Tambayoyi Daga Masu Karatu
Akwai begen tashi daga matattu ga jaririn da ya mutu a cikin mahaifar mamar shi?
Waɗanda ba su taɓa shaida hakan ba, ba za su fahimci irin baƙin cikin da waɗanda suka yi hakan suke yi ba. Wasu iyaye suna yin baƙin ciki sosai domin irin wannan rashin. Wata mata ta yi ɓarin ciki sau biyar. Daga baya, ta yi farin cikin samun ’ya’ya maza guda biyu masu ƙoshin lafiya. Duk da haka, tana tuna dukan ɓarin cikin da ta yi. Har ƙarshen rayuwarta, tana tunanin shekarun yaran da a ce ba ta yi ɓarin su ba. Waɗannan Kiristoci suna da bege cewa za a ta da yaran da suka yi ɓari daga matattu?
Amsar ita ce, ba mu sani ba. Littafi Mai Tsarki bai taɓa ambata batun tashin matattu na jarirai da aka yi ɓarin cikinsu ba. Duk da haka, Kalmar Allah tana ɗauke da ƙa’idodin da suka shafi wannan tambayar kuma za su ba da bege.
Bari mu tattauna tambayoyi guda biyu. Na farko, a gaban Jehobah, a wane lokaci ne rayuwar mutum take farawa, sa’ad da aka ɗauki cikinsa ne ko kuma sa’ad da aka haife shi? Na biyu, yaya Jehobah yake ɗaukan jaririn da ke cikin ciki, a matsayin cikakken mutum ne ko kuma ƙwayoyin halitta a cikin mace? Mizanan da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun ba da amsoshi masu kyau ga waɗannan tambayoyin.
Dokar Musa ta bayyana cewa rayuwa tana somawa ne tun daga ciki. Kamar yaya? Dokar ta nuna cewa za a iya kashe duk wanda ya kashe ɗan tayi. Dokar ta ce: “Za ka bada rai don rai.”a (Fit. 21:22, 23) Saboda haka, jaririn da ke cikin ciki yana da rai kuma mutum ne. Sanin wannan gaskiyar ya taimaka wa miliyoyin Kiristoci su guje wa zubar da ciki, domin mugun zunubi ne a gaban Allah.
Ko da yake jaririn da ke ciki yana da rai, amma yaya Jehobah yake ɗaukan wannan ran? Dokar da aka ambata a baya ta ce a kashe mutumin da ya jawo mutuwar jaririn da ke cikin ciki. Hakika, rayuwar jaririn da ke cikin ciki tana da muhimmanci sosai a wajen Allah. Bugu da ƙari, Nassosi da yawa sun nuna cewa Jehobah yana ɗaukan jaririn da ke cikin ciki a matsayin mutum mai rai. Alal misali, an hure Sarki Dauda ya ce game da Jehobah: “Ka harhaɗa ni cikin cikin uwata . . . Idanunka sun ga gaɓaɓuwan jikina tun ba su cika ba, a cikin littafinka an rubuta dukansu, waɗanda ake sifantarsu yau da gobe.”—Zab. 139:13-16; Ayu. 31:14, 15.
Jehobah ya ga cewa jarirai da ke cikin ciki suna da halaye dabam dabam kuma za su iya zama babban mutum a nan gaba. Sa’ad da Rifkatu matar Ishaƙu take da cikin tagwaye, Jehobah ya yi annabci game da yara biyun da suke gwagwagwa a cikin mahaifarta, a haka yana nufin cewa ya riga ya ga wasu halaye a cikin su da za su shafi mutane a nan gaba.—Far. 25:22, 23; Rom. 9:10-13.
Wani al’amari mai ban sha’awa shi ne na Yohanna mai baftisma. Labarin da ke cikin Linjila ya ce: “Sa’anda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, jariri ya zabura a cikin cikinta. Alisabatu ta cika da Ruhu Mai-tsarki.” (Luk 1:41) Sa’ad da yake kwatanta wannan yanayin, likita Luka ya yi amfani da kalmar Helenanci da take nufin tayi ko kuma jariri bayan an haife shi. Ya yi amfani da wannan kalmar sa’ad da yake maganar jariri Yesu sa’ad da yake kwance a kan sakarkari.—Luk 2:12, 16; 18:15.
Ta wajen yin la’akari da dukan waɗannan batutuwa da kuma nassosi, Littafi Mai Tsarki ya bambanta jaririn da ke cikin ciki da kuma wanda aka haifa? Bai yi hakan ba. Kuma hakan ya jitu da binciken kimiyya na zamani. Alal misali, masu bincike sun gano cewa jaririn da ke cikin ciki yana jin abin da ke faruwa a waje kuma ya aikata bisa ga hakan. Shi ya sa mata mai ciki take ƙulla gami na kud da kud da jaririn da ke cikin cikinta.
Ana haifan jarirai bayan lokaci dabam dabam da suke girma a ciki. Yi la’akari da wannan misalin: Wata uwa ta haifi bakwaini, amma ya mutu bayan ’yan kwanaki. Wata uwa kuma jaririnta ya kai wata tara a ciki, amma jaririn ya mutu ana gab da haihuwarsa. Uwa ta farko tana da bege ne cewa za a ta da jaririnta daga matattu domin an haifi shi bakwaini, yayin da uwa ta biyu ba ta da irin wannan begen?
A taƙaice, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa rai yana somawa ne sa’ad da mace ta ɗauki ciki kuma Jehobah yana ɗaukan ɗan tayi da matsayin mutum mai tamani. Bisa ga waɗannan gaskiya da ke cikin Nassi, wasu suna ganin cewa ba daidai ba ne a ce jaririn da ba a haifa da ya mutu bai da begen tashi daga matattu. Hakika, suna iya ganin cewa hakan zai sa a yi shakkar mizananmu na Nassi game da zubar da ciki, wanda yake bisa waɗannan koyarwa na gaskiya.
A dā, wannan mujallar ta yi wasu tambayoyi game da yadda za a ta da jarirai da suka mutu kafin a haife su daga matattu, kuma waɗannan tambayoyi sun sa ana shakkar irin wannan tashin matattu. Alal misali, Allah zai saka ɗan tayi ne a cikin mahaifar mace ne a Aljanna? Amma, ƙarin nazari, bimbini da addu’a sun sa Hukumar Mulki ta kammala cewa waɗannan abubuwa ba su da muhimmanci idan ya zo ga begen tashin matattu. Yesu ya ce: “Ga Allah abu duka ya yiwu.” (Mar. 10:27) Abin da ya faru ga Yesu ya nuna gaskiyar wannan furcin, an turo ransa daga sama zuwa cikin mahaifar budurwa, hakika, ga mutum hakan ba zai yiwu ba.
Dukan waɗannan suna nufin Littafi Mai Tsarki ya koyar ne cewa za a ta da yara da suka mutu kafin a haife su daga matattu? Dole ne mu nanata cewa Littafi Mai Tsarki bai amsa wannan tambayar kai tsaye ba, saboda haka ba tushen da zai sa ’yan adam su nace cewa za a ta da su daga matattu. Wannan batun zai iya ta da tambayoyi masu yawa. Ya fi kyau a guji yin hasashe. Abin da muka sani shi ne: Jehobah Allah, wanda yake cike da juyayi da alheri ne ya san yadda zai bi da batun. (Zab. 86:15) Babu shakka, yana son ya kawar da mutuwa ta wajen tashin matattu. (Ayu. 14:14, 15) Muna da tabbaci cewa yana yin abin da ya dace a kowane lokaci. Zai warkar da raunin da rayuwa a wannan mugun zamani ya jawo, sa’ad da ya ja-goranci Ɗansa ya “halaka ayyukan Shaiɗan.”—1 Yoh. 3:8.
[Hasiya]
a A wani lokaci ana fassara wannan nassin a hanyar da ke nuna cewa mutuwar uwar ce kawai za ta jawo hukunci na mutuwa. Amma, kalmar Ibrananci ta ainihi ta nuna cewa dokar tana nufin hatsarin da ya kai ga mutuwar uwar ko jaririn da ke cikinta.
[Hotunan da ke shafi na 13]
Jehobah zai kawar da dukan abubuwa masu ban ciwo