“Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
“Ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Kristi zuwa rai na har abada.”—YAHU. 21.
1, 2. Yaya Jehobah ya nuna mana ƙaunarsa, kuma yaya muka sani cewa ba ya tsare mu cikin ƙaunarsa haka kawai?
JEHOBAH ALLAH ya nuna mana ƙaunarsa a hanyoyi masu yawan gaske. Babu shakka, tabbaci mafi girma na ƙaunar da Jehobah yake yi mana ita ce tanadin fansar hadaya. Ƙaunar da Jehobah yake yi wa ’yan adam tana da girma sosai wadda hakan ta sa ya aiko ƙaunataccen Ɗansa zuwa duniya ya mutu domin mu. (Yoh. 3:16) Jehobah ya yi hakan ne domin yana son mu rayu har abada, kuma yana son mu amfana daga ƙaunarsa har abada!
2 Amma, ya kamata mu yi tsammanin cewa Jehobah zai tsare mu ne cikin ƙaunarsa ko da menene muka zaɓi mu yi? A’a. A Yahuda aya 21, an ba mu wannan shawarar: “Ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Kristi zuwa rai na har abada.” Furcin nan ‘ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah,’ yana nufin cewa muna bukatan mu ɗauki wasu matakai. To, menene muke bukatar mu yi domin mu ci gaba da kasancewa cikin ƙaunar Allah?
Ta Yaya Za Mu Kasance Cikin Ƙaunar Allah?
3. Menene Yesu ya ce yana da muhimmanci a gare shi idan yana so ya kasance cikin ƙaunar Ubansa?
3 Mun sami amsar wannan tambayar a cikin kalaman da Yesu ya faɗa a dare na ƙarshe na rayuwarsa a nan duniya. Ya ce: “Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin ƙaunata: kamar yadda na kiyaye dokokin Ubana, ina zaune kuwa cikin ƙaunatasa.” (Yoh. 15:10) Babu shakka, Yesu ya san cewa bin dokokin Jehobah yana da muhimmanci idan yana so ya ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da Ubansa. Idan Ɗan Allah, wanda kamiltacce ne ya yi hakan, dole ne mu ma mu yi hakan!
4, 5. (a) A wace hanya ce ainihi za mu iya nuna cewa muna ƙaunar Jehobah? (b) Me ya sa ba mu da wani dalili na ƙin yin biyayya ga dokokin Jehobah?
4 Ainihi, muna nuna ƙaunarmu ga Jehobah ta wajen yi masa biyayya. Manzo Yohanna ya furta batun kamar haka: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo.” (1 Yoh. 5:3) Hakika, yin biyayya ya zama tsohon yayi a wannan duniyar. Amma ka lura da furcin nan: “Dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” Jehobah bai ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba.
5 Ga misali: Za ka iya gaya wa wanda kake ƙauna ya ɗauki kayan da ka san cewa ya fi ƙarfinsa? A’a! Jehobah ya fi mu nuna alheri nesa ba kusa ba kuma ya san ƙarfinmu. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da mu cewa Jehobah yana tunawa cewa “mu turɓaya ne.” (Zab. 103:14) Ba zai taɓa ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba. Saboda haka, ba mu da wani dalilin ƙin yin biyayya ga dokokin Jehobah. Akasin haka, muna yi masa biyayya ne domin dama ce mai kyau ta nuna wa Ubanmu na samaniya cewa muna ƙaunarsa da gaske kuma muna son mu kasance cikin ƙaunarsa.
Kyauta na Musamman Daga Jehobah
6, 7. (a) Menene lamiri? (b) Ka kwatanta yadda lamiri zai taimaka mana mu kasance cikin ƙaunar Allah.
6 A cikin duniya mai wuya da muke zaune ciki, muna bukatar mu tsai da shawarwari masu yawa da suka ƙunshi biyayyarmu ga Allah. Ta yaya za mu tabbata cewa waɗannan shawarwarin sun jitu da nufin Allah? Jehobah ya ba mu kyautar da za ta taimaka mana sosai a wannan batu na biyayya. Lamiri ne. Menene lamiri? Wani abu ne na musamman da ke sa mu bincika kanmu. Yana aikatawa ne kamar alƙali a cikinmu, da ke sa mu bincika zaɓen da za mu yi a rayuwa ko kuma mu yi tunani a kan matakan da muka riga muka ɗauka kuma mu bincika ko suna da kyau ko ba su da kyau.—Karanta Romawa 2:14, 15.
7 Ta yaya za mu iya yin amfani da lamirinmu yadda ya dace? Ka yi la’akari da wannan misalin. A ce za ka wani wuri da ba ka sani ba. Amma kana tare da wani wanda ka amince da shi kuma wanda ya san wurin sosai. Shi ne zai yi maka ja-gora. Idan ka bi umurninsa, ba za ka ɓace ba. Hakazalika, mutumin da bai da lamiri zai ɓace nan da nan sa’ad da yake son ya yi zaɓi a rayuwa game da ɗabi’a, yin abin da ya dace, da kuma aminci.
8, 9. (a) Wace kasawa ta lamirinmu ne muke bukatar mu riƙa tunawa? (b) Menene za mu iya yi don mu tabbata cewa lamirinmu zai amfane mu sosai?
8 Kamar mutumin nan mai ja-gora, lamiri yana da kasawarsa. Idan muka ƙi bin shawarar mutumin nan za mu iya ɓata. Hakazalika, idan muka fi mai da hankali ga muradin zuciyarmu, menene zai faru? Muradinmu na son kai na iya ɓata lamirinmu. Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa “zuciya ta fi komi rikici, cuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya.” (Irm. 17:9; Mis. 4:23) Bugu da ƙari, idan mutumin nan mai ja-gora da muka ambata a cikin misali ya rikice, zai iya ɓatar da mu. Kuma idan muka yi musu da shi, muka ƙi ja-gorarsa, muka bi hanyar da muke tsammanin ita ce daidai, za mu iya ɓata. Hakazalika, idan muka ƙi dogara da tabbatacciyar ja-gorar da ke cikin Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, lamirinmu zai iya kasancewa marar amfani. (Zab. 119:105) Abin baƙin ciki, mutane da yawa a wannan duniyar sun fi mai da hankali ga muradin zuciyarsu fiye da ƙa’idodin da aka tsara a cikin Kalmar Allah. (Karanta Afisawa 4:17-19.) Shi ya sa mutane da yawa suke yin mugayen abubuwa, duk da cewa suna da lamiri.—1 Tim. 4:2.
9 Ya kamata mu ƙudurta cewa ba za mu kasance kamar su ba! Maimakon haka, bari mu ci gaba da ƙyale Kalmar Allah ta ilimantar da lamirinmu kuma ta koyar da shi domin ya amfane mu sosai. Kuma muna bukatan mu bi lamirinmu da aka koyar da Littafi Mai Tsarki, maimakon mu ƙyale muradinmu na son kai ya sha kan shi. Kuma, ya kamata mu yi ƙoƙari mu daraja lamirin ’yan’uwanmu ƙaunatattu na ruhaniya. Muna iya ƙoƙarinmu don kada mu sa su yi tuntuɓe ta wajen tuna cewa lamirin ’yan’uwanmu yana iya ƙin abin da na mu ke so.—1 Kor. 8:12; 2 Kor. 4:2; 1 Bit. 3:16.
10. Waɗanne wurare uku na rayuwa ne za mu tattauna yanzu?
10 Bari yanzu mu tattauna wurare uku na rayuwa da za mu iya nuna ƙaunarmu ga Jehobah ta wajen yin biyayya. A kowannensu, za a ambata lamiri, amma da farko, ana bukatan a yi masa ja-gora da hurarrun mizanai na ɗabi’a da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Hanyoyi uku da muke yi wa Jehobah biyayya cikin ƙauna su ne: (1) Mu ƙaunaci waɗanda Jehobah yake ƙauna; (2) mu daraja waɗanda suke da iko; kuma na (3) mu yi iya ƙoƙarinmu mu kasance da tsabta a gaban Allah.
Ka Ƙaunaci Waɗanda Jehobah Yake Ƙauna
11. Me ya sa ya kamata mu ƙaunaci waɗanda Jehobah yake ƙauna?
11 Na farko, dole mu ƙaunaci waɗanda Jehobah yake ƙauna. Mutane kamar soso suke idan ya zo ga batun tarayya. Muna tsotse dukan wani abin da ke inda muke. Mahaliccinmu ya san haɗari da kuma taimakon tarayya ga mutane ajizai. Saboda haka, ya ba mu wannan shawarar mai kyau: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.” (Mis. 13:20; 1 Kor. 15:33) Babu wani a cikinmu da ke son ya “cutu.” Kowannenmu yana son ya zama mai “hikima.” Babu wanda zai iya daɗa wa Jehobah hikima, kuma babu wanda zai iya ɓata shi. Duk da haka, ya kafa mana misali mai kyau game da tarayya. Kun tuna mutane ajizai da Jehobah ya zaɓa su zama abokansa?
12. Waɗanne irin abokai ne Jehobah yake zaɓa?
12 Jehobah ya kira Ibrahim uban iyali “abokina.” (Ish 41:8, Littafi Mai Tsarki) Wannan mutumin ya yi fice wajen aminci, adalci da kuma biyayya, mutumi ne mai bangaskiya. (Yaƙ. 2:21-23) Irin abokin da Jehobah ya zaɓa ke nan. Kuma irin su ne yake abota da su a yau. Idan Jehobah ya zaɓi irin waɗannan abokan, yana da muhimmanci mu ma mu zaɓi abokan kirki, mu yi tafiya da mutane masu hikima don mu yi hikima.
13. Idan ya zo ga zaɓan abokai, menene zai taimake mu mu yi zaɓi mai kyau?
13 Menene zai taimake ka ka zaɓi abokan kirki? Yin nazari a kan misalan da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai iya motsa ka. Ka yi la’akari da abutar da ke tsakanin Ruth da surukarta Naomi, Dauda da Jonathan, ko kuwa Timotawus da Bulus. (Ruth 1:16, 17; 1 Sam. 23:16-18; Filib. 2:19-22) Mutanen nan sun zama abokai na kud da kud musamman domin dalili ɗaya: Kowannensu yana ƙaunar Jehobah sosai. Za ka iya samun abokai da ke ƙaunar Jehobah kamar ka? Ka sani cewa ikilisiyar Kirista tana cike da irin waɗannan abokan. Irin waɗannan abokan ba za su tura ka ka yi abin da zai ɓata wa Jehobah rai ba. Maimakon haka, za su taimaka maka ka yi biyayya ga Jehobah, ka girma a ruhaniya, kuma ka yi shuka bisa ga ruhu. (Karanta Galatiyawa 6:7, 8.) Za su taimake ka ka tsare kanka cikin ƙaunar Allah.
Ka Girmama Hukuma
14. Waɗanne abubuwa ne suke sa girmama hukuma yake yi mana wuya a yawancin lokaci?
14 Hanya ta biyu da muke nuna ƙaunarmu ga Jehobah ta shafi hukuma. Dole ne mu girmama hukuma. Me ya sa girmama hukuma yake yi mana wuya a wasu lokatai? Dalili guda shi ne, mutane masu iko ajizai ne. Ƙari ga hakan, mu ma ajizai ne. Muna kokawa da muradin yin tawaye.
15, 16. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu girmama waɗanda Jehobah ya ɗanka wa hakkin kula da mutanensa? (b) Wane darassi mai kyau ne muka koya daga yadda Jehobah ya ɗauki tawayen da Isra’ilawa suka yi wa Musa?
15 Kana iya cewa, ‘Idan daraja hukuma yana yi mana wuya, me ya sa muke bukatan mu yi hakan?’ Amsar ta shafi ikon mallaka. Wanene za ka zaɓa ya zama mamallakinka, wanda zai yi sarauta a kan ka? Idan muka zaɓi Jehobah ya zama Mamallakinmu, muna bukatar mu daraja ikonsa. Idan ba mu yi hakan ba, za mu iya kiransa Mamallakinmu da gaske? Bugu da ƙari, Jehobah yana yi mana ja-gora ne ta hanyar mutane ajizai da ya ba hakkin kula da mutanensa. Idan muka yi tawaye ga waɗannan mutanen, yaya ne Jehobah zai ɗauki halayenmu?—Karanta 1 Tasalonikawa 5:12, 13.
16 Alal misali, sa’ad da Isra’ilawa suka yi gunaguni da tawaye ga Musa, Jehobah ya ɗauki abin da suka yi kamar shi ne suka yi wa. (Lit. Lis. 14:26, 27) Allah bai canja ba. Idan muka yi tawaye ga mutanen da ya ba iko, hakan zai nuna cewa shi ne muke yi wa tawaye!
17. Wane hali mai kyau ne ya kamata mu yi ƙoƙari mu nuna ga waɗanda suke da iko cikin ikilisiya?
17 Manzo Bulus ya bayyana irin hali mai kyau da ya kamata mu nuna ga waɗanda suke da iko a ikilisiyar Kirista. Ya rubuta: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabanninku, ku sarayar da kanku gare su: gama suna yin tsaro sabili da rayukanku, kamar waɗanda za su amsa tambaya; su yi shi da farinciki, ba da baƙinciki ba: gama wannan marar-anfani ne gare ku.” (Ibran. 13:17) Hakika, muna bukatar mu yi aiki tuƙuru don mu yi biyayya da kuma miƙa kai. Ka tuna cewa, muna aiki ne don mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah. Wannan makasudin kwalliya ce da za ta biya kuɗin sabulu, ko ba haka ba?
Ka Kasance da Tsabta a Gaban Jehobah
18. Me ya sa Jehobah yake son mu kasance da tsabta?
18 Hanya ta uku da za mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah ita ce ta wajen yin iya ƙoƙarin mu mu kasance da tsabta a gaban Jehobah. Iyaye suna aiki tuƙuru don su tabbata cewa ’ya’yansu sun kasance da tsabta. Me ya sa? Dalili guda shi ne, kasancewa da tsabta zai sa yaron ya kasance da koshin lafiya. Bugu da ƙari, yaro mai tsabta zai sa a daraja iyalin, domin hakan zai bayyana ƙauna da kulawa da iyayen ke nunawa. Domin irin waɗannan dalilan, Jehobah yana son mu kasance da tsabta. Ya san cewa kasancewa da tsabta yana da muhimmanci idan muna son mu kasance da lafiya. Ya san cewa tsabtarmu tana shafansa, a matsayinsa na Ubanmu na samaniya. Hakan yana da muhimmanci sosai, mutane suna iya kusantar Allahn da muke bauta wa domin sun lura cewa mun fita dabam daga mutanen da ke cikin wannan lalatacciyar duniyar.
19. Ta yaya muka san cewa tsabta na zahiri tana da muhimmanci?
19 A waɗanne hanyoyi ne muke bukatar mu kasance da tsabta? A dukan fasaloli na rayuwarmu. A Isra’ila ta dā, Jehobah ya bayyana wa mutanensa dalla-dalla cewa dole ne su kasance da tsabta ta jiki. (Lev. 15:31) Dokar Musa ta kafa dokoki game da batutuwa kamar su yin bayan gida, wanke kwanoni, da kuma wanke hannuwa, ƙafafuwa da sitira. (Fit. 30:17-21; Lev. 11:32; Lit. Lis. 19:17-20; K. Sha 23:13, 14) An tuna wa Isra’ilawa cewa Allahnsu, Jehobah, yana da “tsarki,” kuma hakan na nufin cewa yana da tsabta. Bayin Allah mai tsarki suna bukatar su kasance da tsarki.—Karanta Levitikus 11:44, 45.
20. A waɗanne hanyoyi ne muke bukatan mu kasance da tsabta?
20 Saboda haka, muna bukatan mu kasance da tsarki a ciki da waje. Muna bukatar mu yi tunanin abubuwa masu kyau. Muna bukatan mu manne wa mizanan Jehobah game da ɗabi’a, duk da lalatar da ta zama ruwan dare a duniyar da muke ciki. Mafi muhimmanci, muna bukatan mu nace wa tsabtace bautarmu, ta wajen guje wa duk wata gurɓatarwa daga addinin ƙarya. Kada mu mance hurarren gargaɗin da ke rubuce a Ishaya 52:11: “Ku tashi, ku tashi, ku fita daga can, kada ku taɓa wani abu mai-ƙazamta; ku fita daga cikin tsakiyarta; ku tsarkaka.” A yau, muna kasancewa da tsabta a ruhaniya ta wajen guje wa duk wani abin da ya shafi addinin ƙarya. Alal misali, shi ya sa ba ma yin bukukuwa na addinan ƙarya da suka zama ruwan dare a duniya a yau. Hakika, kasancewa da tsabta zai iya zama ƙalubale. Amma mutanen Jehobah suna yin ƙoƙari su kasance hakan, domin wannan yana taimaka musu su tsare kansu a cikin ƙaunar Allah.
21. Ta yaya za mu iya tabbata cewa za mu kasance cikin ƙaunar Allah?
21 Jehobah yana son mu kasance cikin ƙaunarsa har abada. Amma kowannenmu yana bukatar ya tabbata cewa yana iya ƙoƙarinsa don ya kasance cikin ƙaunar Allah. Za mu yi hakan ta wajen bin misalin Yesu da kuma nuna cewa muna ƙaunar Jehobah ta wajen yin biyayya da dokokinsa. Idan muka yi hakan, za mu kasance da tabbaci cewa babu abin da zai “iya raba mu da ƙaunar Allah, wadda ke cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.”—Rom. 8:38, 39.
Ka Tuna?
• Ta yaya lamirinmu zai taimake mu mu kasance cikin ƙaunar Allah?
• Me ya sa muke bukatan mu ƙaunaci waɗanda Jehobah yake ƙauna?
• Me ya sa girmama hukuma yake da muhimmanci?
• Me ya sa tsabta yake da muhimmanci ga mutanen Allah?
[Hotunan da ke shafi na 18]
“Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin ƙaunata: kamar yadda na kiyaye dokokin Ubana, ina zaune kuwa cikin ƙaunatasa”