“Shugaba Ɗaya Gare Ku, Wato Almasihu”
“Kada . . . a kira ku shugabanni, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato Almasihu.”—MAT. 23:9, 10, Littafi Mai Tsarki.
1. Wanene Shaidun Jehobah suka ɗauka Shugaba, kuma me ya sa?
COCIN Kiristendom suna da shugabanni ’yan Adam, kamar su paparuma, da kuma shugabannin coci dabam dabam da sauran addinai. Shaidun Jehobah ba su da shugaba ɗan Adam. Su ba almajirai ko mabiyan kowanne ɗan Adam ba ne. Wannan ya yi daidai da furcin annabci da Jehobah ya yi game da Ɗansa: “Ga shi, na sanya shi shaida ga al’ummai, shugaba da mai-mulki ga al’ummai.” (Isha. 55:4) Ikilisiyar shafaffun Kiristoci na dukan duniya da abokansu “waɗansu tumaki” ba sa son shugaba fiye da wanda Jehobah ya ba su. (Yoh. 10:16) Sun goyi bayan furcin Yesu: “Shugaba ɗaya gare ku, wato Almasihu.”—Mat. 23:10, LMT.
Ɗan Sarki na Ruhaniya na Isra’ila
2, 3. Wane matsayi mai muhimmanci ne Ɗan Allah ya cika a Isra’ila?
2 Ƙarnuka kafin ya ƙafa ikilisiyar Kirista, Jehobah yana da mala’ikan da ya shugabanci mutanensa Isra’ila. Bayan ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar, Jehobah ya gaya musu: “Ga shi, ina aika mala’ika a gabanka, wanda za ya kiyaye ka cikin tafarki, ya kai ka cikin wurin da na shirya. Ku lura da shi, ku kasa kunne ga muryatasa; kada ku cakune shi: gama ba za ya gafarta kurakuranku ba: gama sunana yana cikinsa.” (Fit. 23:20, 21) Daidai ne mu gaskata cewa Ɗan fari na Allah ne wannan mala’ika, wanda ‘sunan Jehobah yake cikinsa.’
3 Kafin a haife shi a matsayin ɗan Adam, mai yiwuwa Ɗan Allah yana da suna Mika’ilu. A cikin littafin Daniel an kira Mika’ilu “sarkin” mutanen Daniel, Isra’ila. (Dan. 10:21) Almajiri Yahuda ya nuna cewa Mika’ilu ya sa hannu a harkokin Isra’ila tun kafin kwanakin Daniel. Bayan mutuwar Musa, wataƙila Shaiɗan ya yi niyyar yin amfani da gawar don ya biya bukatunsa, wataƙila ya zuga Isra’ilawa su bauta wa gunki. Mika’ilu ya ɗauki mataki don ya hana shi. Yahuda ya rubuta: “Mika’ilu shugaban mala’iku, sa’anda yana muhawara da Shaitan yana gardama da shi a kan jikin Musa, bai yi saurin furta masa shari’a da zafin magana ba, amma ya ce, Ubangiji ya tsauta maka.” (Yahu. 9) Kafin a kewaye Yariko, babu shakka, Mika’ilu ne “Sarkin rundunar Ubangiji” wanda ya bayyana ga Joshua don ya sake tabbatar da shi cewa Allah yana goyon bayansa. (Karanta Joshua. 5:13-15.) Sa’ad da wani aljani mai ƙarfi ya yi ƙoƙarin hana wani mala’ika ya idar da wani saƙo mai muhimmanci ga annabi Daniel, Mika’ilu shugaban mala’iku ya zo ya taimaka wa wannan mala’ikan.—Dan. 10:5-7, 12-14.
Shugaba da Aka Yi Annabcinsa Ya Iso
4. Wane annabci ne aka yi game da zuwan Almasihu?
4 Kafin aukuwar abin da aka ambata a baya, Jehobah ya aika mala’ikansa Jibra’ilu zuwa wurin annabi Daniel don ya gaya masa annabci game da zuwan “Masiya [Shugaba].” (Dan. 9:21-25)a A daidai lokaci, a ƙarshen shekara ta 29 A.Z., Yohanna ya yi wa Yesu baftisma. An zuba ruhu mai tsarki a kan Yesu, hakan ya sa ya zama Shafaffe, wato, Kristi, Almasihu. (Mat. 3:13-17; Yoh. 1:29-34; Gal. 4:4) Saboda haka, zai zama Shugaban da babu kamarsa.
5. Menene Kristi ya yi a matsayin Shugaba a lokacin da yake hidima a duniya?
5 Daga somawar hidimarsa a duniya, Yesu ya nuna cewa shi ne “Masiya [Shugaba].” Cikin ’yan kwanaki da soma hidimarsa a duniya, ya soma tara almajirai, kuma ya yi mu’ujizarsa ta farko. (Yoh. 1:35–2:11) Almajiransa sun bi shi yayin da yake tafiya zuwa ko’ina a ƙasar, yana wa’azin bisharar Mulki. (Luk 8:1) Ya koya musu aikin wa’azi kuma ya yi ja-gora a wa’azi da koyarwa, ya kafa misali mai kyau. (Luk 9:1-6) Ya kamata dattawa Kiristoci a yau su yi koyi da shi a wannan batun.
6. A wace hanya ce Kristi ya zama Makiyayi da Shugaba?
6 Yesu ya yi nuni ga wani fanni na shugabancinsa ta wajen kwatanta kansa da makiyayi mai ƙauna. Makiyaya na gabas suna ja-gorar tumakinsu a zahiri. A cikin littafin nan The Land and the Book, W. M. Thomson ya rubuta: “Makiyayi yana kasancewa a gaba, ba kawai don ya nuna musu hanya ba, amma don ya tabbata cewa babu damuwa kuma suna iya bin hanyar. . . . Da sandarsa, yana yi wa garken ja-gora zuwa wuri mai dausayi, kuma yana kāre su daga maƙiyansu.” Da yake nuna cewa shi Makiyayi ne da Shugaba na gaske, Yesu ya ce: “Ni ne makiyayi mai-kyau: makiyayi mai-kyau yakan bada ransa domin tumaki. Tumakina suna jin muryata, na kuwa san su, suna biyona kuma.” (Yoh. 10:11, 27) Don ya cika maganarsa, Yesu ya yi mutuwar hadaya domin tumakinsa, amma Jehobah ya ta da shi ya zama “Shugaba da kuma Mai Ceto.”—A. M. 5:31, LMT; Ibran. 13:20.
Mai Kula da Ikilisiyar Kirista
7. Ta hanyar menene Yesu yake kula da ikilisiyar Kirista?
7 Gab da komawarsa sama, Yesu da aka ta da daga matattu ya gaya wa almajiransa: “Dukan hukunci a cikin sama da ƙasa an bayas gareni.” (Mat. 28:18) Jehobah ya sa Yesu ya aika da ruhu mai tsarki don ya ƙarfafa almajiransa a koyarwar Kirista. (Yoh. 15:26) Yesu ya zuba wannan ruhun a kan Kiristoci na farko a Fentakos na shekara ta 33 A.Z. (A. M. 2:33) Zuba wannan ruhu mai tsarki ne somawar ikilisiyar Kirista. Jehobah ya naɗa Ɗansa shugaba a sama bisa dukan ikilisiyoyi da ke duniya. (Karanta Afisawa 1:22; Kolosiyawa 1:13, 18.) Yesu yana yi wa ikilisiyar Kirista ja-gora ta wurin ruhu mai tsarki na Jehobah, kuma yana da mala’iku da suke yi masa hidima waɗanda aka ‘sarayar da su a ƙarƙashinsa.’—1 Bit. 3:22.
8. Waɗanne mutane Kristi ya yi amfani da su a duniya a ƙarni na farko don ya ja-goranci almajiransa, kuma waɗanne mutane yake amfani da su a yau?
8 Kuma ta wurin ruhu mai tsarki, Kristi ya ba da “kyautai ga mutane,” wasu a matsayin “makiyaya da malaman koyarwa” a cikin ikilisiya. (Afis. 4:8, 11) Manzo Bulus ya aririci Kiristoci masu kula: “Ku tsare kanku, da dukan garke kuma, wanda Ruhu Mai-tsarki ya sanya ku shugabannai a ciki, garin ku yi kiwon ikilisiyar Allah.” (A. M. 20:28) Sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista, dukan waɗannan masu kula maza ne shafaffu. Manzanni da dattawa na ikilisiyar Urushalima ne hukumar mulki. Kristi ya yi amfani da wannan hukumar mulki ya ja-goranci dukan rukuni na ‘’yan’uwansa’ shafaffu a duniya. (Ibran. 2:11; A. M. 16:4, 5) A wannan zamani na ƙarshe, Kristi ya ɗanka “dukan abin da yake da shi,” wato, dukan abubuwa na Mulkin a duniya ga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da kuma wakilinsa Hukumar Mulki, rukunin maza Kiristoci shafaffu. (Mat. 24:45-47) Shafaffu da abokansu waɗansu tumaki sun fahimci cewa ta wajen bin ja-gorar Hukumar Mulki na zamani, suna bin Shugabansu, Kristi.
Kristi Ne ya Fara Aikin Wa’azi
9, 10. Ta yaya Kristi ya ja-goranci al’amura game da yaɗa bisharar Mulki?
9 Tun daga farko, Yesu da kansa ne ya ja-goranci aikin wa’azi da koyarwa da ake yi a dukan duniya. Ya kafa tsarin da za a isar da bisharar Mulkin ga mazauna na duniya. A lokacin hidimarsa, ya ba manzanninsa umurni: “Kada ku bi ta hanyar Al’ummai, kada ku shiga kowane birni kuma na Samariyawa: sai dai ku tafi wurin batattun tumaki na gidan Isra’ila. A cikin tafiyarku kuma ku yi wa’azi, ku ce, Mulkin sama ya kusa.” (Mat. 10:5-7) Sun yi hakan da himma tsakanin Yahudawa da waɗanda suka shiga Yahudanci, musamman bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z.—A. M. 2:4, 5, 10, 11; 5:42; 6:7.
10 Daga baya, ta wurin ruhu mai tsarki, Yesu ya yaɗa aikin wa’azin Mulki ga Samariyawa da kuma waɗanda ba Yahudawa ba. (A. M. 8:5, 6, 14-17; 10:19-22, 44, 45) Da niyyar ƙarfafa yaɗa bishara tsakanin al’ummai, Yesu da kansa ya motsa Shawulu na Tarsus ya zama Kirista. Yesu ya umurci almajirinsa Hananiya: “Tashi, ka tafi cikin hanya wadda ana ce da ita Miƙaƙiya, a cikin gidan Yahuda sai ka yi tambayar wani mutum, sunansa Shawulu, mutumin Tarsus . . . Yi tafiyarka: gama wannan santali zaɓaɓe ne a gare ni, zai ɗauki sunana gaban al’ummai da sarakuna, da ’ya’yan Isra’ila.” (A. M. 9:3-6, 10, 11, 15) “Wannan mutum” ne ya zama manzo Bulus.—1 Tim. 2:7.
11. Ta yaya Kristi ta wurin ruhu mai tsarki ya faɗaɗa aikin wa’azi?
11 Domin Kristi yana son al’ummai da ba na Yahudawa ba su ji saƙon Mulki, ta hanyar ruhu mai tsarki ya ja-goranci Bulus ya yi tafiye-tafiye na wa’azi a Asiya Ƙarama da kuma Turai. Labarin Luka a cikin littafin Ayyukan Manzanni ya ce: “[Annabawa Kiristoci da malamai cikin ikilisiya da ke Suriya ta Antakiya] suna nan suna sujada ga Ubangiji, suna azumi, sai Ruhu Mai-tsarki ya ce, ku keɓe mini Barnaba da Shawulu domin aikin da na kirawo su gare shi. Sa’annan, da suka yi azumi da addu’a, suka ɗibiya masu hannuwa kuma, suka sallame su.” (A. M. 13:2, 3) Yesu ne da kansa ya kira Shawulu na Tarsus ya zama ma’aikaci ‘zaɓaɓɓe’ don ya ba da shaidar sunansa ga al’ummai; saboda haka, wannan sabuwar motsawa ta aikin wa’azi ta zo ne daga Kristi, Shugaban ikilisiya. Sanin cewa Yesu yana amfani da ruhu mai tsarki don ya ja-goranci aikin ya fita dalla-dalla a lokacin tafiyar wa’azi na biyu na Bulus. Labarin ya faɗi cewa “ruhun Yesu,” wato, Yesu ta hanyar ruhu mai tsarki ya ja-goranci Bulus da abokan tafiyarsa a zaɓin da suka yi na lokaci da kuma inda za su tafi, kuma wani wahayi ya sa su tafi cikin Turai.—Karanta Ayyukan Manzanni 16:6-10.
Shugabancin Yesu Bisa Ikilisiyarsa
12, 13. Ta yaya littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa Kristi yana lura da abin da yake faruwa a cikin kowace ikilisiya?
12 Yesu yana lura da abin da yake faruwa a cikin ikilisiyoyin mabiyansa shafaffu a ƙarni na farko K.Z. Yana sane da yanayin ruhaniya ta kowace ikilisiya. Za mu fahimci hakan sa’ad da muka karanta Ru’ya ta Yohanna sura na 2 da 3. Ya kira sunayen ikilisiyoyi bakwai, kuma duk suna Asiya Ƙarama. (R. Yoh. 1:11) Muna da dalilin gaskata cewa a lokacin yana sane da yanayin ruhaniya na sauran ikilisiyoyi na mabiyansa a duniya.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 2:23.
13 Yesu ya yaba wa wasu a cikin ikilisiyoyin domin jimrewarsu, aminci a lokacin gwaji, aminci ga kalmarsa, da kuma ƙin ’yan ridda. (R. Yoh. 2:2, 9, 13, 19; 3:8) A wata sassa, ya ba da gargaɗi sosai ga ikilisiyoyi da yawa domin ƙaunarsu a gare shi ta yi sanyi, sun ƙyale bautar gumaka da fasikanci, da kuma ɗarika. (R. Yoh. 2:4, 14, 15, 20; 3:15, 16) A matsayin mai kula na ruhaniya mai ƙauna, har ma ga waɗanda ya ba gargaɗi, Yesu ya ce: “Iyakar waɗanda na ke ƙauna, ina tsauta su ina masu horo kuma: Ka yi himma fa, ka tuba.” (R. Yoh. 3:19) Ko da yake yana sama, Yesu yana yi wa ikilisiyoyin almajiransa a duniya ja-gora ta hanyar ruhu mai tsarki. A ƙarshen saƙonsa ga waɗannan ikilisiyoyi, ya ce: “Wanda yake da kunne, bari ya ji abin da ruhu ke faɗa wa ikilisiyoyi.”—R. Yoh. 3:22.
14-16. (a) Yaya Yesu ya zama Shugaba mai gaba gaɗi na mutanen Jehobah a duniya? (b) Menene sakamakon kasancewa “tare da” almajiransa da Yesu ya yi “kullayaumi har matuƙar zamani”? (c) Menene za mu bincika a talifi na gaba?
14 Mun ga cewa Mika’ilu (Yesu) ya kasance mala’ika jarumi Shugaban Isra’ila. Daga baya, Yesu ya kasance Shugaba mai gaba gaɗi da kuma makiyayi mai ƙauna na almajiransa na farko. A lokacin da yake hidima a duniya, ya yi ja-gora a aikin wa’azi. Kuma bayan tashinsa daga matattu, ya kula da yaɗa bisharar Mulki sosai.
15 Ta wurin ruhu mai tsarki, daga baya Yesu zai faɗaɗa aikin wa’azi zuwa iyakar duniya. Kafin ya koma sama, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Za ku karɓi iko lokacin da Ruhu Mai-tsarki ya zo bisanku; za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.” (A. M. 1:8; karanta 1 Bitrus 1:12.) A ƙarƙashin ja-gorancin Kristi, an ba da shaida mai yawa a ƙarni na farko.—Kol. 1:23.
16 Amma Yesu da kansa ya nuna cewa za a ci gaba da wannan aikin har zuwa lokacin ƙarshe. Bayan ya ba mabiyansa umurni su yi wa’azi kuma su almajirantar a cikin dukan al’ummai, Yesu ya yi musu alkawari: “Ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Mat. 28:19, 20) Tun lokacin da aka ba shi ikon sarauta a shekara ta 1914, Kristi yana “tare da” almajiransa kuma yana nuna ƙwazo a matsayin Shugabansu. Za a bincika aiki mai yawa da yake yi tun shekara ta 1914 a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Don tattauna wannan annabci, ka duba babi na 11 na littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy!
Ta Hanyar Bita
• Ta yaya Ɗan Allah ya zama Shugaba mai ƙwazo a Isra’ila?
• Ta wace hanya ce Kristi yake ja-gorar ikilisiyarsa a duniya?
• Ta yaya Kristi ya ja-goranci yaɗa bishara?
• Menene ya nuna cewa Kristi yana lura da yanayi na ruhaniya na kowace ikilisiya?
[Hoton da ke shafi na 21]
“Ina aika mala’ika a gabanka”
[Hoton da ke shafi na 23]
Kamar yadda ya yi a dā, Kristi yana amfani da “kyautai ga mutane” don ya ja-goranci garkensa