa?