An Yi Wa Bawan Jehobah Rauni “Domin Kurakuranmu”
“Sabili da laifofinmu ne aka yi masa rauni, aka ƙuje shi domin kurakuranmu; . . . ta wurin dūkansa da ya sha mun warke.”—ISHA. 53:5.
1. Menene ya kamata mu sa a zuciya sa’ad da muke Tuna Mutuwar Yesu, kuma wane annabci ne zai taimaka mana mu yi haka?
MUNA tuna Mutuwar Kristi ne don mu tuna dukan abubuwan da mutuwarsa da tashinsa daga matattu suka cim ma. Tuna Mutuwar tana tuna mana kunita ikon mallakar Jehobah, tsarkake sunansa, da kuma cikar manufarsa har da ceton ’yan adam. Babu wani annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da ya bayyana hadayar Kristi dalla-dalla da kuma abin da ta cim ma wa fiye da wanda aka rubuta a Ishaya 53:3-12. Ishaya ya annabta wahalolin da Bawan zai sha kuma ya yi bayani game da mutuwar Kristi da kuma albarkar da mutuwarsa za ta kawo ga ’yan’uwansa shafaffu da “waɗansu tumaki.”—Yoh. 10:16.
2. Menene annabcin Ishaya ya tabbatar, kuma yaya zai shafe mu?
2 Ƙarni bakwai kafin haihuwar Yesu a duniya, Jehobah ya hure Ishaya ya annabta cewa zaɓaɓɓen Bawansa zai kasance da aminci ko da wane irin jarraba ce ya fuskanta. Wannan gaskiyar ta tabbatar da irin amincewar da Jehobah yake da ita ga amincin Ɗansa. Sa’ad da muke bincika wannan annabcin, zuciyarmu za ta daɗaɗa kuma bangaskiyarmu za ta ƙarfafa.
An ‘Raina’ Shi Kuma ba a “Maishe Shi Wani Abu Ba”
3. Me ya sa ya kamata Yahudawa su marabci Yesu, amma ta yaya suka karɓe shi?
3 Karanta Ishaya 53:3. Ka yi tunanin irin sadaukarwar da Ɗan Allah makaɗaici ya yi, na barin jin daɗin yin hidima a gefen Ubansa kuma ya zo duniya don ya ba da ransa hadaya domin ya ceci mutane daga zunubi da mutuwa! (Filib. 2:5-8) Hadayarsa za ta sa a sami cikakkiyar gafara na zunubai, abin da hadayun dabbobi a ƙarƙashin Dokar Musa suka wakilta. (Ibran. 10:1-4) Ya kamata a ce aƙalla Yahudawa da suke jiran Almasihu da aka yi alkawarinsa su marabce shi kuma su ɗaukaka shi. (Yoh. 6:14) Maimakon haka, Yahudawa sun ‘raina’ Kristi, kuma ba su “maishe shi wani abu ba,” kamar yadda Ishaya ya annabta. Manzo Yohanna ya rubuta: “Ya zo wurin abin mulkinsa, amma su waɗanda ke nasa ba su karɓe shi ba.” (Yoh. 1:11) Manzo Bitrus ya gaya wa Yahudawa: “Allah . . . na ubanninmu, ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka yi musun saninsa a gaban Bilatus, lokacinda ya ƙudurta za ya sake shi. Amma Mai-tsarki da Mai-adilci kuka musunce.”—A. M. 3:13, 14.
4. Ta yaya Yesu ya san rashin lafiya?
4 Ishaya ya kuma annabta cewa Yesu “ya saba da ciwuta.” A lokacin hidimarsa, akwai lokacin da Yesu ya gaji, amma babu alamar cewa ya yi rashin lafiya. (Yoh. 4:6) Amma, ya san game da rashin lafiyar waɗanda ya yi wa wa’azi. Ya ji tausayinsu kuma ya warkar da yawancinsu. (Mar. 1:32-34) Ta yin hakan, Yesu ya cika annabcin da ya ce: “Lallai da kayan ciwutanmu ya nawaita, ya ɗauki baƙincikinmu.”—Isha. 53:4a; Mat. 8:16, 17.
“Dukakke na Allah”
5. Yaya yawancin Yahudawa suka ɗauki mutuwar Yesu, kuma me ya sa hakan ya daɗa ga wahalarsa?
5 Karanta Ishaya 53: 4b. Mutanen zamanin Yesu ba su fahimci dalilin da ya sa ya sha wahala kuma ya mutu ba. Sun gaskata cewa Allah ne yake horonsa, kamar ya ɗora masa cuta mai ban ƙyama. (Mat. 27:38-44) Yahudawa sun zargi Yesu cewa ya yi saɓo. (Mar. 14:61-64; Yoh. 10:33) Hakika, Yesu ba mai zunubi ko kuma mai saɓo ba ne. Amma domin yana ƙaunar Ubansa sosai, ra’ayin cewa zai mutu kamar wanda aka tuhuma da yin saɓo ya daɗa ga wahalarsa a matsayin Bawan Jehobah. Duk da haka, ya amince ya miƙa kansa ga nufin Jehobah.—Mat. 26:39.
6, 7. Ta yaya Jehobah ya ‘ƙuje’ Bawansa mai aminci, kuma me ya sa hakan ya faranta wa Allah rai?
6 Ba mu yi mamakin karanta cewa annabcin Ishaya ya ce mutane za su ce ‘Allah ne ya duki’ Kristi ba, amma abin mamaki shi ne abin da annabcin ya ce: “Ubangiji ya nufa a ƙuje shi.” (Isha. 53:10) Tun da yake Jehobah ya ce: “Ku duba barana . . . zaɓaɓena wanda raina yana murna da shi,” ta yaya ne Jehobah zai “nufa a ƙuje shi”? (Isha. 42:1) Ta yaya za a ce hakan ya sa Jehobah farin ciki?
7 Don mu fahimci wannan sashen annabcin, ya kamata mu tuna cewa sa’ad da Shaiɗan yake ƙalubalantar ikon mallakar Jehobah, ya ce bayin Allah na sama da duniya ba za su kasance da aminci ba. (Ayu. 1:9-11; 2:3-5) Ta wajen kasancewa da aminci har mutuwa, Yesu ya ba da amsa mafi kyau ga ƙalubalen da Shaiɗan ya yi. Da haka, ko da yake Jehobah ya ƙyale maƙiyansa su kashe Kristi, babu shakka cewa Jehobah ya yi baƙin ciki sa’ad da ya ga yadda aka kashe zaɓaɓɓen Bawansa. Amma, ganin yadda Ɗansa ya kasance da aminci ya faranta wa Jehobah rai sosai. (Mis. 27:11) Bugu da ƙari, sanin amfanin da mutuwar Ɗansa za ta kawo wa ’yan adam da suka tuba, ya sa Jehobah farin ciki sosai.—Luk 15:7.
“Sabili da Laifofinmu ne Aka Yi Masa Rauni”
8, 9. (a) Ta yaya ne aka yi wa Yesu ‘rauni sabili da laifofinmu’? (b) Ta yaya ne Bitrus ya tabbatar da haka?
8 Karanta Ishaya 53:6. Kamar ɓatacciyar tunkiya, mutane masu zunubi suna ta kai da kawowa, suna neman ceto daga rashin lafiya da mutuwa da muka gada daga Adamu. (1 Bit. 2:25) Domin su ajizai ne, babu wani a cikin zuriyar Adamu da zai iya fansar abin da Adamu ya rasa. (Zab. 49:7) Domin ƙaunarsa mai girma, “Ubangiji kuma ya ɗibiya masa dukan kurakuranmu,” wato, ƙaunataccen Ɗansa kuma zaɓaɓɓen Bawansa. Domin ya yarda a ‘yi masa rauni sabili da laifofinmu’ kuma a “ƙuje shi domin kurakuranmu,” Kristi ya ɗauki zunubanmu a kan gungumen azaba kuma ya mutu a madadinmu.
9 Manzo Bitrus ya rubuta: “Gama zuwa wannan aka kiraye ku: gama Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa. Da kansa fa ya ɗauki zunubanmu ya kai su cikin jiki nasa bisa itacen, domin mu, matattu ga zunubai, mu rayu ga adalci.” Sa’ad da yake ƙaulin annabcin Ishaya, Bitrus ya daɗa: “Ta wurin dūkansa da ya sha mun warke.” (1 Bit. 2:21, 24; Isha. 53:5) Hakan ya buɗe wa masu zunubi hanyar sake soma dangantaka da Allah, kamar yadda Bitrus ya ce: “Kristi kuma ya sha azaba sabili da zunubai so ɗaya, mai-adilci sabili da marasa-adilci, domin shi kawo mu ga Allah.”—1 Bit. 3:18.
An Kawo Shi “Kamar Ɗan Rago da a ke Kai Wurin Yanka”
10. (a) Yaya Yohanna Mai Baftisma ya kwatanta Yesu? (b) Me ya sa kalaman Yohanna suka dace?
10 Karanta Ishaya 53:7, 8. Sa’ad da Yohanna mai Baftisma ya ga Yesu yana tafe, ya ce da babbar murya: “Duba, ga Ɗan rago na Allah wanda yana ɗauke da zunubin duniya!” (Yoh. 1:29) Sa’ad da ya kira Yesu Ɗan rago, wataƙila Yohanna yana nufin kalmomin da ke Ishaya da suka ce, an kawo shi “kamar ɗan rago da a ke kai wurin yanka.” (Isha. 53:7) Ishaya ya annabta cewa, “ya tsiyaye ransa har ga mutuwa.” (Isha. 53:12) Abin al’ajabi shi ne, a daren da Yesu ya kafa Tuna Mutuwarsa, ya ba almajiransa 11 masu aminci kofin ruwan inabi kuma ya ce: “Wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa zuwa gafarar zunubai.”—Mat. 26:28.
11, 12. (a) Menene son rai da Ishaƙu ya nuna na yin hadaya da shi ya kwatanta game da hadayar Kristi? (b) Menene ya kamata mu tuna game da Ibrahim Mafi Girma, Jehobah, sa’ad da muke Tuna Mutuwar Yesu?
11 Kamar Ishaƙu na dā, Yesu yana shirye ya ba da ransa hadaya a kan bagadin nufin Jehobah dominsa. (Far. 22:1, 2, 9-13; Ibran. 10:5-10) Ko da yake Ishaƙu da son ransa ya yarda a miƙa shi hadaya, Ibrahim ne ya miƙa hadayar. (Ibran. 11:17) Hakanan ma, Yesu da son ransa ya yarda cewa zai mutu, amma Jehobah ne ya tsai da yadda za a miƙa fansar. Hadayar Ɗansa ta nuna cewa Allah yana ƙaunar ’yan adam sosai.
12 Yesu da kansa ya ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Manzo Bulus ya rubuta: “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da shi ke, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Rom. 5:8) Saboda haka, yayin da muke daraja Kristi ta wajen tuna mutuwarsa, kada mu manta cewa wanda ya tsara wannan hadayar shi ne Ibrahim Mafi Girma, Jehobah. Muna Tuna Mutuwar Yesu ne don mu ɗaukaka Jehobah.
Bawan “Ya Baratadda Masu-Yawa”
13, 14. Ta yaya ne Bawan Jehobah “ya baratadda masu-yawa”?
13 Karanta Ishaya 53:11, 12. Game da zaɓaɓɓen Bawansa, Jehobah ya ce: “Bawana mai-adilci za ya baratadda masu-yawa.” Ta wace hanya? Ƙarshen aya ta 12 ta ba mu haske game da amsar. “[Bawan] ya kuma yi roƙo sabili da masu-laifi.” An haifi dukan zuriyar Adamu cikin zunubi, wato, “masu-laifi,” kuma saboda haka sun sami “hakkin zunubi,” wato, mutuwa. (Rom. 5:12; 6:23) Ana bukatar sulhu tsakanin Jehobah da mutane masu zunubi. Sura ta 53 na annabcin Ishaya ta yi kwatanci mai kyau na yadda Yesu ya “yi roƙo” a madadin mutane ajizai, yana cewa: “[Horo] kuma mai-kawo lafiyarmu a kansa ya ke; ta wurin dūkansa da ya sha mun warke.”—Isha. 53:5.
14 Ta wajen ɗaukan zunubanmu a kansa kuma ya mutu dominmu, Kristi “ya baratadda masu-yawa.” Bulus ya rubuta: “Dukan cikar Allah ta nufa ta zauna cikinsa [Kristi]; ta wurinsa kuwa a sulhunta abu duka gareshi, bayanda ya yi salama ta wurin jinin giciyyensa; ta wurinsa, ni ke cewa, ko abubuwan da ke bisa duniya, ko kuwa abubuwan da ke cikin sama.”—Kol. 1:19, 20.
15. (a) Su wanene “abubuwan da ke cikin sama” da Bulus ya ambata? (b) Su wanene kaɗai suke da ’yancin cin gurasa da shan inabi na Tuna Mutuwar Yesu, me ya sa?
15 “Abubuwan da ke cikin sama” da suka sulhunta da Jehobah ta hanyar jinin Kristi su ne shafaffun Kiristoci, da aka kira su su yi mulki tare da Kristi a sama. Kiristoci da “masu-tarayya na kira basamaniya” sun sami “kuɓutar rai.” (Ibran. 3:1; Rom. 5:1, 18) Bayan haka, Jehobah ya karɓe su a matsayin ’ya’yansa na ruhaniya. Ruhu mai tsarki yana shaida musu cewa su “masu-tarayyan gādo da Kristi” ne, kuma an zaɓe su su zama sarakuna da firistoci a Mulkinsa na sama. (Rom. 8:15-17; R. Yoh. 5:9, 10) Sun zama sashen Isra’ila na ruhaniya, wato, “Isra’ila na Allah,” kuma an kai su cikin “sabon alkawari.” (Irm. 31:31-34; Gal. 6:16) A matsayin waɗanda suke cikin sabon alkawari, suna da ikon cin gurasar Tuna Mutuwar Yesu, har da ruwan inabin, wanda Yesu ya ce game da shi: “Wannan ƙoƙon sabon alkawali ne, cikin jinina, wanda an zubas dominku.”—Luk 22:20.
16. Menene “abubuwan da ke bisa duniya,” kuma ta yaya suka sami matsayi na adalci a gaban Jehobah?
16 “Abubuwan da ke bisa duniya” su ne wasu tumaki na Kristi, waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya har abada. Ga waɗannan kuma, zaɓaɓɓen Bawan Jehobah ya sa sun sami matsayi na adalci a gaban Jehobah. Domin suna da bege a hadayar fansa na Kristi kuma sun “wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon,” Jehobah ya mai da su masu aminci, ba a matsayin ’ya’yansa na ruhu ba, amma a matsayin abokansa, kuma ya ba su bege mai kyau na tsira “daga cikin babban tsananin.” (R. Yoh. 7:9, 10, 14; Yaƙ. 2:23) Domin ba sa cikin sabon alkawari kuma ba su da begen yin rayuwa a sama, wasu tumaki ba sa cin gurasa da shan inabi na Tuna Mutuwar Yesu amma suna hallara ne a matsayin masu kallo cikin daraja.
Godiya ta Tabbata ga Jehobah da Amintaccen Bawansa!
17. Ta yaya ne nazarin annabce-annabce da ke Ishaya da suka mai da hankali ga Bawa suka taimaka mana mu shirya hankulanmu ga Tuna Mutuwar Yesu?
17 Bincika annabce-annabcen da ke cikin Ishaya da suka yi magana a kan Bawan nan hanya ce mai kyau na shirya hankulanmu don Tuna Mutuwar Kristi. Sun sa mu “zuba ido ga . . . shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta.” (Ibran. 12:2) Mun koyi cewa Ɗan Allah ba mai rashin biyayya ba ne. Akasin Shaiɗan, yana son Jehobah ya koyar da shi, domin ya yarda cewa shi ne Ubangiji Mai ikon mallaka. Mun ga cewa a lokacin hidimar Kristi a duniya, ya nuna juyayi ga mutanen da ya yi wa wa’azi, ya warkar da yawancinsu a zahiri kuma a ruhaniya. Ta haka, ya nuna abin da zai yi a matsayin Sarki Almasihu a sabuwar duniya sa’ad da ya “kafa shari’a ta gaskiya cikin duniya.” (Isha. 42:4) Ƙwazon da ya nuna a wajen wa’azin Mulki, a matsayin “haske na al’ummai,” abin tunawa ne ga mabiyansa da zai sa su yi wa’azi da ƙwazo a dukan duniya.—Isha. 42:6.
18. Me ya sa annabcin Ishaya ya cika zukatanmu da godiya ga Jehobah da kuma Bawansa mai aminci?
18 Annabcin Ishaya ya kuma faɗaɗa fahimtarmu ta sadaukarwa mai girma da Jehobah ya yi sa’ad da ya aiko da ƙaunataccen Ɗansa zuwa duniya don ya sha wahala kuma ya mutu dominmu. Jehobah ya yi farin ciki, ba a ganin yadda Ɗansa ya sha wahala ba, amma ta wajen ganin cikakken amincin da Yesu ya nuna har mutuwa. Ya kamata mu yi farin ciki kamar Jehobah, ta wajen sanin dukan abubuwan da Yesu ya yi don ƙaryata Shaiɗan kuma ya tsarkake sunan Jehobah, da haka, ya kunita ikon Jehobah na yin Sarauta. Bugu da ƙari, Kristi ya ɗauki zunubanmu a kansa kuma ya mutu dominmu. Ta wannan hanyar, ya sa ya yiwu ƙaramin garke na ’yan’uwansa shafaffu da kuma wasu tumaki su kasance da matsayi mai kyau a gaban Jehobah. Yayin da muka taru domin Tuna Mutuwar Yesu, bari zukatanmu su cika da godiya ga Jehobah da kuma Bawansa mai aminci.
Ta Hanyar Bita?
• Ta yaya ne Jehobah ya “nufa” a “ƙuje” Ɗansa?
• Ta yaya aka ji wa Yesu ‘rauni saboda laifofinmu’?
• Ta yaya ne Bawan “ya baratadda masu-yawa”?
• Ta yaya ne annabce-annabce game da Bawan suka shirya hankalinka da zuciyarka ga Tuna Mutuwar Yesu?
[Hotunan da ke shafi na 26]
“Aka rena shi . . . mu kuma ba mu maishe shi wani abu ba”
[Hotunan da ke shafi na 28]
“Ya tsiyaye ransa har ga mutuwa”
[Hotunan da ke shafi na 29]
“Waɗansu tumaki” suna halartar Tuna Mutuwar Yesu a matsayin masu kallo cikin daraja