Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 4/15 pp. 7-11
  • Amincinka Yana Sa Jehobah Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amincinka Yana Sa Jehobah Farin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kada Ka Mance Ainihin Maƙiyin
  • Ka Ƙulla Dangantaka na Kud da Kud da Jehobah
  • Jehobah Yana Tallafa wa Bayinsa Masu Aminci
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • “Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Ka Rike Amincinka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 4/15 pp. 7-11

Amincinka Yana Sa Jehobah Farin Ciki

“Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.”—MIS. 27:11.

1, 2. (a) Wane ƙalubale na Shaiɗan ne Littafin Ayuba ya kwatanta? (b) Menene ya nuna cewa Shaiɗan ya ci gaba da ƙalubalantar Jehobah bayan zamanin Ayuba?

JEHOBAH ya ƙyale Shaiɗan ya jarraba amincin bawansa, Ayuba. A sakamakon haka, Ayuba ya rasa dabbobinsa, ’ya’yansa, da kuma lafiyarsa. Amma sa’ad da Shaiɗan ya ƙalubanci amincin Ayuba, ba Ayuba kaɗai ya ƙalubalanta ba. Shaiɗan ya ce: “Ai, fata a bakin fata, hakika dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” Ban da Ayuba, wannan ƙalubalen ya jawo zancen da ya shafi wasu, kuma shekaru da yawa bayan mutuwar Ayuba, Shaiɗan ya ci gaba da ƙalubalantar amincin mutane.—Ayu. 2:4.

2 Shekara 600 bayan jarabobbin Ayuba, Jehobah ya hure Sulemanu ya rubuta: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” (Mis. 27:11) Babu shakka, a wannan lokacin, Shaiɗan ya ƙalubalanci Jehobah. Bugu da ƙari, a wahayin da aka ba manzo Yohanna, ya ga Shaiɗan yana ƙalubalantar bayin Allah bayan da aka jefo shi daga sama bayan da aka kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914. Hakika, a yau ma, a ƙarshen wannan zamanin, Shaiɗan yana ƙalubalantar amincin bayin Allah!—R. Yoh 12:10.

3. Wane darassi ne muka koya daga littafin Ayuba?

3 Ka yi la’akari da darussa guda uku da muka koya daga littafin Ayuba. Na farko, jarrabobin Ayuba ya nuna ainihin abokin gaban ’yan adam da kuma mai hamayya da mutanen Allah. Wannan maƙiyin shi ne Shaiɗan Iblis. Na biyu, idan muna da dangantaka na kud da kud da Allah, hakan zai sa mu riƙe amincinmu a duk wata jarrabar da muka fuskanta. Na uku, sa’ad da muka fuskanci jarrabobi kuma aka gwada mu, Allah yana taimaka mana kamar yadda ya taimaka wa Ayuba. A yau, Jehobah yana yin hakan ta hanyar Kalmarsa, ta hanyar ƙungiyarsa, da kuma ruhunsa mai tsarki.

Kada Ka Mance Ainihin Maƙiyin

4. Wanene za a ɗora wa laifin yanayin duniya a yau?

4 Yawanci ba su yarda ba cewa akwai Shaiɗan. Da hakan, ko da suna a faɗake game da yanayin duniya, ba su san ainihin mai jawo su ba, wato, Shaiɗan Iblis. Hakika, ’yan adam ne suke jawo yawancin matsalolin da suke fuskanta. Iyayenmu na farko, Adamu da Hauwa’u, sun ’yanta kansu daga Mahaliccinsu. Kuma tun lokacin, mutane da yawa sun bi halinsu. Duk da haka, Iblis ne ya ruɗi Hauwa’u kuma ta yi tawaye ga Allah. Shi ne ya tsara yanayin duniya wanda ’yan adam ajizi suke ciki. Domin Shaiɗan shi ne “allah na wannan zamani,” mutane suna nuna ainihin irin halayensa kamar su, girman kai, masifa, kishi, son kai, ruɗi, da kuma tawaye. (2 Kor. 4:4; 1Ti 2:14; 3:6; karanta Yaƙub 3:14, 15.) Irin Waɗannan halayen sun jawo rikici, ƙiyayya, haɗama, da hargitsi na siyasa da addini, kuma hakan na ƙara bala’in da ’yan Adam suke fuskanta.

5. Menene muke son mu yi da wannan sani mai tamani da muke da shi?

5 Mu bayin Jehobah muna da sani mai tamani game da shi! Hakika, mun san wanda ke da alhakin yanayin duniya wadda ke ci gaba da taɓarɓarewa. Hakan ya motsa mu mu saka hannu a hidimar fage don mu gaya wa mutane ainihin ko wanene maƙiyinsu, ko ba haka ba? Kuma muna farin cikin kasancewa a gefen Allah na gaskiya, Jehobah, mu kuma yi wa mutane bayani game da yadda zai kawar da Shaiɗan da duk wahalolin ’yan adama, ko ba haka ba?

6, 7. (a) Wanene yake sa a tsananta wa masu bauta ta gaskiya? (b) Ta yaya za mu yi koyi da misalin Elihu na zamanin dā?

6 Shaiɗan ne ke da alhakin matsaloli da yawa da ake fuskanta a duniya kuma shi ne ke jawo hamayyar da mutanen Allah suke fuskanta. Ya ƙudurta cewa zai gwada mu. Yesu Kristi ya gaya wa manzo Bitrus: “Siman, Siman, ga Shaiɗan ya roƙa ya same ku, domin shi rairaye ku kamar alkama.” (Luk. 22:31) Hakazalika, kowannenmu da ke bin tafarkin Yesu zai fuskanci gwaji ko yaya. Bitrus ya kwatanta Iblis da “zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” Kuma Bulus ya ce: “Dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.”—1 Bit. 5:8; 2 Tim. 3:12.

7 Sa’ad da bala’i ya faɗa wa ɗan’uwa mai bi, ta yaya za mu nuna cewa mun san ainihin maƙiyin? Maimakon mu guji ɗan’uwan da abin ya shafa, ya kamata mu yi kamar Elihu na zamanin dā, wanda ya tattauna da Ayuba kamar abokin gaske. Ya kamata mu tallafa wa ɗan’uwanmu a famar da yake yi da magabcin dukanmu, Shaiɗan. (Mis. 3:27; 1 Tas. 5:25) Makasudinmu shi ne mu taimaka wa ɗan’uwanmu ya riƙe amincinsa, ko ta yaya, don ya faranta wa Jehobah rai.

8. Me ya sa Shaiɗan bai yi nasara ba wajen hana Ayuba daraja Jehobah?

8 Dukiya na farko da Shaiɗan ya sa Ayuba ya rasa shi ne dabbobinsa. Waɗannan dabbobin suna da daraja gare shi, domin wataƙila ta nan ne yake samun abinci da sha. Kuma yana yin amfani da su wajen bauta. Bayan Ayuba ya tsarkake ’ya’yansa, “yana sammako da sassafe, yana yin hadayu na ƙonawa domin ƙowane ɗayansu: gama Ayuba ya ce, Watakila ’ya’yana sun yi zunubi, sun yi saɓon Allah a zuciyarsu. Ayuba ya kan yi hakanan babu fāsawa.” (Ayu. 1:4, 5) Da haka, Ayuba yana yin hadayun dabbobi ga Jehobah babu fasawa. Sa’ad da gwajin ya soma, hakan bai yiwu ba kuma. Ayuba ba shi da “wadata” wadda zai daraja Jehobah da ita. (Mis. 3:9) Amma ya ɗaukaka Jehobah da bakinsa!

Ka Ƙulla Dangantaka na Kud da Kud da Jehobah

9. Menene abin da ya fi tamani a rayuwarmu?

9 Ko mu mawadaci ne ko talaka, matashi ko tsoho, mai lafiya ko marar lafiya, muna iya ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. Ko da wane irin jarraba ne muke fuskanta, kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah zai taimaka mana mu riƙe amincinmu kuma mu faranta zuciyar Jehobah. Wasu ma da ba su da cikakken ilimi na gaskiya, sun kasance da gaba gaɗi kuma sun riƙe amincinsu.

10, 11. (a) Menene wata ’yar’uwa ta yi sa’ad da aka jarraba amincinta? (b) Ta yaya wannan ’yar’uwar ta ƙaryata Shaiɗan?

10 Yi la’akari da misalin ’Yar’uwa Valentina Garnovskaya, wadda tana ɗaya daga cikin Shaidu masu yawa da suka riƙe amincinsu kamar Ayuba duk da gwaji masu tsanani da suka fuskanta. A shekara ta 1945, sa’ad da take ’yar shekara 20, wani ɗan’uwa ya yi mata wa’azi. Ya sake komowa sau biyu don ya tattauna Littafi Mai Tsarki da ita, amma bayan haka, ba ta sake ganin shi ba. Duk da haka, Valentina ta soma yi wa maƙwabtanta wa’azi. A sakamakon haka, aka kama ta aka saka ta cikin kurkuku na tsawon shekara takwas. An sake ta a shekara ta 1953, kuma nan da nan ta soma yin wa’azi. Aka sake kama ta kuma aka saka ta a kurkuku, a wannan karon na shekara goma. Bayan ta yi shekaru masu yawa a kurkuku guda, sai aka sake kai ta wani. A wannan kurkukun, akwai wasu ’yan’uwa mata da suke da Littafi Mai Tsarki. Wata rana, wata ’yar’uwa ta nuna wa Valentina Littafi Mai Tsarkin. Wannan abun farin cikin ne sosai! Kafin wannan lokacin, Littafi Mai Tsarki da Valentina ta taɓa gani shi ne wanda ɗan’uwan nan ya yi amfani da shi sa’ad da ya yi mata wa’azi a 1945!

11 A shekara ta 1967, an saki Valentina kuma ta sami zarafin keɓe rayuwarta ga Jehobah ta hanyar yin baftisma. Ta yi amfani da ’yancin da ta samu wajen saka hannu a hidimar fage har shekara ta 1969. A wannan shekarar ce aka sake kama ta, kuma aka jefa ta kurkuku har tsawon shekara uku. Duk da haka, Valentina ta ci gaba da yin wa’azi. Kafin ta rasu a shekara ta 2001, ta taimaka wa mutane 44 su koyi gaskiya. Kuma ta yi shekara 21 a gidan kurkuku da sansani dabam-dabam. Da son rai, ta sadaukar da komi har da ’yancinta, don ta riƙe amincinta. A ƙarshen rayuwarta, Valentina ta ce: “Ban taɓa samun gidan kaina ba. Dukan abin da na mallaka suna cikin jaka guda kawai, amma na sami farin ciki da gamsuwa wajen bauta wa Jehobah.” Hakika, Valentina ta ƙaryata Shaiɗan, wanda ya yi da’awa cewa ’yan adam ba za su kasance da aminci ga Allah ba a lokacin jarraba! (Ayu. 1:9-11) Mun tabbata cewa ta faranta zuciyar Jehobah kuma yana jiran lokacin da zai tayar da Valentina tare da duk waɗanda suka mutu da aminci daga matattu.—Ayu. 14:15.

12. Menene matsayin ƙauna a dangantakarmu da Jehobah?

12 Muna dangantaka da Jehobah ne domin muna ƙaunarsa. Muna son halayen Allah kuma muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi rayuwar da ta jitu da manufofinsa. Akasin abin da Shaiɗan ya faɗa, muna ƙaunar Jehobah ne da son rai ba tare da samun wani abu ba. Wannan ƙaunar tana ƙarfafa mu mu riƙe amincinmu a lokacin gwaji. A nasa ɓangaren, Jehobah zai “kiyaye tafarkin tsarkakansa.”—Mis. 2:8; Zab. 97:10.

13. Yaya Jehobah yake ganin abubuwan da muka yi domin sa?

13 Ƙauna tana motsa mu mu ɗaukaka sunan Jehobah, ko da ba mu da zarafi sosai. Yana ganin muradinmu mai kyau kuma ba ya hukunta mu idan mun ƙasa yin duk abin da muke son mu yi. Abin da muka yi da kuma dalilin da ya sa muka yi shi yana da muhimmanci sosai a gare shi. Ko da yake Ayuba ya yi baƙin ciki kuma jimre abubuwa masu yawa, ya gaya wa waɗanda suke zarginsa game da yadda yake ƙaunar dokokin Jehobah. (Karanta Ayuba 10:12; 28:28.) A sura ta ƙarshe a littafin Ayuba, Jehobah ya nuna fushinsa ga Eliphaz, Bildad, da Zophar domin ba su faɗi gaskiya ba. A lokacin kuma, Jehobah ya nuna amincewarsa ga Ayuba don ya kira shi “bawana” sau huɗu kuma ya ce ya yi wa waɗanda suka yi zunubi addu’a. (Ayu. 42:7-9) Bari mu ci gaba da yin abin da zai sa Jehobah ya dube mu da tagomashi.

Jehobah Yana Tallafa wa Bayinsa Masu Aminci

14. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Ayuba ya daidaita tunaninsa?

14 Ayuba ya riƙe amincinsa duk da cewa shi ajizi ne. A wasu lokatai, sa’ad da yake fuskantar matsi sosai, bai yi tunanin da ya dace ba. Alal misali, ya ce wa Jehobah: “Ina yi maka kuka, ba ka amsa mani ba . . . Da ƙarfin hannunka kana tsananta mani.” Bugu da ƙari, Ayuba ya mai da hankali sosai ga nuna cewa bai da laifi sa’ad da ya ce: “Ba ni da mugunta” da kuma “ba aikin zilama a hannuwana ba, addu’ata kuma da tsabta.” (Ayu. 10:7; 16:17; 30:20, 21) Duk da haka, cikin tausayi Jehobah ya taimaka wa Ayuba ta wajen yi masa jerin tambayoyin. Tambayoyin sun taimaka wa Ayuba ya gani dalla-dalla cewa Allah shi ne mafi girma kuma mutum ba zai iya kwatanta kansa da Allah ba. Ayuba ya karɓi ja-gorar kuma ya yi gyara.—Karanta Ayuba 40:8; 42:2, 6.

15, 16. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake taimaka wa bayinsa a yau?

15 Jehobah yana ba bayinsa a yau shawara da ja-gora da za ta amfane su. Ƙari ga haka, muna samun amfani masu muhimmanci. Alal misali, Yesu Kristi ya ba da hadayar fansa don mu sami gafarar zunubanmu. Domin wannan hadayar, za mu iya samun dangantaka na kud da kud da Allah duk da ajizancin mu. (Yaƙ. 4:8; 1 Yoh. 2:1) Sa’ad da muke fuskantar jarrabobi, muna yin addu’a don samun taimako da ƙarfafawa daga ruhu mai tsarki na Allah. Ƙari ga haka, muna da cikakken Littafi Mai Tsarki, kuma idan mun karanta shi kuma muka yi bimbini a kan abin da ke ciki, za mu kasance a shirya a lokacin da aka gwada bangaskiyarmu. Nazari yana taimaka mana mu fahimci batun ikon mallaka na dukan sararin samaniya da kuma yadda za mu kasance da aminci.

16 Ƙari ga haka, muna amfana sosai daga kasancewa cikin ’yan’uwantaka na dukan duniya wanda Jehobah yake ba abinci na ruhaniya ta hanyar “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Mat. 24:45-47) A cikin dukan ikilisiyoyi 100,000 na Shaidun Jehobah, ana yin taro da ke koyar da mu da kuma ƙarfafa mu don mu fuskanci duk wani irin gwajin da zai taso. Za mu iya kwatanta hakan da labarin Sheila, wata Mashaidiya matashiya da ke da zama a ƙasar Jamus.

17. Ka ba da misalin da ya sa yake da kyau mu bi umurnin ƙungiyar Jehobah sosai a yau.

17 A wata rana sa’ad da suke makaranta, babu malami a cikin ajinsu Sheila. Sai ’yan ajinta suka yanke shawarar yin amfani da wani allon da ake yin duba da shi mai suna Ouija. Sai Sheila ta bar ajin da gaggawa, kuma abin da ta ji daga baya ya faranta mata rai cewa ta yanke wannan shawarar. Sa’ad da suke amfani da allon, wasu daga cikin ɗaliban sun ga alamar bayyanuwar aljanu sai suka gudu cikin tsoro. Menene ya taimaka wa Sheila ta bar ajin da gaggawa? “Kafin wannan aukuwar, mun tattauna haɗarin da ke tattare da allon Ouija a Majami’ar Mulki. Saboda haka, na san abin da ya kamata na yi” in ji Sheila. “Na so na faranta wa Jehobah rai kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce a Misalai 27:11.” Yana da kyau sosai cewa Sheila ta halarci wannan taron kuma ta saurari jawabin sosai!

18. Menene ka ƙudurta cewa za ka yi?

18 Bari dukanmu mu tsai da shawarar manne wa umurnin da muke samu daga ƙungiyar Allah. Ta wajen halartan taro kullum a kowane lokaci, karanta Littafi Mai Tsarki, yin nazarin Littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, yin addu’a, yin tarayya da ’yan’uwa Kiristoci da suka manyanta, za mu sami ja-gora da taimakon da muke bukata. Jehobah yana son mu yi nasara, kuma yana da tabbaci cewa za mu ci gaba da kasancewa da aminci. Lallai muna da gatar ɗaukaka sunan Jehobah, kasancewa da aminci, da kuma faranta wa Jehobah rai!

Ka Tuna?

• Waɗanne yanayi da jarrabobi ne Shaiɗan yake jawo?

• Menene abu mafi tamani da muke da shi?

• Menene tushen abotarmu da Jehobah?

• Ta waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake taimaka mana a yau?

[Hotunan da ke shafi na 8]

Kana da niyyar gaya wa mutane abin da ka sani?

[Hotunan da ke shafi na 9]

Za mu iya taimaka wa ’yan’uwa masu bi su riƙe amincinsu

[Hotunan da ke shafi na 10]

Valentina ta yarda ta sadaukar da dukan abin da take da shi don ta riƙe amincinta

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba