Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 9/15 pp. 2-29
  • Shugabanmu Mai Ƙwazo A yau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shugabanmu Mai Ƙwazo A yau
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tsabtace Bawansa na Duniya
  • Yin Girbi a Duniya
  • Shugabancin Ikilisiyoyi
  • “Ka Zo, Ya Ubangiji Yesu”
  • Yesu ya Gama Cin Nasara
  • ‘Ga Shi, Ina Tare da Ku Kullayaumi’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • “Shugaba Ɗaya Gare Ku, Wato Almasihu”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Karɓi “Ruhu Na Gaskiya”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Sun Sami Cancantar Samun Ja-gora Zuwa Maɓulɓulan Ruwaye Na Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 9/15 pp. 2-29

Shugabanmu Mai Ƙwazo A yau

“A kan nasara ya fita, garin yin nasara kuma.”—R. YOH. 6:2.

1, 2. (a) Yaya aka kwatanta aikin sarki Kristi tun shekara ta 1914 a cikin Littafi Mai Tsarki? (b) Waɗanne abubuwa ne Kristi ya yi tun lokacin da aka naɗa shi sarki?

AN NAƊA Kristi a matsayin Sarkin Mulkin Jehobah ta hannun Almasihu a shekara ta 1914. Yaya muke ɗaukansa yanzu a idanunmu na zuci? A matsayin sarki mai tunani sosai da ke zaune a kan karagarsa, yana kallon duniya lokaci lokaci don ya ga yadda ikilisiyarsa take? Idan haka ne muke ɗaukansa, ya kamata mu canja ra’ayinmu. Zabura da littafin Ru’ya ta Yohanna sun nuna shi a matsayin sarki mai ƙwazo a kan doki, “a kan nasara ya fita, garin yin nasara kuma,” ya ci gaba da ‘nasara’ har ƙarshe.—R. Yoh. 6:2; Zab. 2:6-9; 45:1-4.

2 Abin da Kristi ya fara yi bayan ya zama sarki shi ne nasarar da ya ci bisa ‘macijin da mala’ikunsa.’ A matsayin Mika’ilu shugaban mala’iku tare da mala’ikunsa, Kristi ya jefo Shaiɗan da aljanunsa daga sammai masu tsarki zuwa duniya. (R. Yoh. 12:7-9) Sa’an nan, a matsayinsa na “mala’ikan alkawari” na Jehobah, Yesu ya zo tare da Ubansa don su bincika haikali na ruhaniya. (Mal. 3:1) Ya yi wa Kiristendom shari’a, sashe mai yawan alhaki na “Babila Babba,” kuma ya same ta da alhakin jini da ɓata kanta ta wajen saka hannu a tsarin siyasa na wannan duniyar.—R. Yoh. 18:2, 3, 24.

Tsabtace Bawansa na Duniya

3, 4. (a) Wane aiki ne Kristi ya cim ma a matsayin “mala’ikan” Jehobah? (b) Binciken haikalin ya nuna menene, kuma wane naɗi ne Yesu ya yi a matsayin Shugaban ikilisiya?

3 Binciken da Jehobah da ‘mala’ikansa’ suka yi ya kuma nuna bayyanuwar rukuni na Kiristoci na gaskiya, waɗanda ba sa cikin sashen cocin Kiristendom a farfajiya ta duniya na haikali na ruhaniya. Amma, su ma waɗannan shafaffun Kiristoci ko kuma “’ya’yan Levi,” suna bukatan a tsabtacce su. Hakan ya yi daidai da annabcin da annabi Malakai ya yi: “[Jehobah] za ya kuwa zauna kamar mai-gyaran azurfa mai-tsarkakewarta, kuma za ya tsarkake ’ya’yan Levi, yana tsabtatar da su kamar zinariya da azurfa; har su miƙa ma Ubangiji hadayu cikin adalci.” (Mal. 3:3) Jehobah ya yi amfani da “mala’ikan alkawari,” Yesu Kristi, don ya tsabtacce waɗannan Isra’ilawa na ruhaniya.

4 Har ila, Kristi ya samu waɗannan shafaffun Kiristoci masu aminci suna yin iya ƙoƙarinsu don su yi tanadin abinci na ruhaniya a lotonsa ga masu bauta wa Allah na gaskiya. Tun daga shekara ta 1879, a cikin yanayi mai kyau da marar kyau, suna wallafa gaskiyar Littafi Mai Tsarki game da Mulkin Allah a shafuffukan wannan mujallar. Yesu ya yi annabci cewa “sa’anda ya zo” don ya bincika iyalin gidansa a lokacin “cikar zamani,” zai samu wani bawa yana yi musu tanadin “abincinsu a lotonsa.” Zai yaba wa wannan bawan kuma ya “sanya shi bisa dukan abin da ya ke da shi” a duniya. (Mat. 24:3, 45-47) A matsayin Shugaban ikilisiyar Kirista, Kristi ya yi amfani da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” don ya ja-goranci abubuwa na Mulki da yake da su a duniya. Ya ba da ja-gora ga “iyalin gidansa” shafaffu da abokansu “waɗansu tumaki” ta wurin Hukumar Mulki.—Yoh. 10:16.

Yin Girbi a Duniya

5. Menene Yohanna ya ga Sarki Almasihu yake yi a cikin wahayi?

5 Manzo Yohanna ya ga wahayin wani abu kuma da Sarki Almasihu zai yi a “ranar Ubangiji,” bayan da aka naɗa shi a shekara ta 1914. Yohanna ya rubuta: “Na duba kuma, sai ga farin girgije; a bisa girgijen kuma na ga wani a zaune mai-kama da ɗan mutum, bisa kansa yana da rawani na zinariya, cikin hannunsa kuma lauje mai-ƙaifi.” (R. Yoh. 1:10; 14:14) Yohanna ya ji wani mala’ika daga Jehobah yana gaya wa wannan Mai Girbi ya miƙa laujensa domin “amfanin duniya ya wuce nuna.”—R. Yoh. 14:15, 16.

6. Menene Yesu ya ce zai faru da shigewar lokaci?

6 Wannan “amfanin duniya” ya tuna mana almarar Yesu ta alkama da zawa. Yesu ya kamanta kansa da mutumin da ya shuka irin alkama a gonarsa da ra’ayin cewa zai girbe alkama mai kyau, wanda ke wakiltar “’ya’yan mulki,” wato, Kiristoci na gaskiya da aka shafa su yi sarauta da shi a Mulkinsa. Amma, daddare, wani maƙiyi, “Iblis,” ya shuka zawa a cikin gonar, wato, “’ya’yan Mugun.” Mashukin ya umurci ma’aikatansa su bar alkamar da zawan su yi girma tare har sai lokacin kaka, a “matuƙar zamani.” A wannan lokacin, zai aika da mala’ikunsa su ware alkamar daga zawan.—Mat. 13:24-30, 36-41.

7. Yaya Kristi yake aikin girbe “amfanin duniya”?

7 A cikar wahayin da aka nuna wa Yohanna, Yesu yana aikin girbi a dukan duniya. An soma girbe “amfanin duniya” ta wurin tattara mutane 144,000 da suka rage, wato, “’ya’yan mulki,” “alkama” na almarar Yesu. An ga bambanci tsakanin Kiristoci na gaskiya da na ƙarya sosai bayan Yaƙin Duniya na ɗaya, kuma hakan ya buɗe hanya ga sashe na biyu na girbe “amfanin duniya,” wato, tattara waɗansu tumaki. Waɗannan ba “’ya’yan mulki” ba ne, amma “taro mai-girma” na talakawa masu yardan rai na Mulki. An girbe su daga cikin dukan “al’ummai, da dangogi, da harsuna.” Sun miƙa kai ga Mulkin Almasihu, da ya ƙunshi Kristi Yesu da “tsarkaka” mutane 144,000 da za su yi sarauta da shi a wannan gwamnati na samaniya.—R. Yoh. 7:9, 10; Dan. 7:13, 14, 18.

Shugabancin Ikilisiyoyi

8, 9. (a) Menene ya nuna cewa Kristi yana lura da halin dukan ikilisiyoyi da kuma salon rayuwa na waɗanda suke cikinta? (b) Kamar yadda aka nuna a shafi na 26, waɗanne “zurfafan al’amura na Shaiɗan” ya kamata mu guje wa?

8 A talifin da ya gabata mun ga yadda Kristi yake lura da yanayi na ruhaniya na kowace ikilisiya da ke ƙarni na farko A.Z. A zamaninmu, a matsayin Sarki mai sarauta da aka ba “dukan hukunci a cikin sama da ƙasa,” Kristi Shugabanmu yana nuna shugabanci da ƙwazo bisa ikilisiyoyin da ke dukan duniya da masu kula da su. (Mat. 28:18; Kol. 1:18) Jehobah “ya sanya shi kuma shi zama kai a bisa abu duka ga ikilisiya,” na shafaffu. (Afis. 1:22) Saboda haka, babu abin da yake faruwa cikin fiye da ikilisiyoyi 100,000 na Shaidun Jehobah da bai sani ba.

9 Yesu ya aika da wannan saƙo ga ikilisiya ta dā da ke Tiyatira: “Ga magana da Ɗan Allah ya faɗi, shi wanda idanunsa suna kama da harshen wuta, . . . Na san ayyukanka.” (R. Yoh. 2:18, 19) Ya tsauta wa waɗanda suke cikin wannan ikilisiya don salon rayuwarsu na lalata da yawan jin daɗi, ya gaya musu: “Ni ne mai-bimbinin zukata: kuma zan sāka ma kowane cikinku gwargwadon ayyukanku.” (R. Yoh. 2:23) Wannan kalamin ya nuna cewa Kristi yana lura da halin kowace ikilisiya da kuma salon rayuwa na mutane ɗaɗɗaya da ke cikinta. Yesu ya yaba wa Kiristoci da ke Tiyatira “waɗanda ba [su] san zurfafan al’amura na Shaiɗan ba.” (R. Yoh. 2:24) A yau, yana amincewa da waɗanda suka ƙi saka hannu a cikin “zurfafan al’amura na Shaiɗan,” matasa ko manya, ta hanyar Intane ko wasanni bidiyo na mugunta ko kuma kasancewa da halin ba komi na ’yan Adam. Yana farin cikin lura da ƙoƙarce-ƙoƙarce da sadaukarwa na Kiristoci masu yawa a yau waɗanda suke iya ƙoƙarinsu don su bi ja-gorarsa a dukan fannonin rayuwarsu!

10. Yaya aka kwatanta ja-gorar Kristi bisa dattawan ikilisiya, amma menene ya kamata su fahimta?

10 Kristi yana tanadin kulawa mai kyau ga ikilisiyoyinsa a duniya ta wurin dattawa da aka naɗa. (Afis. 4:8, 11, 12) A ƙarni na farko, dukan masu kula shafaffu ne. An nuna su a cikin Ru’ya ta Yohanna a matsayin taurari a hannun dama na Kristi. (R. Yoh. 1:16, 20) A yau, yawancin dattawan ikilisiya suna cikin waɗansu tumaki ne. An naɗa su bayan addu’a kuma a ƙarƙashin ja-gorar ruhu mai tsarki, saboda haka za a ɗauka cewa su ma Kristi ne yake musu ja-gorar. (A. M. 20:28) Amma, sun fahimci cewa Kristi yana amfani da ƙaramin rukunin maza shafaffu a matsayin Hukumar Mulki don ya ja-goranci almajiransa a duniya.—Karanta A. M. 15:6, 28-30.

“Ka Zo, Ya Ubangiji Yesu”

11. Me ya sa muke ɗokin ganin zuwan Shugabanmu da sauri?

11 A cikin wahayin da aka nuna wa manzo Yohanna, sau da yawa Yesu ya ce yana zuwa da sauri. (R. Yoh. 2:16; 3:11; 22:7, 20) Babu shakka, yana maganar zuwansa don yanke hukunci a kan Babila Babba da kuma sauran mugun zamanin Shaiɗan. (2 Tas. 1:7, 8) Da yake yana ɗokin ganin cikar dukan abubuwa masu ban al’ajabi da aka annabta, manzo Yohanna tsoho ya ce: “Amin: ka zo, ya Ubangiji Yesu.” Mu da muke zama a wannan lokaci na ƙarshe muna ɗokin ganin Shugabanmu da kuma Sarkinmu ya zo da ikon sarauta don ya tsarkake sunan Ubansa kuma ya kunita ikon mallakarsa.

12. Wane aiki ne Kristi zai gama kafin a saki iskokin halaka?

12 Kafin Yesu ya halaka ƙungiyar Shaiɗan da ake gani a duniya, waɗanda suka rage a cikin 144,000 da suke cikin Isra’ila ta ruhaniya za su karɓi hatimi na ƙarshe. Littafi Mai Tsarki ya faɗi sarai cewa ba za a saki iskokin halaka a kan zamanin Shaiɗan ba sai an gama hatimce mutane 144,000.—R. Yoh. 7:1-4.

13. Ta yaya Kristi zai sa a san ya bayyana a sashe na farko na “ƙunci mai-girma”?

13 Yawancin mutanen da suke duniya ba su lura da “dawowar” Kristi tun shekara ta 1914 ba. (2 Bit. 3:3, 4, Littafi Mai Tsarki) Amma dai, ba da daɗewa ba, zai sa a san ya bayyana ta wajen zartar da hukuncin Jehobah a kan ɓangarori dabam-dabam na zamanin Shaiɗan. Halakar “mutumin zunubi,” wato, limaman Kiristendom, zai zama “bayyanuwar zuwansa.” (Karanta 2 Tasalunikawa 2:3, 8.) Zai kasance cikakkiyar shaida da ke nuna cewa Kristi ya soma aikatawa a matsayin Alƙali da Jehobah ya naɗa. (Karanta 2 Timotawus 4:1.) Za a halaka Kiristendom, wanda shi ne sashe mafi alhaki na Babila Babba kafin a halaka muguwar daular duniya ta addinin ƙarya gabaki ɗaya. Jehobah zai saka shi cikin zukatan shugabannin ’yan siyasa su halaka wannan karuwa ta ruhaniya. (R. Yoh. 17:15-18) Wannan zai zama sashe na farko na “ƙunci mai-girma.”—Mat. 24:21.

14. (a) Me ya sa za a gajartar da sashe na farko na ƙunci mai girma? (b) Menene “alama ta Ɗan mutum” za ta nufa ga mutanen Jehobah?

14 Yesu ya faɗi cewa za a gajartar da kwanakin ƙunci mai girma “sabili da zaɓaɓu,” wato, shafaffun Kiristoci da har ila suka rage a duniya. (Mat. 24:22) Jehobah ba zai ƙyale wannan halakar addinin ƙarya ta kawar da shafaffun Kiristoci da abokanansu waɗansu tumaki ba. Yesu ya daɗa cewa “bayan ƙuncin waɗannan kwanaki” za a ga alamu a cikin rana, wata, da taurari, “sa’annan alama ta Ɗan mutum za ta bayyana a sama.” Hakan zai sa al’ummai na duniya “su yi baƙinciki.” Shafaffu da suke da begen zuwan sama da abokansu waɗanda suke da begen zama a duniya ba za su yi hakan ba. Za su ‘duba bisa, su tada kansu; gama fansarsu ta kusa.’—Mat. 24:29, 30; Luk 21:25-28.

15. Wane aiki ne Kristi zai yi sa’ad da ya zo?

15 Kafin ya gama cin nasara, har ila Ɗan mutum zai zo a wata hanya. Ya yi annabci: “Amma sa’anda Ɗan mutum za ya zo cikin darajassa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajassa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi ya kan rarraba tumaki da awaki: kuma za ya sanya tumaki ga hannun damansa, amma awaki ga hagu.” (Mat. 25:31-33) Wannan yana nuni ga zuwan Kristi a matsayin Alƙali don ya ware mutane na “dukan al’ummai” zuwa gida biyu: “tumaki,” su ne waɗanda suka goyi bayan ’yan’uwa shafaffu na ruhaniya (shafaffun Kiristoci a duniya) kuma “awaki” su ne “waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.” (2 Tas. 1:7, 8) Tumaki, waɗanda aka kira “masu-adalci” za su samu “rai na har abada” a duniya, amma awaki “za su tafi cikin hukunci na har abada,” ko halaka.—Mat. 25:34, 40, 41, 45, 46.

Yesu ya Gama Cin Nasara

16. Ta yaya Kristi Shugabanmu ya gama cin nasara?

16 Da yake an saka hatimi a kan adadin waɗanda za su yi sarauta da shi kuma an gano tumakin kuma suna hannunsa na dama don samun ceto, Kristi zai iya zuwa ya gama cin “nasara.” (R. Yoh. 5:9, 10; 6:2) A matsayin shugaba na mala’iku masu iko da kuma ’yan’uwansa da aka ta da daga matattu, zai halaka dukan siyasa, runduna, da kuma tsarin kasuwanci na Shaiɗan a duniya. (R. Yoh. 2:26, 27; 19:11-21) Kristi zai gama cin nasara sa’ad da ya halaka zamanin Shaiɗan. Sa’annan zai saka Shaiɗan da aljanu a cikin rami har tsawon shekara dubu.—R. Yoh. 20:1-3.

17. Zuwa ga menene Kristi zai yi wa waɗansu tumaki ja-gora a lokacin Sarautar Shekara Dubu, kuma menene ya kamata ya zama ƙudurinmu?

17 Sa’ad da yake maganar “taro mai-girma” na waɗansu tumaki, waɗanda za su tsira daga ƙunci mai-girma, manzo Yohanna ya yi annabci cewa “Ɗan rago wanda ke cikin tsakiyar kursiyin za ya zama makiyayinsu, za ya bishe su kuma wurin maɓulɓulan ruwaye na rai.” (R. Yoh. 7:9, 17) Hakika, a dukan lokacin Sarautarsa na Shekara Dubu, Kristi zai ci gaba da yi wa waɗansu tumaki ja-gora, waɗanda suka saurari muryarsa, kuma zai yi musu ja-gora zuwa rai na har abada. (Karanta Yohanna 10:16, 26-28.) Bari mu bi Shugabanmu da aminci, a yanzu har zuwa cikin sabuwar duniya da Jehobah ya yi alkawarinta!

Ta Hanyar Bita

• Wane mataki ne Kristi ya ɗauka bayan da aka naɗa shi sarki?

• Su wanene Kristi yake amfani da su a duniya don ya ja-goranci ikilisiyoyi?

• A waɗanne hanyoyi ne Kristi Shugabanmu zai zo?

• Ta yaya Kristi zai ci gaba da ja-gorarmu a sabuwar duniya?

[Hoton da ke shafi na 29]

Halakar mugun zamani na Shaiɗan zai sa a san cewa Kristi ya bayyana

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba