Ka Tuna?
Ka yi farin cikin karanta fitowar Hasumiyar Tsaro na kwanan nan? Ka ga ko za ka iya amsa waɗannan tambayoyin:
• Me ya sa yake da kyau mu kasance da nagartanmu ta Kirista?
Yin nagarta tana sa mu goyi bayan ikon mallaka na Jehobah don ƙaunar da muke masa kuma mu ƙaryata Shaiɗan. Nagartanmu ita ce kuma tushen hukuncin da Allah zai iya yi mana kuma tana da muhimmanci ga begenmu na nan gaba.—12/15, shafi na 4-6.
• Waɗanne laƙabi ne suka nuna matsayin Yesu na musamman a nufin Allah?
Ɗa haifaffe kaɗai. Kalman. Amin. Matsakanci na sabon alkawari. Babban Firist. Zuriya da aka yi alkawarinta.—12/15, shafi na 15.
• Ta yaya za mu daɗa farin cikinmu a hidimar fage?
Za mu iya shirya zuciyarmu, ta wajen mai da hankali ga yadda za mu iya taimaka wa waɗansu. Za mu iya yin wa’azi da ƙudurin fara Nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Idan muka fuskanci tsanani, za mu iya canja gabatarwarmu kuma mu tattauna batutuwan da mutanen da suke yankinmu suke so.—1/15, shafofi na 8-10.
• Ta yaya koyarwar Littafi Mai Tsarki zai shafi halin Kirista da al’adu game da Jana’iza?
Ko da yake Kirista zai iya yin makoki domin ƙaunatattunsa da suka mutu, amma ya san cewa matattu ba su san komi ba. Ko da marasa bin gaskiya sun yi tir da shi, za ya ƙi kowanne al’ada da ke haɗe da imanin cewa matattu za su iya rinjayar masu rai. Don guje wa matsaloli, waɗansu Kiristoci sukan rubuta abubuwan da suke so a yi game da shirin jana’izarsu.—2/15, shafi na 29-31.
• Menene ma’anar kalmar nan ta Dauda ga Jehobah: “Ka sa hawayena cikin goranka”? (Zabura 56:8)
Dauda ya gaskata cewa Jehobah yana kallonsa kuma zai tuna da azabarsa, kamar ya adana ta a gorarsa. Hakazalika, yawancin mutane a yau, musamman ma waɗanda suke iya ƙoƙarinsu su faranta wa Allah rai, suna fuskantar matsalolin da suke shafan motsin zuci, hankali ko kuma wahala ta zahiri. Amma dai, suna iya kasancewa da tabbacin sanin cewa Ubansu na samaniya yana sane da gwajin da suke fuskanta da kuma yadda hakan ke shafan su. Yana sane da azabar da bayinsa suke sha kuma yana tuna hawayensu da wahalolinsu, wato a alamance yana saka su cikin gorarsa.—Oktoba-Disamba, shafi na 30.
• “Litafi na Jashar” da kuma ‘litafin Yaƙin Jehobah’ ɓatattun littattafai ne na Littafi Mai Tsarki? (Joshua 10:13; Litafin Lissafi 21:14)
A’a. Wataƙila wadannan littattafan ba hurarru ba ne da suka wanzu a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki kuma waɗanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki sun ambata su.—3/15, shafi na 32.
• Me ya sa tsabta take da muhimmanci a rayuwar duk Kirista na gaskiya?
Annabi Ishaya ya rubuta wani wahayi da mala’ika ya kwatanta Mahalicci da waɗannan kalaman “Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki.” (Ishaya 6:3) Wannan kwatancin ya nanata cewa Allah mai tsarki ne kuma mai tsabta. Saboda haka, Allah yana bukatar dukan bayinsa su kasance da tsarki da kuma tsabta. Ya ce masu: “Ku za ku zama masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.” (1 Bitrus 1:16)—Janairu-Maris, shafi na 24.