Ka Tuna?
Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka bincika ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
Shin ya dace Kiristoci su ƙona gawa a lokacin jana’iza?
Ƙona gawa a lokacin jana’iza shawara ce da mutum zai iya yi idan ya ga dama. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai yi magana kai tsaye game da ƙona gawa ba, babu shakka an ƙona gawar Sarki Saul da na ɗansa Jonathan kuma aka binne su bayan haka. (1 Sam. 31:2, 8-13)—6/15, shafi na 7.
Me ya sa muka tabbata cewa ba Allah ba ne yake haddasa munanan abubuwa?
Allah mai adalci ne a dukan ayyukansa. Shi mai aminci ne kuma mai gaskiya. Ƙari ga haka, Jehobah mai tausayi ne kuma mai jin ƙai. (K. Sha 32:4; Zab. 145:17; Yaƙ. 5:11)—7/1, shafi na 4.
Waɗanne ƙalubale ne mutum zai iya fuskanta sa’ad da ya koma wata ƙasa don hidima a inda ake bukatar masu shela sosai?
Ƙalubale uku da za su iya fuskanta su ne (1) daidaita salon rayuwa da yanayin wurin, (2) kewar gida da kuma (3) yin abokantaka da ’yan’uwa da ke yankin. Allah ya albarkaci ’yan’uwa da yawa da suka jimre da waɗannan ƙalubalen.—7/15, shafuffuka na 4-5.
Me ya sa sababbin warƙoƙi suke da kyau kuma suka kasance da sauƙi a yin wa’azi?
Dukan sababbin warƙoƙin suna da manufa ɗaya. Kowace warƙa tana ɗauke da ayar Littafi Mai Tsarki da za mu iya karanta wa mutane kuma mu yi musu tambayar da za ta ba su damar ba da amsa. Ko da wace amsa ya bayar, sai mu buɗe cikin warƙar kuma mu nuna masa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Za mu iya yi masa wata tambaya da ke warƙar kuma mu gaya masa cewa za mu dawo don mu ba da amsar.—8/15, shafuffuka na 13-14.
Mene ne iyaye Kiristoci za su yi don su kula da yaransu?
Yana da muhimmanci iyaye su riƙa sauraron ’ya’yansu don su san su da kyau. Ƙari ga haka, ya kamata su koya musu Kalmar Allah da kyau. Su ja-gorance su cikin ƙauna musamman lokacin da yaran suke shakkar abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.—9/15, shafuffuka na 18-21.
Waɗanne abubuwa ne za a kawar idan Mulkin Allah ya soma sarauta?
Rashin lafiya, mutuwa da rashin aiki da yaƙi da ƙarancin abinci da kuma talauci ba za su ƙara kasancewa ba.—11/1, shafuffuka na 6-7.
Wane alkawari ne a cikin Littafi Mai Tsarki ya ba wasu damar yin sarauta da Kristi?
Bayan Yesu ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji, ya yi wani alkawari da amintattun almajiransa, kuma wannan shi ne alkawari na Mulki. (Luk. 22:28-30) Wannan alkawarin ne ya tabbatar musu cewa za su yi sarauta tare da Yesu a sama.—10/15, shafuffuka na 16-17.
Su waye ne ‘jama’a domin sunansa’ da Yaƙub ya ambata, kamar yadda aka rubuta a Ayyukan Manzanni 15:14?
Wannan sabuwar al’umma da aka san ta da sunan Jehobah ta ƙunshi masu bi Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba da Allah ya zaɓa don su “gwada mafifitan halulluka” na wanda ya zaɓe su. (1 Bit. 2:9, 10)—11/15, shafuffuka na 24-25.