Duba! Bawan Da Jehobah Yake Murna Da Shi
“Ku duba barana . . . wanda raina yana murna da shi.”—ISHA. 42:1.
1. Menene aka ƙarfafa mutanen Jehobah su yi, musamman da yake lokacin Tuna Mutuwar Yesu ya kusa, kuma me ya sa?
YAYIN da lokacin tuna mutuwar Kristi yake kusatowa, yana da kyau mutanen Allah su bi gargaɗin manzo Bulus su “zuba ido ga Yesu shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta.” Bulus ya daɗa: “Gama ku lura da shi wanda ya jimre da wannan irin jayayyar mutane masu-zunubi a kansa, domin kada ku gaji, ku yi suwu cikin rayukanku.” (Ibran. 12:2, 3) Mai da hankali ga tafarkin Kristi na aminci, wanda a ƙarshensa ya ba da ransa, zai taimaka wa shafaffu Kiristoci da abokanansu waɗansu tumaki su ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci kuma su guji ‘yin suwu cikin rayukansu.’—Gwada Galatiyawa 6:9.
2. Menene za mu iya koya daga annabce-annabcen Ishaya da suka yi magana game da Ɗan Allah?
2 Ta bakin annabi Ishaya, Jehobah ya hure annabce-annabce da yawa kai tsaye game da Ɗansa. Waɗannan annabce-annabce za su taimake mu mu “zuba ido ga Yesu shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta,” Yesu Kristi.a Sun ba da bayani game da halinsa, wahalar da ya sha, da yadda aka ɗaukaka shi a matsayin Sarkinmu kuma Mai Cetonmu. Za su sa mu faɗaɗa fahiminmu game da Tuna Mutuwarsa, wadda za a yi wannan shekara a ranar Alhamis, 9 ga Afrilu, bayan faɗuwar rana.
An Gane Bawan
3, 4. (a) A cikin littafin Ishaya, mecece kalmar nan ‘bawa’ take nufi? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya bayyana Bawan da aka ambata a Ishaya surori 42, 49, 50, 52, da 53?
3 Kalmar nan ‘bawa’ ta fito a wurare da yawa a littafin Ishaya. A wani lokaci, yana nufin annabin da kansa. (Isha. 20:3; 44:26) A wani lokacin kuma yana nuni ga dukan al’ummar Isra’ila, ko Yaƙub. (Isha. 41:8, 9; 44:1, 2, 21) Annabce-annabce na musamman game da Bawan da ke rubuce a Ishaya surori 42, 49, 50, 52, da 53 kuma fa? Nassosin Kirista na Helenanci sun bayyana mana sarai ko wanene Bawan Jehobah da aka kwatanta a waɗannan surorin. Hakika, ma’aikacin Habasha da aka ambata a littafin Ayyukan Manzanni yana karanta ɗaya cikin waɗannan annabce-annabcen sa’ad da ruhu mai tsarki ya ja-gorance Filibbus mai wa’azi ya je ya same shi. Da yake ma’aikacin ya karanta ayoyin Littafi Mai Tsarki da ke Ishaya 53:7, 8, ya tambayi Filibbus: “Ina biɗa gareka, Annabi yana ambaton wanene? kansa ne, ko wani ne?” Filibbus bai ɓata lokaci ba ya bayyana masa cewa Ishaya yana magana ne game da Almasihu, Yesu.—A. M. 8:26-35.
4 Sa’ad da Yesu yake jariri, wani mutum mai adalci da ake kira Siman ya sanar ta ikon ruhu mai tsarki cewa “yaro Yesu” zai zama “haske domin bayanuwa ga Al’ummai,” kamar yadda aka annabta a Ishaya 42:6 da 49:6. (Luk 2:25-32) Bugu da ƙari, an annabta wulakancin da Yesu ya sha a daren da aka kama shi a littafin Ishaya 50:6-9. (Mat. 26:67; Luk 22:63) Bayan Fentakos ta 33 A.Z., manzo Bitrus ya nuna sarai cewa Yesu ne ‘Bawan’ Jehobah. (Isha. 52:13; 53:11; karanta Ayukan Manzanni 3:13, 26.) Menene za mu iya koya daga waɗannan annabce-annabce game da Almasihu?
Jehobah Ya Koyar da Bawansa
5. Wace koyarwa ce aka yi wa wannan Bawan?
5 Ɗaya daga cikin annabce-annabcen Ishaya game da Bawan Allah ya ba da haske a kan dangantaka na kud da kud da ke tsakanin Jehobah da Ɗansa na fari kafin ya zo duniya. (Karanta Ishaya 50:4-9.) Bawan da kansa ya faɗi cewa Jehobah ya ci gaba da koyar da shi, ya ce: “Ya kan farkarda kunnena domin in ji kamar koyayyun mutane.” (Isha. 50:4) A wannan lokacin, Bawan Jehobah ya saurari Ubansa kuma ya koya daga wajensa, ya zama almajiri mai yin biyayya. Gata ne na musamman Mahaliccin sararin samaniya ya koyar da shi!
6. Ta yaya Bawan ya nuna cewa ya yi biyayya sosai ga Ubansa?
6 A cikin wannan annabcin, Bawan ya kira Ubansa “Ubangiji Yahweh.” Wannan ya nuna cewa Bawan ya koyi gaskiya mai muhimmanci game da ikon mallaka na Jehobah. Da yake nuna biyayyarsa sosai ga Ubansa, ya faɗa: “Ubangiji Yahweh ya buɗe kunnena, ban yi tayarwa ba, ban kuwa bada baya ba.” (Isha. 50:5) Yana “nan wurinsa, [Jehobah, a matsayin] gwanin mai-aiki” sa’ad da yake halittan sararin samaniya da kuma ’yan adam. Wannan “gwanin mai-aiki” yana “farinciki a gabansa [Jehobah]. Farinciki ni ke yi a cikin wuraren zama na duniyarsa: daulata [Ɗan Allah] tana wurin ’yan adam.”—Mis. 8:22-31.
7. Menene ya nuna cewa Bawan ya tabbata cewa Ubansa zai taimake shi a lokacin gwajinsa?
7 Koyarwa da aka yi wa Bawan da kuma yadda yake son ’yan adam ya sa ya jimre sa’ad da ya zo duniya kuma ya fuskanci hamayya mai tsanani. Ya ci gaba da yin nufin Ubansa tare da farin ciki, har lokacin da ya fuskanci hamayya mai tsanani. (Zab. 40:8; Mat. 26:42; Yoh. 6:38) A lokacin da yake fuskantar gwaji a duniya, Yesu ya kasance da tabbaci cewa Ubansa ya amince da shi kuma yana goyon bayansa. Kamar yadda aka annabta a annabcin Ishaya, Yesu ya ce: “Mai-baratadda ni yana kusa; wa za ya yi kokuwa da ni? . . . Ga shi, Ubangiji Yahweh za ya taimake ni.” (Isha. 50:8, 9) Babu shakka, Jehobah ya taimaki Bawansa mai aminci sa’ad da yake hidima a duniya, kamar yadda wani annabci na Ishaya ya nuna.
Hidimar Bawan a Duniya
8. Menene ya nuna cewa Yesu ne ‘zaɓaɓɓe’ na Jehobah, kamar yadda aka annabta a Ishaya 42:1?
8 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da ya faru sa’ad da aka yi wa Yesu baftisma a shekara ta 29 A.Z.: “Ruhu Mai-tsarki kuwa ya sauko . . . bisansa, murya kuwa ta fito daga sama, Kai ne Ɗana ƙaunatacce: da kai raina ya ji daɗi ƙwarai.” (Luk 3:21, 22) Jehobah ya nuna ‘zaɓaɓɓensa’ sarai, da aka ambata a annabcin Ishaya. (Karanta Ishaya 42:1-7.) Sa’ad da yake hidima a duniya, Yesu ya cika wannan annabcin a hanya ta musamman. A labarin Linjila, Matta ya yi ƙaulin kalmomin da ke Ishaya 42:1-4 kuma ya nuna yadda annabcin ya cika a kan Yesu.—Mat. 12:15-21.
9, 10. (a) Ta yaya ne Yesu ya cika annabcin da ke Ishaya 42:3 a lokacin hidimarsa? (b) Ta yaya ne Kristi ya “fito da shari’a” sa’ad da yake duniya, kuma a wane lokaci ne “ya kafa shari’a ta gaskiya cikin duniya”?
9 Shugabannin addini na Yahudawa sun rena talakawa da ke tsakaninsu. (Yoh. 7:47-49) An wulakanta mutanen kuma za a iya kwatanta su da “rarraunan kara” ko kuma ‘lagwani mai-hayaƙi’ sa’ad da yake gab da mutuwa. Amma, Yesu ya nuna juyayi ga talakawa da waɗanda suke wahala. (Mat. 9:35, 36) Ya miƙa wa irin waɗannan mutanen gayyata mai kyau, yana cewa: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa.” (Mat. 11:28) Bugu da ƙari, Yesu ‘ya fito da gaskiya’ ta wajen koyar da mizanan Jehobah game da abin da yake da kyau da marar kyau. (Isha. 42:3) Ya kuma nuna cewa ana bukatar a yi amfani da Dokar Allah da sanin ya kamata da kuma jin kai. (Mat. 23:23) Yesu ya kuma nuna shari’a ta gaskiya ta wajen yin wa’azi ga mawadata da talakawa ba son kai.—Mat. 11:5; Luk 18:18-23.
10 Annabcin Ishaya ya kuma nuna cewa ‘zaɓaɓɓe’ na Jehobah ya “kafa shari’a ta gaskiya cikin duniya.” (Isha. 42:4) Zai yi hakan ba da daɗewa ba sa’ad da ya zama Sarkin Mulkin Almasihu, zai halaka dukan mulkokin siyasa kuma ya sauya su da nasa sarauta ta adalci. Zai gabatar da sabuwar duniya, inda “adalci yake zaune.”—2 Bit. 3:13; Dan. 2:44.
“Haske” da “Alkawari”
11. Ta yaya ne Yesu ya zama “haske na al’ummai” a ƙarni na farko, kuma ta yaya ne yake yin hakan har yanzu?
11 Sa’ad da yake cika annabcin da ke Ishaya 42:6, Yesu ya nuna da gaske cewa shi ne “haske na al’ummai.” A lokacin da yake hidima a duniya, ainihi ya kawo haske na ruhaniya ne ga Yahudawa. (Mat. 15:24; A. M. 3:26) Amma Yesu ya ce: “Ni ne hasken duniya.” (Yoh. 8:12) Ya zama haske ga Yahudawa da kuma al’ummai ta wajen hasken da ya kawo na ruhaniya da kuma kamiltaccen ransa da ya bayar a matsayin fansa ga dukan mutane. (Mat. 20:28) Bayan an ta da shi daga matattu, ya umurci almajiransa su zama shaidunsa “har kuma iyakan duniya.” (A. M. 1:8) A lokacin hidimarsu, Bulus da Barnaba sun yi ƙaulin furcin nan “haske na al’ummai” kuma sun ce yana nuni ne ga aikin wa’azin da suke yi a tsakanin waɗanda ba Yahudawa ba. (A. M. 13:46-48; gwada Ishaya 49:6.) Ana ci gaba da yin wannan aikin yayin da ’yan’uwan Yesu shafaffu da ke duniya da abokansu suke yaɗa haske na ruhaniya kuma suke taimaka wa mutane su yi imani da Yesu, wanda shi ne “haske na al’ummai.”
12. Ta yaya ne Jehobah ya ba da Bawansa kamar “alkawari na mutane”?
12 A wannan annabcin, Jehobah ya gaya wa zaɓaɓɓen Bawansa: “[Zan] kiyaye ka kuma, in maishe ka alkawari na mutane.” (Isha. 42:6) Shaiɗan ya yi iya ƙoƙarinsa ya halaka Yesu kuma ya hana shi kammala hidimarsa a duniya, amma Jehobah ya kāre shi har lokacin da aka ƙayyade masa ya mutu. (Mat. 2:13; Yoh. 7:30) Bayan haka, Jehobah ya ta da Yesu daga matattu kuma ya ba da shi kamar “alkawari” ga mutane a duniya. Wannan alkawarin ya ba da tabbaci cewa Bawan Allah mai aminci zai ci gaba da kasancewa “haske na al’ummai,” yana ’yantar da waɗanda suke cikin duhu na ruhaniya.—Karanta Ishaya 49:8, 9.b
13. Ta wace hanya ce Yesu ya ceci “mazauna a cikin duhu” sa’ad da yake hidima a duniya, kuma ta yaya yake ci gaba da yin hakan?
13 Daidai da wannan alkawarin, zaɓaɓɓen Bawan Jehobah zai “buɗe idanun makafi,” zai “fito da yan sarƙa daga cikin duhu,” kuma zai ceci “mazauna a cikin duhu.” (Isha. 42:7) A lokacin da yake hidima a duniya, Yesu ya yi hakan ta wajen fallasa al’adu na addinin ƙarya da kuma yin wa’azin bishara na Mulki. (Mat. 15:3; Luk 8:1) Ta hakan, ya ceci Yahudawan da suka zama almajiransa daga kurkuku na ruhaniya. (Yoh. 8:31, 32) Hakazalika, Yesu ya kawo ceto na ruhaniya ga miliyoyin mutanen da ba Yahudawa ba. Ya umurci mabiyansa su “tafi fa, [su] almajirtadda dukan al’ummai,” kuma ya yi alkawari cewa zai kasance da mabiyansa “har matuƙar zamani.” (Mat. 28:19, 20) Daga inda yake a sama, Yesu Kristi yana kula da aikin wa’azin da ake yi a dukan duniya.
Jehobah Ya Ɗaukaka ‘Bawan’
14, 15. Me ya sa Jehobah ya ɗaukaka Bawansa kuma ta yaya ya yi hakan?
14 A wani annabci kuma game da Bawansa Almasihu, Jehobah ya faɗa: “Ga shi, bawana za ya yi albarka, za ya yi girma ya ɗaukaka, za ya zama maɗaukaki ƙwarai.” (Isha. 52:13) Domin Ɗansa ya miƙa kansa ga ikon mallakarsa da kuma amincinsa cikin gwaji mafi tsanani, Jehobah ya ɗaukaka shi.
15 Manzo Bitrus ya rubuta game da Yesu: “Shi wanda ke ga hannun dama na Allah, ya rigaya ya hau sama; an sarayyadda mala’iku da mulkoki da ikoki ƙarƙashinsa.” (1 Bit. 3:22) Hakazalika, manzo Bulus ya rubuta: “Ya ƙasƙantadda kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa, i, har mutuwa ta giciye. Domin wannan Allah kuma ya ba shi mafificiyar ɗaukaka, ya ba shi suna wanda ke bisa kowane suna; domin cikin sunan Yesu kowacce gwiwa ta rusuna, ta cikin sama da ta kan duniya da ta ƙarƙashin duniya, kowane harshe kuma shi shaida Yesu Kristi Ubangiji ne, zuwa darajar Allah Uba.”—Filib. 2:8-11.
16. Ta yaya Yesu ya “zama maɗaukaki ƙwarai” a shekara ta 1914, kuma menene ya cim ma tun lokacin?
16 A shekara ta 1914, Jehobah ya ƙara ɗaukaka Yesu. Ya “zama maɗaukaki ƙwarai” sa’ad da Jehobah ya ɗora shi a kan kursiyi a matsayin Sarkin Mulkin Almasihu. (Zab. 2:6; Dan. 7:13, 14) Tun lokacin, Kristi ya fita garin cin “sarauta a tsakiyar maƙiyan[sa].” (Zab. 110:2) Ya fara cin nasara a kan Shaiɗan da aljannunsa, ya jefo su zuwa duniya. (R. Yoh. 12:7-12) A matsayin Cyrus Mai Girma, Kristi ya ceci sauran ’yan’uwansa shafaffu a duniya daga “Babila babba.” (R. Yoh. 18:2; Isha. 44:28) Ya ja-goranci aikin wa’azi da ake yin a dukan duniya da ya sa ake tattara “sauran zuriya” na ’yan’uwansa na ruhaniya da kuma miliyoyin “waɗansu tumaki,” abokai masu aminci na “ƙaramin garke.”—R. Yoh. 12:17; Yoh. 10:16; Luk 12:32.
17. Menene muka koya daga nazarin annabce-annabcen Ishaya game da ‘bawan’?
17 Nazarin waɗannan annabce-annabce na musamman a cikin littafin Ishaya babu shakka ya ƙara fahiminmu game da Sarkinmu da kuma Mai Ceto, Yesu Kristi. Biyayyarsa sa’ad da yake hidima a duniya ta nuna irin koyarwar da Ubansa ya yi masa kafin ya zo duniya. Ya nuna cewa shi ne “haske na al’ummai” ta hanyar hidimarsa da kuma aikin wa’azi da yake ja-gora har yanzu. Kamar yadda za mu gani, wani annabcin kuma game da Bawa Almasihu ya nuna cewa zai sha wahala kuma zai ba da ransa don amfaninmu, batutuwa da ya kamata mu “lura da” su domin lokacin Tuna Mutuwar Yesu ya kusa.—Ibran. 12:2, 3.
[Hasiya]
a Za ka iya ganin waɗannan annabce-annabce a Ishaya 42:1-7; 49:1-12; 50:4-9; da 52:13–53:12.
b Don tattauna annabcin da ke Ishaya 49:1-12, ka duba Isaiah’s Prophecy—Light for All Mankind na 2, shafuffuka na 136-145.
Don Maimaitawa
• Wanene ‘bawan’ da aka ambata a annabce-annabcen Ishaya, kuma yaya muka sani?
• Wace koyarwa ce Bawan ya samu daga Jehobah?
• Ta yaya Yesu ya zama “haske na al’ummai”?
• Ta yaya aka ɗaukaka Bawan?
[Hotunan da ke shafi na 21]
Filibbus ya nuna cewa Yesu Almasihu ne ‘bawan’ da Ishaya ya ambata
[Hotunan da ke shafi na 23]
Da yake shi ne Bawan nan da Jehobah ya zaɓa, Yesu ya nuna juyayi ga talakawa da kuma waɗanda suke wahala
[Hotunan da ke shafi na 24]
Yesu ya samu ɗaukaka daga wurin Ubansa kuma ya naɗa shi Sarkin Mulkin Almasihu